A yau 1 ga watan Oktoba ne Nijeriya ta ke cika shekara 59 da samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar kasar Ingila. A duk shekara ana gudanar da bikin tunawa da ranar ‘yancin kan a duk sassan Nijeriya, inda jami’an tsaro suke gudanar da faretin ban girma ga kasar.
An gudanar da wannan bikin yau Talata 1 ga watan Oktoba, a karo na 59. Inda aka gudanar da faretin ban girma da kuma jawabai. Shugaban kasa Buhari ya gudanar da jawabi, inda aka yanka alkakin cikar Nijeriya shekara 59; cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban Kasa Buhari, mataimakin shugaban kasa Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawal, Alkalin-alkalan Nijeriya da sauran manyan jami’an gwamnatin Nijeriya, da ma tsoffin shugabannin kasa da ‘yan siyasa. Ga kada daga cikin hotonan taron.