Ni Da Al’ummata!

Aliyu Dahiru Aliyu dahiraliyualiyu@gmail.com                    +2349039128220 (Tes Kawai)

Ina kallon al’ummata sai na rasa shin kuka zan mata ko kuma kokarin nusar da ita zan yi? Ina son al’ummata fiye da yadda wani zai so min ita. Akwai wani da zai rabani da kuncin da yake tattare da zuciyata akanta idan ni ban yi wani abu akai ba? Allah yana gayamana acikin Alkur’aninsa cewa ba ya canjawa mutane komai sai sun canja da kansu. A wata ayar kuma ya fada cewa duk bala’i da musibar da ta samu al’umma to ita fa ta kai kanta da kanta. Kada mu zargi kaddara ko turawa ko yahudawa ko duk wanda muke so mu dorawa laifukan abinda mukai da hannunmu. Mu ne muka janyo musiba da kanmu kuma a kanmu zata kare har zuwa ranar da zamu gyara da kanmu. Ba na son mu dinga dorawa kaddara laifi a yayin da a hannunmu kaddararmu take. Mu muke da hannun juya kaddararmu yadda muke so. Allah ba ya canjawa mutane har sai sun fara canjawa da kansu.

Me yake damuna game da al’ummarmu? Menene ma ba zai dameni a al’ummarmu ba? Me al’ummarmu take da zai farantamin rai? A zamanin baya muna alfahari cewa mun fi turawa riko da gaskiya da ladabi da biyayya. A yanzu kam bana zaton akwai wata biyayya da riko da gaskiya da suka ragemana. Hatta cika alkawarin da riko da gaskiya a yanzu an barmu a baya. Za kai alkawari da bature cewa karfe 9 akwai taro kuma insha Allah zaka ganshi. Amma idan kai alkawari da al’ummarmu karfe tara to ka jira isowarta karfe 11 ko 11:30. Me ya ragemana na cika alkawarin? Ita kam riko da gaskiya kama bar maganar. Mu ne cikakkun makaryata. Makaryata a addini, makaryata a siyasa, makaryata a rayuwa kuma makaryata a zamantakewa. Wannan duk ina maganar inda a da aka sanmu da mutunci ne amma yanzu sai dai mu gani muna yabawa. Idan muka zo maganar ilimai kam to ina zaton mune karshen baya. Bamu da komai a ilimi, musamman na Kimiyya da shine tushen cigaba.

Abin yana damuna kwarai idan na tambayi kaina da hakikar gaskiya a karkashin zuciyata, me duniya za ta rasa idan babu musulmi a yau? Kaima kasan amsar. Mai bada amsa da gaskiya zai gayamaka babu wata girgiza da duniya zatai idan musulmi suka bace daga ban kasa! Mu ne al’ummar da muka fi kowace al’umma rigima a tsakaninmu kan kananun mas’aloli. Mu ne wadanda idan masu ilimi suka bunkasa acikinmu sai a koresu. Me ya faru da Muhammad Abdus Salam? Ya gama bincikensa na kimiyya ya samo lambar yabo ta NOBEL a kasar Pakistan, sai aka koreshi saboda kawai dan Ahmadiyya ne! Me ya shafemu da Ahmadiyyarsa tunda yace shi musulmi ne? Shin an aikomu mala’iku mu dinga duba zukatan mutane don mu gane dan wuta da aljanna? Su kam yahudawa a lokacin da nasu, Albert Einstein, ya samo wannan lambar yabo kawai sai suka ce zasu bashi shugabancin Israel ya hau! Haka ma fa mu kai da Ahmed Zewail. Ya samo lambar yabon a kimiyya amma bayan ya mutu na ga wani a shafin YouTube yana cewa ai zewail wuta zashi! A haka zamu cigaba da zagin masu iliminmu? A haka zamu cigaba da sagewa na kasa gwuiwar karatu? Tamkar yadda mukai da Ibn Sina, Ibn Rushd, Gazzhali da Ibnul Arabi haka muke so mu yi da wadanda suka biyo bayansu?

Sai  ka  kara tambayar kanka, wannan wace irin al’umma ce da bata son masu ilimi? Wannan wace irin al’umma ce da rigima akan kananun abubuwa suka fi tasiri acikinta fiye da magana akan manyan abubuwan amfani? Lambar girma ta NOBEL nawa muke da ita a fannin ilimi? Duka-duka bata kai goma ba har ta bangaren zaman lafiyar. Kuma mafi yawan wadanda aka bawa daga cikinmu an kafirta su ko an koresu daga cikinmu. Masu ilimi irin su Abdul Salam da Ahmed Zewail anaimisu fatan wuta. Kada ma kayi maganar irin su Malala Yousafzei wacce dama tuni aka koreta daga cikinmu bayan ta samu lambar akan ilimin mata. Su kam wadanda muka dauka abokan gaba daga yahudawa su ne suka fi kowa samun wannan lambar. Kai idan kaso ka iya cewa ilimin “Physics” na zamani da ake yanzu, daga “relatibity” zuwa “kuantum mechanics” duk na yahudawa ne! Su suke da kaso 80 cikin 100 na masu lambar Nobel a kimiyya! Wani zai iya cewa ai wannan siyasar duniya ce tasa aka ware musulmi aka bawa yahudawa. Ni kam ina fadin cewa tabbas akwai siyasar duniya acikin bada lambar yabon NOBEL amma a bangaren zaman lafiya (nobel peace prize) amma ba a bangaren ilimi ba. Ilimi a zahiri yake, idan kayi kayi idan bakai ba baka da lambar yabo.

Jami’o’i nawa kasar Israel take dasu? Ita kadai tana da sama da jami’o’in kasashen musulmi! Kasar Amurika kuwa tana da jami’o’i ninkin na kasashen musulmi uku! Ya ilahi ina muke dosa ne?! A shekarun baya aka lissafa cewa kwatankwacin (percentage) jahilan da suke kasar Japan su ne kwatankwacin masu ilimin da suke kasar Masar! Masar din da ita ce tushen ilimin musulmi da wayewarsu amma cike take da jahilan da basu san me duniya take ciki ba a yanzu. Ta yaya zamu samu cigaba a haka? Ta yaya zamu kamo gudun da ilimi yake a duniya a haka? Duniya tayi gaba mu muna jira wadanda basu iya bude ko shafukan litattafai ba su budemana kasashe!

Na sha fada, al’ummarmu ita ta kirkiri mulhidan cikinta. Masu koyamana addini basu fahimci addinin ba. Ba wanda zai karanta irinsu Sigmund Freud, JS Mill, Bertrand Russel, Richard Dawkins da ire-irensu sannan ya dawo gida yaji ana cewa Kimiyya haramun ce ba tare da an tarwatsamasa imani ba. Ba wannan ne mafi muni acikinmu ba. Mu sama da biliyan, wani zai dauka zuciyoyinmu daya suke amma a wargatse suke. Yan tsiraru a Israel sun gagaremu saboda su suka dauki sababin suka barmu da hangen shirme. Babu mafi shirme irin wanda yake ganin rahama ce har ta sanya bature yake kirkirar abubuwan fasaha muna siya! Kana zaton makiyinka zai keramaka bindigar da zaka kasheshi da ita? Zamani muke na ilimin da yahudawa sun yi mana nisa don haka suke mulkar duniya. Su suke rike da America din da muke ganin matsala. Kaso 50 cikin 100 na malaman jami’a a America yahudawa ne. Su suke da kasuwancin duniya. Idan yahudawa suka janyo kudinsu daga America to sai ta sha wahalar tattalin arziki. Su suke da kafafan yada labarai. Daga New York Times zuwa Yahoo! duk na yahudawa ne.

Mu me muke dashi? Rigimar addini da kashe kawunanmu da raba kanmu! Masu ilimi daga cikinmu a kafirta su, jahilai su zama jagorori. Masu kudi acikinmu sai dai su siyo gida a France ko su yi bandakin gwal! Kaso 80 cikin dari na kungiyoyi masu zaman kansu da suke talkafawa (NGOs) ba na musulmi bane. Muna cikin yunwa amma muna ganin zamu iya bude duniya mu yi kasar musulinci. A hakan? A lokacin da muka kasa komai a Palestine kuma a zamanin muke tunanin “Fatahud Dunya”?! Ina tsoron lokacin da yayan da zamu haifa zasu fara tunanin mun taba hauka. Shin ba alamar hauka bane wanda ya kasa saita kansa ya dinga hange bude wajensa? Lokacin da kake tunanin me ya sa  Allah yaki taimakon musulmi a Palestine, ka taba tunanin cewa matsalar ta musulmi ce? Mu al’umma ne da muke karanta “Hasbunnallah” amma muna nufin “Hasbunat Takhalluf” (ci baya ya ishemu). Ta yaya Allah zai taimakemu bamu tashi mun taimaki kanmu ba? Dukkaninmu muna aiki wajen tarwatsa al’ummar maimakon hada kanta. Kayi tunani, da ace yan Palestine yan Shia ne kamar na Yemen, da wallahi sai wasu sun goyi bayan yahudawa akan kisansu! Ba musulinci ne ya damemu ba, kungiyoyin musulinci muke bautawa.

Mutanen Japan idan suka je turai to ilimansu suke debowa. Yawo suke daga wannan jami’ar zuwa waccan jami’ar. Amma mu idan mun je turai to sai dai mu yi yawo daga wancan shagon zuwa wancan shagon. Daga Gucci zuwa Burberry, daga Dolce & Gabbana zuwa Calbin Klein. Hatta fetur din da yake kasashen musulmi, turawa ne suke hakowa su debi kasansu su bamu ragowar. Idan muka karbi ragowar to sai mu kara komawa can mu kashesu a shagon Ferragamo ko a Louis Buitton. A haka mukai ta yi har ya zama a shekarar baya aka gano kididdigar masu ilimi a kasar Japan tayi daidai da kididdigar jahilai a kasar Masar! Masar fa tushen iliminmu abar alfaharinmu ba wata ba.

Ina mafita? Allah ya gama bayanin mafitar. Da farko dai sai mun canja da kanmu sannan Allah zai taimakemu. Abu na biyu kuma dole mu ajiye girman kai mu kwaikwayi yahudawa. Babu irin tsanar da yahudawa basu sha a kasashen turai ba. Babu irin azabar da yahudawa basu sha a turai ba. Kai sai da ta kai ko ruwan sama aka rasa a turai to yanka yahudawa ake saboda ana ganin sune matsalar! To amma me ya sa yanzu aka karbesu? Me ya sa yanzu sai abinda suka ce? Me ya sa yanzu suke juya duniyar? Amsar kawai ta bangaren rungumar ilimi. Idan muka rungumi ilimi to tabbas zamu samu nasara mai yawa. A yayin da suke yan kadan mu kam muna da yawa. Me kake tunani da ace yawanmu na ilimi ne ba ba na zanga-zanga ba?

 

Exit mobile version