Salisu Dango Yana">

Nijeriya A Shekaru 60: Ina Mu Ka Fito, Ina Mu Ka Dosa?

Ranar 1 ga watan Oktoban wannan shekara ta 2020, Nijeriya ta cika shekaru 60 da samun ‘ƴancin kai daga kasar Burtaniya. Wadanne buruka kasar Nijeriya da cimma a wadannan shekaru sittin da ‘yancin kai? Wannan ne ta sanyani yin wadannan tambayoyi, Daga ina muke? A ina muke yanzu? Kuma ina muka dosa a nan gaba?

 

Daga Ina Mu Ke?

Bayan samun ‘yancin kai, Nijeriya ta shiga yanayi daban-daban, kama daga zabukan farko bayan samun ‘yanci a shekarar 1964 mai cike da bangaranci da kabilanci da banbancin addinai. Juyin mulki na farko a shekarar 1966 mai cike da kabilanci, bangaranci da ya tafi da rayukan manyan jagororin samo ‘yancin kasar. Juyi juyin mulki na soji lokaci bayan lokaci har zuwa babban zabe na kasa a shekarar 1979.

Wannan zaben, duk da sojoji ne suka shiryashi, sun mika mulki ga farar hula cikin nutsuwa da zummar tunda soji sun gagara to bari a gwada farar hula. Wannan mulki na farar hula saida ya shekara sama da hudu babu tsanin takawa sai karuwar cin hanci da rashawa, almundahana, sace-sacen dukiyar al’umma, rashin hangen nesa da kuma rashin halastacce ingantaccen zabe.

Wadannan dalilan suka sanya soji shirya juyin mulki a shekarar 1983 domin kawo gƴara ga wadannan matsalolin, an garkame mutane a kurkuku na tsawon shekaru 100 ko sama da haka duk don tsoratar da masu wadannan dabi’un, amman har gwamnatin ta kare, ba a samu bakin zaren ba. Wadansu sojawan suka kara kwace mulkin suma a cewarsu za su gyara abin da na baya suka gagara gyarawa, amma su ma shiru.

Wani abin mamaki da tarihi ba zai manta ba a kasar nan shine na wata gwamnati da aka yi ta watanni uku da ba zabarsu akai ba kuma ba sojawa ba, wai ko za a samu zaren amman nan ma babu labari. Soji suka dawo duk domin neman mafita amman har shekarar 1999 ba a samu mafitar ba, yayin da suka yanke hukuncin sake komawa ga mulkin farar hula ko za a dace.

 

A Ina Mu Ke?

Shekarar 1999, watan Mayu, ranar 29, aka rantsar da sabuwar gwamnati mai cike da tsammanin canja lamuran da ‘yan Nijeriya suka fito daga ciki na kunci da talauci, amma sai cin hanci da rashawa suka dawo suka kuma samu gindin zama, kabilanci da bangaranci suka samu masu daure musu gingi, zabuka suka lalace, jam’iyyu suka dimauce, kowa ya zauce da neman abin duniya da mukamai na gwamnati, barna ta zama abin alfahari ga ‘yan Nijeriya, kowa ya mance daga ina ya fito kuma ina ya dosa.

Irin wannan yanayin kasar ta samu kanta har lokacin da ‘yan Nijeriya suka nemi su canzawa kansu yanayin domin kawo sabo kuma ingantaccen shugabanci ga kasarsu a shekarar 2015.

Cike da murna da fatan alheri, ‘yan Nijeriya suka samu kansu bayan rantsar da sabon shugaban kasa daga sabuwar jam’iyya a ranar 29/05/2015 da tsammanin kawo karshen cin hanci da rashawa da ya addabi kasar tun daga ‘yancin kai, rashin zaman lafiya a wasu yankunan kasar, rashin ayyukan yi ga matasa, rashin wutar lantarki, rashin ingantattun hanyoyin sufuri, rashin ingantaccen ilimi, nakasashshen kiwon lafiya, da dai dubban matsaloli da kasar ta samu kanta duk saboda rashin ingantaccen shugabanci da kasar ta yi ta fama da shi na tsawon shekaru.

Kamar da gaske, gwamnatin ta dauki fada da cin hanci da rashawa, a kama wannan a kulle, a kama wannan a kwace, kamo can daure nan, cin hanci sai kara samun gindin zama ya ke yi a cikin manya da kananan ma’aikatun gwamnati da na kamfanoni, kowa burinsa ya saci kayan gwamnati da azurta kansa da iyalansa, kowa neman dama ya ke ya shiga gwamnati domin ya tsira daga tuhuma.

