Connect with us

LABARAI

Ni PDP Za Ta Tsayar Dan Takarar Shugaban Kasa – Makarfi

Published

on

Mai neman tsayawa Jam’iyyar PDP takarar shugabancin kasar nan, Sanata Ahmed Makarfi, ya ce, yana da tabbacin shi ne Jam’iyyar za ta tsayar a matsayin dan takarar na ta a babban zaben 2019.
Makarfi ya fadi hakan ne cikin wata tattaunawa da manema labarai ranar Lahadi a Legas.
Tsohon gwamnan na Jihar Kaduna, wanda kuma ya taba rike shugabancin kwamitin rikon kwaryar Jam’iyyar, yana daya daga cikin mutane 12 da suke hankoron Jam’iyyar ta tsayar da su.
Makarfin wanda a kwanan nan ne ya kammala tarukan da yake yi da ‘ya’yan Jam’iyyar na shiyyar Kudu maso yammacin kasar nan, ya ce, rawar da ya taka a matsayin sa na shugaban kwamitin na rikon kwarya, shi ne zai ba shi daman cinye zaben fitar da gwanin.
“PDP ta dawo sabuwa da karfinta saboda rawar da na taka. Kafin nan ana daukan Jam’iyyar a matacciya ce har sai da na zama shugaban kwamitin na ta, sai na dawo da ita da karsashinta.
“Ba wani dan takarar da ya taka wa Jam’iyyar irin rawar da na taka mata. ‘Ya’yan jam’iyyar da suka san aikin da na yi wa Jam’iyyar, sun tabbatar mani da ni ne za su zaba, ba kuma za su sayar wa da kowa kuri’un su ba a ranar zaben.
“Ban taba ficewa daga Jam’iyyar ba, tun daga ranar da na shiga cikinta.
Makarfi ya ce, sabanin abin da wasu ke tunani, kudi ba sune za su yanke hukuncin wanda zai sami tikitin Jam’iyyar ba, kamar yadda kudin ba su taba zamar da wani Shugaban kasar nan ba.
“A yaushe ne Nijeriya ta fara samar da Shugabanta saboda yana da kudi? tsaffin shugabannin kasar nan, Alh. Shehu Shagari, Cif Olusegun Obasanjo, Alh. Umaru Musa Yar’Adua, Dakta Goodluck Jonathan da mai ci yanzun, Shugaba Muhammadu Buhari, duk ba kudin ne suka maishe su shugabannin kasa ba.
“A daya daga cikin Jihohin kudancin kasar nan da na ziyarta, wani wakilin Jam’iyyar ya shaida mani cewa, wani dan takarar ya raba masu kyautuka da kudade domin su zabe shi, to amma ni ba ni da kudi ko kyautukan da zan raba masu domin su zabe ni a zaben fidda gwanin, za kuma su zabe ni domin sun san ni na fi cancanta da aikin.
Kan batun samar da mataimakiyar Shugaban kasan nan, Makarfi ya ce, ya so mace ne ta rufa masa baya in har ya ci zaben fitar da gwanin, amma wacce ya so ta rufa masa bayan ta ki aminta da hakan, sai ta zabi wani mukamin da bai kai wannan din ba.
Ya koka kan yadda har yanzun mata a kasar nan ba su tunkari a ba su matsayin shugabancin kasar nan ko na mataimakin shugaba ba, ya yi nu ni da cewa, ai wadannan mukaman ba a kebe su ga maza ne kadai ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: