Nijar Ta Yi Bikin Cika Shekaru 61 Da Zama Jamhuriya

A jiya 18 ga watan Disamba Jamhuriyar Nijar ke bikin cika shekaru 61 da zama Jamhuriya, dama ce ga shugaban kasa na gabatar da  jawabi ga alummar kasar kan halin da ake ciki.

A jawabi da Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya gabatar zuwa yan kasar ,ya na mai bayyana sabin matakan da gwamnatin kasar tadau domin  tabbatar da tsaro da kuma sake karfafa hulda da wasu kasashe dangane da yaki da yan ta’adda masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

Shugaba Issoufou ya bayyana tsarin samar da cimaka mai rahusa , tsarin da gwamnatin Nijar za ta  mayar da hankali  ganin karancin abinci ko cimaka da ake fuskanta  a wasu sassan kasar. A karshe Shugaban kasar ya jaddada aniyar sa ta sauka daga karagar mulki tareda shirya zabe cikin lokaci da kuma mika mulki zuwa zabbaben Shugaban kasa .

A wani rahoton kuma, a yayin da take bukin cika shekaru hudu da kafuwa, jamiyar Adawa ta MPN Kishin Kasa ta yi bukin rantsar da tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar Ibrahim Yakouba, a matsayin dan takarar da zai tsaya mata a zaben shugaban kasa na 2020.

Dubban magoya bayan MPN Kishin Kasa da suka fito ciki da wajen jamhuriyar Nijar ne suka halarci gangamin da uwar jamiyar ta shirya a dakin taro na Palais Du 29 Juillet, dake birnin Yamai, domin jaddada goyon baya ga shugabanta Ibrahim Yakouba.

Tuni magoya bayan wannan jamiya suka fara jan damara don ganin nasu dan takarar ya samu cin nasara a zaben badi, kamar yadda shugabar matan kishin kasa Hajiya Baraka Sabo ta bayyana.

Jamiyar MPN Kishin Kasa mai manufofin hada kan kasahen Afrika, ta gayyaci yan siyasa daga kasashe da dama na nahiyar domin halartar shagulgulan wannan buki wanda ta wani bangare ke da matsayin murnar cika shekaru hudu da kafuwarta.

A karshen shekarar 2015 ne Ibrahim Yakouba da wasu abokansa suka kafa jamiyar MPN Kishin Kasa, bayan da jamiyar PNDS Tarayya mai mulki ta dakatar da shi daga sahun ya yan ta.

Jamiyar wacce a yau ke adawa da gwamnatin Renaissance na da kujerun wakilci a Majalisar Dokokin kasa, abin da ya sa magoya bayanta ke ganin za su bada mamaki a zabubukan 2020 da 2021.

Exit mobile version