Harkar tsaro sai kara tsoratar da al’ummar kasa take, kullum abin kara ta’azzara ya ke daga wannan bangaren kasa zuwa wancan, sace-sacen mutane don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare har ga iyalan masu mulkin kasar, ‘yan ta’addan Boko Haram suna nan sai kara kai hare-hare suke, ‘yan bindiga dadi kuwa har zaman sulhu ake yi da su da wadansu gwamnonin kasar, har yanzu ba a daina sace shanun Fulani ba, matsalar fadan kabilanci yana nan sai karuwa ya ke, ‘ƴan sanda da sojoji sun dogara da laifukan da talaka zai yi domin karbar kudin beli, kotunan mu sun zama kamar bankuna wurin ajiyar kudi.

Tattalin arzikin kasar nan wanda ya dogara da man fetur, kullum kara rugujewa ya ke, jiya tafi yau. Talauci kara ta’azzara ya ke, rashin ayyukan yi karuwa suke, kaya kullum tsada kuke karawa, kudin shiga wa al’umma kuma raguwa ya ke, rayuwa ta koma gaba kure baya tsiyaki.

Shin ko da akwai wata kasa ko al’umma da ta ci gaba babu ingantaccen ilimi? Shin a kasar nan ana iya samun ingantaccen ilimi kuwa? A kasar da za ka ga mai takardar digiri ba zai iya kare takardar ba, wani lokacin ka ga ana dabi da shi wajen rubuta wasikar neman aiki? Kullum sai kara yawan makarantun Kwaleji da jami’oi muke, kullum kara yaƴe dalibai ake amman babu tunanin abin da za su yi don su amfanar da kasarsu balle kawukansu.

Mafiya yawan yaran da ya kamanci suna azuzuwa domin karatu, suna kan tituna suna barar abin da za su ci, al’ummar kullum kara yawa take, ilimi kuma na kara tabarbarewa. Ko ina kasar ta dosa a haka? Oho.

Lafiya kuwa da ake cewa uwar jiki, babu ingantaccen tanadinta ga ‘yan Nijeriya. Cutar Korona ta sake bankado irin halin ni-‘ya-su da fannin kiwon lafiyan ke ciki. Wai a ce na’urar tallafawa numfashi ma babu a manyan asibitocinmu, ina ga kuma kananan? Babu isassun ma’aikatan lafiya musamman likitoci, ba a maganar magani a asibiti balle a yi maganar kyautarsa.

Hatta shugaban Nijeriya kasar Burtaniya ya ke tafiya neman lafiya, duk girman kasar nan da irin albarkatun da ta mallaka, babu asibiti guda daya da Shugaban kasarta zai iya kwantawa yin jinya don neman lafiya. Shi ya sa kullum asibitocin suke cike da gawawwaki dalilin rashin ma’aikata ko kayan aiki.

A takaice, babu wani fanni a kasar nan da za ka ce yana gudanuwa yadda ya kamata, babu wani buri da kasar ta cimma a wadannan shekarun kama daga samar da Wutar lantarki, hanyoyin sufuri, samar da ruwan sha, ilimi, lafiya, masana’antu, kimiya da fasaha, babu wani fanni da ya kama hanya balle ya isa yadda ya dosa.

 

Ina Mu Ka Dosa?

Dukkanin kasar da ba ta da wani kundi ko kudiri don tafiyar da kasarta, to lalle ba ta kama hanyar kawo karshen matsalolinta ba. Idan kasar nan ta cigaba da tafiya a irin wannan halin na ko-in-kula daga shugabanninta, to babu shakka daga nan har shekaru dubu masu zuwa, a haka kasar za ta zauna.

Kasar da ta gagara samar da wutar lantarki wa ‘yan kasarta, ta gagara samar da ilimi ingantacce ga ‘yan kasarta, babu harkokin lafiya masu inganci, ta barsu a cikin matsanancin talauci, babu ingantaccen tsaro, to ina muke tsammanin zuwa ne a irin wannan halin?

A irin wannan halin, dole ne kullum manyan laifuka su dinga karuwa, yawan kashe-kashe, sace-sace, shaƴe-shaƴe, mace-mace su dinga karuwa. Sanin kowa ne, wannan bashi ne halin da kowacce kasa ke son ‘ƴan kasarta su kasance a ciki ba, amma idan gwamnatoci ba su daina halayyarsu ta mulkin kama karya ba, to lalle ‘ya’yanmu da jikanunmu ba za su yafe mana laifukan da muka yi musu na gagara samar musu da ingantacciyar rayuwa ba.

Fatana a nan shine, Allah ya azurta kasar nan da shugabanni masu hangen nesa, wadanda suke da kishin kasa, wadanda suka san matsalolin kasar da hanyoyin samowa bakin zaren, sannan kuma sai mu cigaba da yi wa shugabannin addu’a domin samun galabar ƴanto kasar nan daga cikin halin da take ciki.

 

Dr. Salisu Dango ya fito daga Yana a cikin Karamar Hukumar Shira da ke Jihar Bauchi.

Za a iya samun sa a imel dinsa  Salisudango@gmail.com ko lambar waya +2348032875677

Exit mobile version