Connect with us

Uncategorized

Nijeriya 2019: Ina Tudun Dafa Wa (III)?

Published

on

Ba za a iya cewa dimokaradiyya ba ta kawo ci gaba ba, sai dai ci gaban bai kai matsayin da ya cancanci a ce haka kasarmu take ba. Abin da zabe na gaba zai nuna shi ne tsakanin wadanda su ka yi tsawon mulki suka sha da kuma wadanda suke ta suka a da, yanzu kuma sun yi an ga kuma su ma irin nasu kamun ludayin. Wannan ne ya kawo ni ga kan gabar taken mukalar tawa na shin a shekara mai zuwa ina ne tudun da fa wa tsakanin bangarorin nan guda biyu? Duk da cewa akwai wasu jam’iyyun amma ba wanda yake tunanin cewa makomar zaben Nijeriya ba a tsakanin APC da PDP ba ne. Bari mu duba PDP a baya da kuma APC a yanzu domin neman bakin zaren.
Gwamnatin PDP ta yi shekara sha shida tana mulki a Nijeriya kuma har ya zuwa yanzu ita ce dadaddiyar jam’ iyyar da babu sa’arta a cikin sauran jam’iyyu balle kuma a samu yayarta. Shekara ashirin ke nan cif da kafa ta kuma cikin mutanen nan G9 da suka yaki gwamnatin soja ta marigayi Janar Sani Abacha su ne suka kafata. Kamar yadda cikin waddanda suka kafa jam’iyyar yake fada cewa sun kafa ta ne domin kawo ci gaban kasa ta fuskar tattalin arzikin kasa da dimokaradiyya da yaki da cin hanci da rashawa da hadin kan ‘yan kasa da kuma tabbatar kawo karshen mulkin soja na har abada a Nijeriya.
A haka jam’iyyar ta fara kuma ta dauko Cif Obasanjo ta ba shi takara ta tallata shi Kudu da Arewa,Gabas da Yamma har ya samu karbuwa aka zabe shi. Bayan rantsar da shi, abin da Obasanjo ya fara shi ne yi wa manyan sojoji ritayar dole domin kamar yadda ya rubuta a cikin littafinsa MY WATCH ya ce matukar ya bar irin wadannan manyan sojojin to ba makawa babu inda dimokaradiyya za ta je a Nijeriya abin da ya faru baya ne zai ci gaba da maimaita kansa wato juyin mulki.
Amma a tsawon wannan shekara sha shida jam’iyyar ta zama duk wani abu marar kyau ana danganta shi da jam’iyyar saboda salon mulkinta da kuma yadda take abin da ga dama. Ma fi yawa daga cikin wadanda suka yankewa jam’iyyar cibiya da kuma rada mata suna sai da suka fice suka bar ta. Jam’iyyar da aka kafa da ‘yan uwantaka da kaunar juna sai da ta zama kamar kunamin da aka zuba su cikin kwando daya kowanne yana harbin dan uwansa. Har ta kai da babban mawakin jam’iyyar na lokacin ya rera wakar “shegiyar uwa mai kashe ‘ya ‘yanta”.
Marigayi Sunday Awoniyi na daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar amma saboda matsalolinta ya bar ta. Ya taba koka wa a kan abubuwan da suke faruwa a jam’iyyar kafin daga karshe su fice cewa “ manufofin jam’iyyar da ta gabatarwa ‘yan Nijeriya har suka aminta suka zabe ta a matsayin tsarin da za a yi amfani da su domin shigabantar kasa an yi watsi da su. An binne manufofin jam’iyyar kamar yadda ya ce har masu mazarin siyasa suna fadin cewa jam’iyyar ba ta da wata manufa da akida.”
Shekara uku ke nan da kawar da PDP kuma yanzu an fara shiga kakar zaben badi da za a yi shin kwalliyar talaka ta biya kudin sabulu wannan shi ne babban kalubalen da ke fuskantar zaben 2019. Mun ga shekara uku cikin hudun na gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari wanda ‘yan Nijeriya suka zabe ta kwansu da kwarkwatarsu da tsammanin samun sa’ida daga bakar azabar da suka zargi gwamnatin PDP ta kakaba musu. Amma ga dukkan alamu jin dadi da walwala ba su samu ba. Abin da ake ji daga bakunan mutane shi ne a dawo musu da wahalar da shekarun da suka gabata maimakon wannan ukubar da suke dandanawa yanzu.
Tun farkon kwanakin wannan gwamnatin aka fara gane cewa akwai matsala a kan wannan canjin da mutane suka kasa, suka tsare,suka raka, sannan kuma suka jira. Gwamnati ce da ta fara tafiyar sabon gurgu, kuma har yanzu taku bai canza ba. Abubuwan da su ya sa aka yi gangami da kudi da lafiya har ma da rayuka aka zabi gwamnatin ba su wuce inganta rayuwar ‘yan kasa da habaka tattalin arziki sannan da tsaro. Wadannan abubuwa su aka fi zargin gwamnatin PDP da lalatawa. Sai kuma a kara da yaki da cin hanci da rashawa abubuwan da wannan gwamnati kullum ta fi azuzuta yaki da shi.
Yanzu lokacin fuskantar wadanda aka yi wa alkawuran da suka fi shurin masaki yawa ya dawo. Dole a yi tunanin abin da za a sake fada musu a karo na biyu. Su kuma yanzu sun fara tunanin ina ne tudun da za su sake dafa wa don su tsira domin sun riga sun yi zaben kure akwati da fatan a dimokaradiyyance kakarsu ta yanke saka, amma yau da gobe ta tabbatar musu da cewa hanyar jirgi daban ta mota daban. Da alama ma dai wasu suna kukan cewa “an ya ba canjin rigar mahaukaci muka yi ba?”
Mu fara da alkawuran da aka yi lokacin zaben 2015 a kan kyautata rayuwar talakan kasa. Da farko an ce za a sai da man fetur a kan Naira Arba’in kowacce lita. Sai aka kara naira dari da biyar ba fa ta batun cire tallafin man fetur din a ke ba. Lokacin da PDP ta yi yunkurin cire tallafi ba irin ta da jijiyar wuyar da wasu daga cikin masu jagorantar gwamnatin nan ba su yi ba.
Da damansu sun jagoranci zanga-zanga na tsawon kwananki suna ta tofin ala tsine. Amma babu wani gamshashen bayani yau a ka cire shi. Cikin alkawuran da aka yi an ce madarar gwangwani da taliya da sauran kayan masarufi da za su inganta rayuwa za a sayar da su kasa da yadda ake sai da su a gwamnatin PDP, amma yau sai kudadensu ya nunnunka baninki.
Batun kuwa tattalin arzikin kasa sai mu ce idan ‘yan kudu Yarabawa sun ce son barka saboda tuwonsu mansu shakka babu ga ‘yan Arewa za su ce bayan tiya da sauran lale. Domin ‘yan kasuwa da dama na Arewancin kasar nan sun rasa jarinsu saboda tsananantawar jami’an shige da fice. Kuma hakan yana daga cikin abubuwan da suka jaza wa ‘yan kasar nan tsananin talauci da ‘yun wan da ta addabe su.
Dangane da tsaro Boko Haram su ma alkawarin wata uku aka yi za a kawar da su. Wannan alkawari an yi shi a gidan Gwamnatin jihar Kano. Yau shekara uku Shekau yana sheke ayarsa. Al’amarin tsaro sai yake sake daukar sabon salo yau ban da Boko Haram a Yankunan Maiduguri, ga rigimar makiyaya da Fulani a jihohin Taraba, da Binuwai da kuma Filato. Ga harin mahara a jihar Zamfara sannan garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a jihar Kaduna.
Wani abin da zai sa duk mai karanta tarihi ya kara jinjinawa da mutunta marigayi Nelson Mandela na Afirka ta Kudu shi ne idan an duba rayuwar ‘yan siyasar Nijeriya. Daga tsohon shugaban kasa Obasanjo zuwa shugaba na yanzu Buhari babu wanda bai yi wa Nijeriyawa alkawarin mulkin wa’adi daya tal ba, amma da lokaci ya yi sai su ka canza. Maganar a nan ita ce shin a wannan bangarori biyu wannene tudun da fa wa?
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: