Khalid Idris Doya">

Nijeriya 60: Gwamnan Gombe Ya Taya ‘Yan Nijeriya Murna

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya shugaba Muhammadu Buhari, da al’ummar Jihar Gombe da Nijeriya baki daya murnar cikar kasar nan shekaru 60 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Ta cikin sakon murnar alamta cikar Nijeriya shekaru 60 da Jihar Gombe kuwa shekaru 24, Gwamna Inuwa Yahaya ya tunatar da al’umma irin sadaukarwa da mazajen farko sukayi wajen gina kasar nan.

A sanarwar mai magana da yawun gwamnan Ismaila Uba Misili ya fitar, gwamnan ya nuna cewa cigaba da bunkasar da jihar Gombe ta samu cikin shekaru 24 abun yabawa da yekuwar murna ne.

Ya ce, “Mu anan Gombe lamarin bikin ya zamto ciki da bai, yayin da muke alamta cika shekaru 24 da kirkiro jihar mu da kuma cikar Nijeriya shekara 60 da samun yanci.

“A yau muna tunawa da irin sadaukarwa da jaruman baya suka yi tare da makasudin samun ingantaccen shugabanci abun kwatance wajen cimma mafarkin kasarmu”.

“A jihar Gombe, muna sanya tubalin bunkasa tattalin arziki da walwala da siyasa, kuma za mu tabbatarda cewa, al’ummah sun sharbi romon demokradiyya daga tushe ta hanyar gudanar ayukkan da za su amfani al’umma.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatin sa ta sanya dambar jadawalin ci gaba na shekaru 10 wanda zai shafi harkokin mulki da tattalin arziki da walwala, domin tabbatarda ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa masu dorewa a jihar.

“Gwamnatin mu tana kuma gina hanyoyi ta karkashin shirin gudanar da hanyoyi kilomita 100 a kowace karamar hukuma a kananan hukumomin jihar guda 11 da ake dasu, domin hade yankuna da al’ummomi tare da bunkasa harkokin sufurin kayayyaki da na al’umma, da inganta sashin ilimi a dukkanin matakai, da bunkasa harkar noma da inganta muhalli ta shirin dashen bishiyoyi na Gombe koriya shar da sauransu don tabbatarda tsaro a jahar mu”.

Ya ce a karkashin mulkinsa, Jihar Gombe za ta riklka waiwaye, domin baiwa al’ummar jihar kwarin gwiwa su kara kaimi, su kuma mayar da jihar wata tauraruwa a arewa maso gabas dama kasa baki daya.

Sai ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da hada kansu wajen gina kasa nagartacciya.

Exit mobile version