Connect with us

MAKALAR YAU

Nijeriya 2019: Ina Tudun Dafa Wa? (II)

Published

on

Ba a samu lokacin da za a iya cewa dimokaradiyya ta dawo daram  ba kamar wannan zangon wanda ya fara daga shekarar 1999 zuwa halin da ake ciki yanzu. Saboda duk wasu gwamnatocin farar hula da aka taba yi a baya, sun fuskanci kutsen soja mai yiwuwa ma wannan kutsen da babu gaira babu dalili da sojojin suka yi ta yi shi ya mai da kasar nan baya ta fuskar siyasa, har ma da tattalin arziki. Da siyasa da tattalin arziki  ‘yan tagwaye ne da ba a raba su, abin da ya shafi daya shakka babu sai ya shafi dayan. 

A gwamnatocin farar hular da suka gabata, ba wadda soja ya bar ta ta kai matsayin da za ta tafi da kafarta. Duk lokacin da dimokaradiyyar ta fara ta-ta-ta sai kawai a tashi da jin begilan shi ke nan kuma sai baba-ta-gani. Soja sun kasa fahimtar cewa yadda dan’adam yake koyon komai sannu a hankali. Ba zai yiwu a haifi yaro a yau, ya kuma mike yana tafiya ba har sai ya bi wasu matakai na rayuwa. A wannan matakan kuma akwai tarin matsaloli masu yawan gaske da za su dinga bijiro masa. To haka abin yake a siyasa. Lokacin jamhuriyya ta farko soja ne suka hambare ta, ranar 15 ga Janairun 1966. Haka bayan dawowa jamhuriyya ta biyu, sojojin suka sake dawo wa da sunan gyara kasa, da haka suka hambare gwamnatin ta farar hular ranar 31 ga Disambar 1983. 

Jamhuriyya ta uku ko ba a fada ba, kowa ya san dimokaradiyya ce da aka dora harsashinta a kan tubalin toka. Domin ungulu da kan zabon da Janar Babangida ya yi babu wani dan Nijeriya da ya gamsu da cewa da gaske soja ya yi niyyar barin fadar mulki. Wato za su koma bariki su dangana da albashinsu, su kuma himmatu da aikin su na tsaron iyakar kasa. Saboda me mutane suka yi  shakkar hakan? Amsar ita ce tsawon lokacin da aka dauka na wannan shirin mika wa farar hula mulki da kuma abubuwan da suka faru baya. Ko da dai ina gudun tsawaita rubutun ka da ya dauke ni makonni da yawa, amma bari mu dan duba kadan daga cikin wasu tsare-tsaren da gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi ko da a gurguje ne.

Babangida ya jawa ‘yan Nijeriya rai da gaske kuma ya iya karantar kwakwalen ‘yan Nijeriya da kuma tunaninsu. Ya karanci sarakunan gargajiya, da malaman addini, da malaman jami’o’i, da shugabannin kungiyoyi, da kuma sauran talakawan kasa. Ba ta batun soja ake ba wadda da ma a cikinsu yake.

Kalilan ne a cikinsu suka tsallake tarkon Babangida, amma ma fi yawansu ya iya siyansu wanda kuma ya gagara siya an bi ta wata hanyar an rufe masa baki. Ta haka ya iya sarrafa kowa yadda ya so, ya kuma ja zarensa na tsawon shekara takwas. Shekaru shida a Dodan Barrack, biyu a Dutsen Aso. Babangida na daya daga cikin shugabannin Nijeriya da bai yarda da amfani da karfi kawai wajen cim ma bukatarsa ta mulki ba. Yakan yi amfani da karfi a wurin da ya fahimci sa karfin shi ne mafita. Haka kuma yakan sa hikima da dabara a fagen da ya fuskanci sa karfi ba zai ba da sakamakon da ake bukata ba.

Shi a takaice ya yarda  da a ciza a hura. Wannan ne ma saboda kwarewarsa a wasa da hankulan ‘yan Nijeriya ya sa har a ake yi masa lakabi da sunan wani shaharren dan kwallon lokacin, dan kasar Argentina mai suna ‘Maradona’. Wasu kuma suna kiransa da “Mazari ba a san gabanka ba”. Lokacin da Babangida ya kwaci mulki a hannun Janar Buhari a Agustan1985 sai ya fito da tsare tsarensa na mayar da Nijeriya tafarkin dimokardiyya. Kan ka ce kwabo ‘yan siyasa sai murna, wato abin jiya zai dawo.

Da haka ya fara jan hankalin ‘yan kasa, ya kafa kwamitin jin ra’ayin ‘yan kasa a shekarar 1986 da zai tattauna da ‘yan kasa da kuma shirya muhawarori a kan kundin tsarin mulki da za a yi amfani da shi wajen dawo da dimokaradiyya. Sai Kwamitin da zai bibiyi kundin tsarin mulkin kasa na 1963 da kuma na 1979 da ya kaddamar a Satumbar 1987. Wannan kwamiti za su yi aikinsu ne da shawarwarin da kwamitin jin ra’ayin ‘yan kasa a kan siyasa ya turo musu. A karshe sai Kwamitin da zai duba daftarin kundin tsarin mulkin da wancan kwamiti na baya ya rubuta. Shi wannan kwamiti an kaddamar da shi a watan Mayun 1988. Haka kuma kowacce karamar hukuma ta zabi wakilinta da a wannan kwamiti, da zai fito da kundin tsarin mulki na 1989. Da haka aka samar da kundin tsarin mulkin 1989 aka kuma bai wa ‘yan kasa damar fito da jam’iyyun siyasa. Amma abin kaico duk jam’iyyun da aka fito da su sai Babangida ya sa kafa ya shure su, daga karshe gwamnatinsa ta kafa jam’iyya biyu rak wanda idan ka na ra ‘ayi ka zabi daya. Jam’iyyun da marigayi Cif Ojukwu ya kira da suna “Tagwayen Babangida”.

A takaice dai da wannan jam’iyyu na aka gabatar da zaben kananan hukumomi a shekarar 1991 da zaben ‘yan majalisun tarayya, gwamnoni da kuma ‘yan majalisun dokoki a shekarar 1992 da kuma zaben shugaban kasa a Yunin 1993 kafin haka an ta daga zaben da haramta wa wasu ‘yan siyasar takara. Shekaru kusan takwas Babangida ya share yana tsara yadda za a dawo tafarkin dimokaradiyya! Sai ka ce wani sabon ‘yanci ake kokarin bai wa Nijeriya. Wannan kuma ba shi ne ba, sai bayan an gama duk wannan shirin, an yi zaben shugaban kasa ana sanar da sakamakon Babangida ya umurci dakatar da sanarwar. Ya kuma rusa zaben da kuma duk dabarar ci gaba da mulki ta kare masa ala dole ya kafa wani gwamnati na rikon kwarya wai da zai  shirya sabon zabe ya mika mulki ga zababbiyar gwamnati. Wannan shi ya kawo Cif Enerst Shonikan kan mulki.

Daga nan rikice-rikice suka balle a kasa, ba a je ko ‘ina ba Janar Sani Abacha ya fito ya kori Shonekan shi ke nan aka koma mulkin soja. Dawowar Abacha ne ya kara farkar da ‘yan kasa cewa soja fa sam ba su da niyyar barin mulki har abada, manufarsu daya ce ta jujjuya mulki a tsakaninsu. Wannan shi ya haifar da bullowar kungiyoyi daban-daban masu rajin kare hakkin bil’adama da kuma masu fafutikar a dawo tafarkin dimokaradiyya. Kuma galibi Yarbawa su ne wadanda suka fi zakalkale wa wajen kafa irin wadannan kungiyoyi. Kamar su NADECO ta su marigayi Cif Abraham Adesanya, da JACON ta su marigayi Cif Gani Fawehinmi, da CD ta su marigayi Dakta  Beko Kuti akwai kuma kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere da dai sauransu. Kodayake a yankin Gabas su ma akwai kungiyoyi irin su MOSOP ta su marigayi Ken Saro Wiwa da ire irensu. A Arewa kuwa babu irin wadannan kungiyoyi, hana rantsuwa akwai Rundunar Adalci ta Malam Abdulkarim Dayyabu. 

Sannan kuma akwai wasu ‘yan siyasa su tara da su ka hadu suka kafa wata kungiya da suka ba ta suna G9 mutanen su ne: Cif Bola Ige, da Cif Solomon Lar, da Dakta Aled Ekueme, da Iyorchia Ayu da, Sanata Francis Ellah, da Farfesa Jerry Gana, da Malam Adamu Ciroma, da Alhaji Abubakar Rimi, da Alhaji Sule Lamido. Daga baya suka kara yawa suka koma su talatin da hudu G34. Su ne suka rubuta wa Abacha takardar cewa lallai sai ya janye kudirinsa na neman zarcewa daga mulkin soja zuwa na farar hula bayan ya kirkiri jam’iyyun nan guda biyar da kowacce take zawarcin da ya shigo cikinta ya yi mata takara. Jam’iyyun da marigayi Bola Ige ya kamanta su da “yatsun kuturu”.

Yunkuri  da gwagwarmayar a dawo ga tafarkin dimokaradiyya na wadannan kungiyoyi da kuma sukar da suke yi wa gwamnatin soja ta Janar Abacha ya sa suka saka kafar wando daya da su. Abacha bai yi wata-wata ba ya yi musu dirar mikiya da kamu da dauri wadansu suka tsere suka bar kasar wasu kuma farashin da suka biya shi ne ransu. Haka aka yi ta fama har rasuwar Abacha da hawan Janar Abdussalami Abubakar wanda shi ne ya dawo da Nijeriya tafarkin dimokaradiyya a watan Mayun 1999.

Harun U. Jahun, 09092389231
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: