A yau Talata ne Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar PDP, Ahmed Mohammed Makarfi ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a garin Ogun.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, Makarfi ya yi wa tsohon shugaban kasar tayin yadawo jam’iyyar PDP, yayin da Obasanjo ya ce, tunda ya fice daga jam’iyyar ba zai kara komawa ba har abada.
Makarfi ya ziyarci Obasanjo ne tare da waɗansu jigajigan jam’iyyar PDP.