Ni Na Fara Kafa Ruga A Shiyyar Kudu Maso Gabashin Nijeriya – Kalu

Wani tsohon gwamnan Jihar Abiya kuma mai tsawatarwa a Majalisar Dattijai ta kasa, Sanata Uzor Orji Kalu, ya bayyana dalilin rashin samun nasarar shirin Shugaba Buhari da kuma gwamnatin tarayya a kan shirin Ruga a sassan Najeroya da cewa, ba a tattauna da mutane an wayar masu da kai ne sosai a kan abinda shirin ya kunsa ba, ya na mai cewa a lokacin da ya ke gwamnan jiharsa ta Abiya ya taba samar da shiri irin na Ruga ba tare wata hatsaniya ba.

A cewar Kalu, ya zama tilas gwamnati ta dakatar da aiwatar da shirin saboda sam ba a yi wa mutane musamman al’ummun da suke a kudanci da kuma wasu sassan tsakiyar kasar nan bayani a kan shirin yanda ya kamata ba sosai.

Da yake magana da manema labarai jita a Abuja, mai tsawatarwar ya bayyana yanda ya fara kagowa da kafa shirin na Ruga a Jihar Abiya, lokacin da yake matsayin gwamnan Jihar a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya bayyana cewa, lokacin a matsayinsa na gwamnan Jihar ya samar da filayen zama ga al’ummar Fulani a Umuahiya.

A cewar shi, ya kafa shirin na Ruga a jihar wanda kuma ya zauna daram ba tare da wata hayaniya, zargi ko kyashin wani abu ba, a tsakanin al’ummar na Jihar ta biya da kuma ‘yan’uwansu da suka zo daga arewacin kasar nan suke kuma zaune a can jihar.

Sanatan ya ce, “In na ji mutane suna magana a kan Ruga, nakan yi mamaki. A shekarar 2001,  na kafa shirin Ruga a Abiya. A Lokpanta, na gina Ruga a wajen ana kuma sayar da shanu a Umuahiya da Aba. A shekarar 2001, na gayyaci al’ummar Hausawa inda suka zabi Aba da Umuahiya.    

“Mun zauna mun tattauna da su, tattaunawa na gaskiya, muka cimma yarjejeniya a kan zan samar masu da fili da Ruwa, Lantarki da dai dukkanin abin bukata, amma a nan wajen ne za su takaita. Na hau manyan motocin bas kirar Coaster guda biyar a tare da wakilansu inda muka zagaya na nuna masu filin da na ba su, wanda kuma kowa ya ji dadi ya kuma aminta da hakan.

“Na kuma zauna da al’ummun wajen muka tattauna a Lokpanta, inda a nan ne aka samar da babbar kasuwar shanu a kudu maso gabas da kudu maso kudancin Nijeriya har a yanzun haka. Don haka lamarin ya danganta ne da yanda aka bullowa mutane da shi.

“Tabbas ya kamata a kowane lokaci in gwamnatin tarayya za ta bullo da wani sabon shiri ta tattauna da mutane sosai ta wayar wa da mutane kai sosai a kana bin da shirin ya kunsa, ba kawai ta yi gaban kanta ba.

Sam mutane a kauyaku ba su fahimci abin da Ruga ke nufi ba, sai su tsorata, su dauka za a zo a kashe su ne.”

Exit mobile version