Khalid Idris Doya" />

Ni Ce Mace Ta Farko Da Zan Sauya Tarihin Jihar Bauchi Ta Hanyar Zama Gwamna – Hajiya Baheejah (II)

Ci gaba daga makon da ya gabata

Ya ya zaki yi ga ki mace guda a tsakanin mazaje masu yawa da ke son hawa wannan kujera ta Gwamna?

Alhamdulillahi na dogara ga Allah wanda shi ne yake ba da mulki wa wanda ya so a lokacin da yaso kuma ya karbe ta a hannun wanda ya so, Allah shi ke da zamani yanzu ya kawo zamanin da mace ta farko za ta zama Gwamna da ikon Allah a jihar Bauchi, Kuma inda goyon bayan mata ‘yan uwana wadanda sune mafi yawan masu zabe, sannan maza da matasa da mutanen kirki da dama a jihar Bauchi duk sun karfafeni in nemi wannan kujera kuma sun nuna goyon bayansu da addu’o’insu da fatan alkairi a garemu kuma a kullum suna tare damu muna tare dasu mafi yawan al’ummar jihar Bauchi kuma ire-iren, ayyukan dana ke yi duka sun shafi kyautata rayuwar dan adam, haka ma  zamantakewar da muka yi da al’umma daban-dabam ya sa na sami gogewa kwarai wajen sanin matsalolin dake damun maza da mata a jihar mu da kasar mu baki daya domin irin ayyukan da nake yi a kullum mu’amala ne da jama’a, insha Allahu zan kasance a tsakaninsu kuma ina da kwarin guiwar Allah zai dubi kyakykyawar niyyar da ke zuciyata don al’ummar Jihar Bauchi nake dubawa ya bani nasara don in cire musu kitse a wuta.

Don gogewata ya sa nasan yadda zan inganta rayuwar dan adam, kuma abu na biyu dani da sauran al’umma muna jin takaicin halin da jihar mu ta ke ciki  misali in zaka kwatanta adalci kullum mu a Bauchi tarihinmu yana nuna gwamma jiya da yau to ni ina so ne in sauya salon wannan batu in Allah ya bani nasara ya zama yau tafi jiya kamar yadda  take ka dubi lokacin mulkin jumhuriyya ta biyu lokacin Jihohin Bauchi da Gombe ne Jihar Bauchi Tatari Ali Allah ya ji kansa shi ne Gwamna a lokacinsu kudaden da suke samu bai kai wanda ake samu yanzu ba amma dukkan kasashen hakimai da ke Jihohin guda biyu sai da suka yi makarantun sakandare suka gina, har da gidajen Malamai suka samar da kayayyakin koyo da koyarwa masu nagarta suka gina asibitoci a dukan kananan hukumomi suka samar da magunguna, haka kuma sun bunkasa noma da gaske ya isheka ofisoshin bunkasa ayyukan gona da muke dasu a dukkan shiyyoyi dake jihohin biyu ga shanun huda masu karko da nagarta, ga turoktocin noma, ga gidan madarar shanu mai suna ubi dairy  ga wurin kiwon dabbobi na Galambi ga kamfanoni irin su na yin fulawa na Zaki dana yin kayan karau a Misau, da Kamfanin Tumatur a Gombe da sauransu ban da tituna irin na zamani ga wutan layi da aka sa a duk titunan, sun aza harsashin guna al’ummar Jihar Bauchi baki daya inda wadanda suka biyo bayansu sun dora da yanzu muna da saukin al’amura da yawa, amma sai aka bari duk kamfanonin da suka bude irin su kobi cola, zaki flour, da sauransu duk sun mutu murus ofisohin bunkasa ayyukan gonanma babu wani abu a wajen, kuma ya kamata masu zabe su sani yawanci wadanda suka yi mulki yanzu Ilimi kyauta suka samu a makaranta, Kiwon lafiya kyauta a asibitoci hatta littattafan da ake karatu dana rubutu duk kyautane har kudin alawus ana bada wa a kowani zangon karatu da kudin mota, wadanda suka biyo baya kowa yayi kokarinsa amma akwai abin da ake cewa bambancin a fili yake saboda haka in muka sami mulki zamu kwatanta adalci  Gwargwadon irin arzikin da Allah ya baiwa jihar Bauchi a lokacin kuma zamu kawo ci gaba ta yadda zai inganta rayuwar al’ummar Jihar Bauchi baki daya, in Allah ya so, lokaci yayi da jama’ar Jihar Bauchi za su fito su hada kansu su baiwa mace dama ta gwada  don mu kafa tarihi a Nijeriya.

Wace shawara za a ba masu zabe?

Shawarar da zan basu shi ne  su zabi mace Baheejah Mahmood don cancantarta da gaskiyar ta da rikon amanarta kuma su kyamaci batun nan na saida kuri’a kan kudi kalilan  a zaben cike gurbi da aka yi a mazabar Sanatan Bauchi ta kudu an samu zarge-zarge masu karfi kan cewa ana baiwa masu zabe kudi kama daga naira 500 har zuwa dubu biyar dubu goma da turmin atamfa don su kada kuri’a wa wani gaskiya wajibi ne mu sauya wannan dabi’a don an ce kuri’arka Yan cinka, kun ji magabatanmu suna cewa kuri’arka wukarka ko ka ba wa wanda zai yankaka ko kuma kabawa wanda zai yanka maka. a bin nufi inka bada kuri’arka wa wanda zai yankaka ka ga sai bayan shekaru hudu haka za ka zauna ba ilimi kai da yayanka ba magunguna a asibiti ba kayayyakin noma ba sana’a ga talauci ga takaici don ka sayar dasu kan kudin da ka kara ba kafin ka zabi wanda yake kai shi yana jin dadi da yayansa da iyalansa kai kuwa kana ta nishi da kuka cikin wahala don haka ya kamata ku kaurace wa amsar kudi ko wani abu domin saida ‘yancinku na kuri’u ga wasu ‘yan siyasar.

Ya dace mutum ya yi zabi da kansa ba wai wani ya ba shi taro sisi ya sanya ku ku zabi wani da yake da muradi ba. Ku dubi wanda ya cancanta wanda ya kware wanda zai jajirce ya mana ayyukan alkhairi shi zamu zaba. Shi ya sa na bada tarihin  yanda al’amura suka kasance a baya. Don ko a bayan akwai jajirtattun mata da aka yi mulkin baya dasu irin su Hajiya Fati Muazu, Dr Mairo Awak, Mrs Hannatu Ibrahim,  da sauran Jajirtatttun mata da suka nuna kwarewa da nisan hankali, kuma ina jan hakalin al’ummarmu da su gane tarihi ya nuna tun zamanin Annabawa Mata suna mulki, ya isas misali kissar Sarauniya Balkisu da Annabi Sulaimanu, haka ma akwai jajirtattun Mata irin su Sarauniya a Mina ta Zazzau da sarauniya Daurama yanzu kuma lokacin su Baheejah ne da ya kamata a basu dama sununa nasu gaskiya da rikon amanar don cigabar Jihar Bauchi da Nijeriya baki daya.

 

 

 

Exit mobile version