Connect with us

ADABI

Ni Na Fara Wallafa Littafin Tarihin Shata A Duniya (I)

Published

on

Na fara son Alhaji Shata da wakokinsa tun cikin 1974 lokacin ina tare da iyayena a Angwan Kanawa, Kaduna, mahaifina ya na koyarwa a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna. Sa’ilin ban wuce shekaru 6 da haihuwa ba. Tun lokacin son da na ke ma Mamman Shata na musamman ne. Tun iyaye na ba su fahimta har su ka gane. Ko a Telebijin aka nuno shi ya na waka na kama murna kenan, da zaran kuma an dauke wuta kafin ya ida wakar, to har kuka na ke yi kuma na dinga fushi kenan har safe.

Ni babana ba ya da wata alaka da Shata, amma ganin ina son sa ya kan zaunar da ni ya bani labarin sa, na zuwan da ya ke yi a RTK Kaduna (watau BCNN da kuma daga bisani NBC) a tsakanin 1969 da 1972 lokacin mahaifin nawu na aiki a can, da kuma ziyarar da ya kan kai ma amininsa Alhaji Hamza Kankara har Musawa lokacin ya na aiki a gonar mahaifin Shata Malam Ibrahim Yaro.

Sai cikin 1975, watarana da babana za ya tafi Katsina, ya ce in shirya in bishi tunda a sannan ban shiga firamare ba, a sa’annan ya na da wata mota Morris Marina. Ba zan manta ba mun shiga Funtuwa a tsakanin mangariba da isha’I, har mu ka bi santar gidan Shata. A daidai kofar gidan Shatan mun zo wucewa sai babana ya ce da ni: ‘Ali Gadanga, ga gidan Shata, ga shi can ma zaune kofar gida’. Ya fadi mani hakane saboda sanin da ya yi ina matukar son makadin. Sai na ce masa ‘mu tsaya in gan shi’ Sai ya  ce : ‘a’a, saboda mu na sauri’. Amma gab da za mu wuce Allah Ya jiye mani muryar Shatan, na ji ya na cewa ’a zo a kwashe kwanonin abincin nan’. Wannan kenan.

A tsakanin 1976 da 1978 an kai ni riko Daura wajen wana Ahmed Ibrahim Kankara, lokacin ya na aiki a can. To a can mu kan ga wasan Shata a kofar fada in ya ziyarci Sarki, da kuma Neja Club da ke kan hanyar Zangon Daura. Har ma nine Shatan Islamiyya Firamare inda na yi karatu. Idan an gama shara da marece, sai a zo bakin ofishin Hedimasta a yi wasan kwaikwayo, to nan ni kan dan yi wakokin Shata ‘yan ajinmu na yi mani amshi. Sunan Hedimasta din mu Hamisu Famili, wanda daga baya ya zama Matawallen Daura.

Cikin 1979 ina aji 5 na Firamare a Kankara (bayan babana ya bar Kaduna, mai riko na kuma na bar Daura) sai Shata ya zo kamfe na GNPP a cikin tawagar ‘yan siyasa a Kankara, nan mu ka yi ta bin motar sa da gudu aka zagaya gari da mu, shi kuma ya na waka. Wannan ta sa wanshekare ni da abokina Garba (Abubakar) Suleiman Kankara (yanzu yana aiki a Dakin Awon Jini na Asibitin Tarayya ta Katsina) mu ka sawo littafi mai warka 40 mu ka fara rubuta tarihinsa, har ma mu ka samu shuwagabannin GNPP na yankin Kankara su ka bamu abinda su ka sani gameda makadin. Amma a lokacin ana ta yarinta, ba mu dauki abin da gaske ba, sai dai mi? abin da yaro ya ke so kuma ya girma da abin nan a zuciyar sa watarana sai ya tabbata, to ashe Allah Za Ya tabbatar da abin a gaba.

A tsakanin 1986 da 1994 ina karakaina, in kai gwauro in kai mari a tsakanin Daura, Malumfashi, Dutsinma, Kankara, Funtuwa da Katsina, duk samari masoya Shata sun sanni kuma inda duk na je ana maraba da ni ana kuma son in zauna in bada labari sabo na Shata da na kalato. Sai da ta kai ma a Malumfashi da Daura mun kafa Kungiya ta masoya Duna na Bilkin Sambo.  Cikin 1987 na fara zuwa gidan Shata kuma mu na haduwa da shi a Zariya (a Magume gidan Sani Gadagau, Bakatoshi) da Kano da Funtuwa da Katsina (Nasara Guest Inn, gidan Sa’in Katsina). Ba wanda ya fara kai ni ya gabatar da ni wurin sa, ni na kai kaina, musamman saboda dalilan can na sama. Cikin 1990, ina tammanin ma ran Lahadi 3/9/1990 ne lokacin na kammala karatu a Kwalejin Ilimi mai zurfi (CAS) Zariya na tafi Funtuwa na samu Shata na kai masa wani littafi da na rubuta mai suna Karon Battar Karfe (na yaki ko hikaya ne), na kwana har da safe ni da shi da Mati Bomber mu ka tafi ofishinsa na kan hanyar Zariya, lokacin ya na shugaban Jam’iyyar SDP, nan mu ka wuni. Na gabatar masa da littafi, na kuma bukaci ina so ya biya kudi a wallafa littafin. Amma ban samu nasara ba, don bai ce ya amince ba, bai kuma ce ba ya yi ba. Na yi wakokin Shata a CAS Zariya a kungiyar mu ta Hausa, a matsayi na na Shatan CAS, sannan da ina Jami’ar Ahmadu Bello na zama Shatan ABU na kungiyar Hausa, duk don dalilin soyayya ta da Shata, mai benen-bene na Izzatu Musawa. Ka ga kenan wanda duk za ya bada labarin ko nuna son Shata baya na ya ke. Wanda duk ya sha wuta baran tsire ne, kuma labarin dare a tambayi kura.

 

Mafarin Tunanin Wallafa Littafin Tarihin Shata, 1992

A cikin 1992, lokacin ina karatun Digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello, aji biyu (300 Lebel) Allah Ya hada ni da wani yaro a Jami’ar mai kwazo mai ilimi ana ce masa Kabiru Husaini Gwangwazo, kuma lokacin ya na karanta Digiri akan harshen Turanci. Mun fara haduwa da shi a taron OUA na wasan kwaikwayo na daliban Turanci, inda ya fito a matsayin Shugaban Zaire watau Mobutu Sese Sekou. Sha’awar da ya bani ta sa na nemi mu yi abotaka, ya amince. Muna nan, mu na nan, ya zo wuri na, nima in je wurin sa. Sai rannan na dauki littafi na na Hausa da na rubuta mai suna Sako Daga Birni Al-Shabdad (na hikaya ne) na ba Gwangwazo domin ya duba mani. Bayan kwanaki, sai wani dan rikici ya sanya aka rufe Jammi’ar. Ina gida Kankara, sai na yi amfani da wannan damar na tafi Kano wajen sa domin in amso littafin. Sai na tarar an tsare shi a Ofishin ‘Yan sanda na Bompai saboda littafin Danmasanin Kano da ya rubuta, aka kaddamar, amma a baya ya ranci kudaden mutane saboda hidimar bai biya su ba, sun sa an kama shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: