Connect with us

WASANNI

Ni Ma Burina Shi Ne In Bugawa Barcelona Wasa Kamar Mahaifina – Kluibert

Published

on

Matashin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Roma ta kasar Italiya, Justin Kluibert ya bayyana cewa shima nan gaba burinsa shi ne yakoma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ya buga wasa kamar yadda mahaifinsa yabuga a kungiyar.
Kluibert dai yana daya daga cikin matasan yan wasan da ake ganin tauraruwarsu zata haskaka a duniya anan gaba bayan daya zura kwallaye 9 cikin wasanni 44 daya buga a kungiyar Ajad kafin a wannan shekarar yakoma Roma.
Dan wasan yace babban burinsa a rayuwa shi ne yabugawa Barcelona wasa kamar yadda mahaifinsa, Patric Kluibert yabugawa kungiyar a shekarun baya kuma nan gaba yana fatan burinsa zai cika.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce dai take zawarcin dan wasan mai shekara 18 a duniya wanda ake tunanin zai maye gurbin mahaifinsa wajen zura kwallo a raga.
Mai koyar da ‘yan wasan tawagar kasar Holland, Roland Koeman dai ya gayya ci matashin dan wasan kuma tuni ya bawa dan wasan shawara daya zauna ya kara shekara daya a kungiyar Ajad kafin yakoma wata babbar kungiya sai dan wasan ya riga ya amince da komawa Roma.
Mahaifin dan wasan dai, Patrice Kluibert ya bugawa Barcelona wasanni 257 daga shekara ta 1998 zuwa shekara ta 2004.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: