Nijar Ta Cika Shekaru 65 Da Samun 'Yancin Kai
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijar Ta Cika Shekaru 65 Da Samun ‘Yancin Kai

bySadiq
2 years ago
Nijar

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, ya jinjina wa al’ummar kasar saboda yadda suka jurewa matsalolin da suka biyo bayan takunkumin kungiyar CEDEAO da UEMOA.

A yayin da a ranar Litinin 18 ga watan Disamba kasar Nijar ke bukukuwan cika shekaru 65 da zama jamhuriya, shugaban gwamnatin mulkin sojin, Janar Abdourahaman Tchiani, ya yi jawabi ta kafafen yada labaran gwamnati a ranar Lahadi, domin bitar halin da ake ciki a kasar a tsawon wadanan gwamman shekaru.

  • Al’ummar Chibok Sun Gudanar Da Bikin Al’adu A Abuja, Sun Buƙaci A Mayar Da Su Gidajensu
  • Kasashe 10 Da Bashin IMF Ya Yi Wa Katutu

Yana mai jaddada alwashin samar da mafitar dambarwar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Batun tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya tabo a wannan jawabi da ke zuwa a wani lokacin da Nijar ta yanke hulda a fannin tsaro da tsohuwar kasar mulkin mallaka Faransa, inda ya ce tuni aka fara ganin haske a fagen daga.

Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce “a dalilin nasarorin da dakarun tsaronmu ke samu, al’amuran tsaro sun fara daidaituwa sannu a hankali.”

Ya ce “abu na zahiri shi ne yadda wasu ‘yan gudun hijirar cikin gida suka fara koma garuruwansu, haka kuma makarantu kusan 200 sun sake budewa a jihar Tilaberi, bayan da suka kasance rufe a tsawon shekaru kusan biyu sanadiyar matsalolin tsaro, sannan mun dauki matakan samar da tsaro kan hanyar shigo da kayan abinci da magunguna da kuma yadda harakokin yau da kullum suka fara dawowa a yankuna da dama.

A cewarsa, “kafuwar kungiyar AES mataki ne na ci gaban kudirin mayar da Sahel wani yankin zaman lafiya da jin dadin rayuwa.”

A fannin yaki da cin hanci, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce “hukumar COLDEFF na nan kan aiki domin bude bincike kan badakalolin da take da hurumi akan su.”

Yana mai jaddada goyon baya ga mambobin wannan hukuma su yi aiki dangance da rantsuwar da suka yi ta yadda al’umma za ta ba su yarda.

Ya kara nanata alkawalinsa da na takwarorinsa na CNSP da gwamnati cewa, ba za su taba bai wa kowa kariya ba. Sanannen abu ne kamarin da cin hanci ya yi a wannan kasa na daga cikin manyan dalilan da ya sa suka hambarar da gwamnati, in ji shi.

Ya kuma yi amfani da wannan dama don mayar da martani ga wadannan kungiyoyi dangane da sharudan da suka gindaya a baya bayan nan.

Ya ce ba za mu taba amincewa dukkan wani jan rai ba, ba kuma za a kara tsoratar da mu ba ko a shimfida mana wata ka’ida ba. kanmu hade yake domin ceton kasa.

Janar Abdouraamane Tchiani ya sha alwashin yin abubuwan da ke yiwuwa, domin tabbatar da ci gaba samar da tsaro da ayyukan jin dadin rayuwar jama’a da hada kan ‘yan kasa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?
Kasashen Ketare

Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?

September 28, 2025
Next Post
Guardiola Ya Soki ‘Yan Wasan Manchester City Kan Rashin Kwazo

Guardiola Ya Soki 'Yan Wasan Manchester City Kan Rashin Kwazo

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version