Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

Nijeriya: Attajirar Kasa Mai Dimbin Talakawa

by Tayo Adelaja
August 1, 2017
in MAKALAR YAU
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da Al Amin Ciroma 08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com       

Zan yi amfani da wannan damar na mika ta’aziyya ga dimbin al’ummar Nijeriya da Afrika baki daya kan babban rashin da muka yi na Marigayi Ambasada Yusuf Maitama Sule (Dan Masanin) Kano. Allah Ubangiji (SWT) Ya gafarta masa, Ya kai haske kabarinsa, sannan Ya ba mu damar yin koyi da dimbin darussan da ya bar mana, amin.

samndaads

Idan za a iya tunawa, ranar 12 ga Fabrairun 2016, mun wallafa wannan shafin makalar a nan, daga bisani, na rika samun korafi kan yadda a ka kasa kai karshen nazarin. Ganin haka ne, na sake rubuta shi kammalalle kamar haka, sai a sake karantawa. Ina sauraren shawarwari da karin bayaninku:

Zan iya tunawa a shekarar 2009 da na je sauke farali a kasa mai tsarki, na hadu da wani direban mota da ya dauke ni zuwa birnin Madina daga Makka. A kan hanya hira ta sarke a tsakaninmu, tun da dama mun saba da shi sosai, ya kan kai ni ziyara wurare daban-daban domin ina da ‘yancin yin zirga-zirga a kasar, ba tare da tsangwamar jami’an tsaronsu ba.

Lallai Balarabe ya dauko ta da zafi, don sai da na mayar da martanin cewa kididdigarsa ba ta tushe balle a tarihi. Tattalin arzikin Lagos kadai daga cikin jihohin jamhuriyyar Nijeriya, ya fi na kasar Kenya baki dayanta. Kenya kuwa ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a yankin Afrika ta Gabas, saboda haka na kara tabbatar masa cewa ban yarda da kididdigarsa kan Nijeriya ba. Daga nan na tsuke bakina. Zancen a nan ya kare, aka ci gaba da tafiya, don Makkah zuwa Madina tafiya ce mai tsawon kilomita kusan 584, wadda akalla zai kwashe kamar sa’o’i biyar ana yi.

To, wannan ‘yar mahawarar ta tuno min da wata kididdiga da aka fitar a watan Afrilun shekarar 2014, wadda ta ce Nijeriya ta na da karfin tattalin arzikin da ya kai sama da Dala biliyan 509, a yayin da ita kuwa Afrika ta Kudu tana da Dala biliyan 353.

Kasa mai dimbin arziki da ni’imomi mara misaltuwa ita ce a yanzu ta fada hannun wasu ‘yan tsirarru daga cikin wadanda madafun iko ke hannunsu, suka rika yin watanda da dukiyar kasar.  Kai ka ce suna da cikakkiyar masaniyar adadin kwanakin da za su rayu, wanda watakila su iya cinye dukiyar da suka sata kafin su mutu, amma ba haka abin yake ba. Allah ne kadai Ya bar wa kansa masaniyar ranar da kowa zai mutu. Da yawa ana satar dukiya, a rasa yadda za a yi da ita. Idan an mutu magada su hau kai su rika aikata abin da ransu yake so. Irin wadannan abubuwan ne suka haifar da masifu wadanda hankali bai cika dauka ba a Nijeriya. A yau an wayi gari duk Nahiyar Afrika, da sauran sassan duniya, babu inda talauci da fatara suka yi katutu, rashin ayyukan yi kamar Nijeriya!

A farkon makon nan, kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta fito kwanta da kwartatarta tana zanga-zangar lumana kan karin kudin wutar lantarki da hukumar samar da wutar ta fito da shi. Wannan yunkuri da kungiyar ta yi, alamu ne da ke tabbatar wa al’umma har yanzu da sauran rina a kaba. A kaikaice da ya kamata duk dan Nijeriya da ya san ciwon kansa ya fito kai-tsaye ya marawa gwamnatin Buhari baya kan yunkurinta na yaki da cin hanci da rashawa. Amma ba daidai ba ne mu tankwashe kafa, muna kallon ‘yan tsirarrun mutane wadanda ba su fi karfinmu kora su da cakulkuli ba, amma sun rike mana dukiyar kasa, wanda sakamakon hakan muka  koma bayi a cikin kasarmu ta gado!

Tuni har wasu sun fara neman haddasa rudu a kasar, watakila a tunaninsu canjin da ake tsammani zai zai tabbata ne tun daga ranar farko da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulki. Duk wannan ba wani abu ba ne illa gazawar shugabannin baya, wadanda hakkinsu ne su ilmantar da al’ummar kasar yadda dimokuradiyya take da salon tafiyar da ita. Amma aka kwashi shekaru 16, babu abin da ake yi illa satar dukiyar kasa da cin amanarta.

Mu tuna cewa tun kusan shekaru 10 da suka wuce, Jihar Lagos kadai a Nijeriya ta na da karfin kashi daya cikin hudu na dukiyar kasar nan baki dayanta. Haka kuma tattalin arzikinta ya fi na Kenya, Libya, Ghana da Tunisiya, kamar yadda na ambata a sama. Amma tun bayan waccan kididdigar, a ke ta faman shan bamban game da bunkasar sassa daban-daban ciki har da bangaren sadarwa.

Idan kuma muka waiwaya shekaru 24 da su ka gabata, layukan waya ba su wuce guda 300,000 ba kwata-kwata a Nijeriya, wadanda kamfanin NITEL ne ya mallake su. Amma yau akwai layukan waya fiye da guda miliyan 146 da wasu kamfanonin su ka mallaka. A lokacin babu masana’antar shirin fim ta Nollywood, wacce a yau ake kallo a matsayin ta biyu a fadin duniya wajen yawan shirya finafinai baya ga masana’antar Indiya ta Bollywood. Idan mu ka kara da masana’antar shirin finafinai ta Hausa wato Kannywood da sauransu, to kenan za a iya cewa kididdigar ta ma sha bamban.

Saboda haka abubuwa da yawa sun wakana ga tattalin arzikinmu wanda ya dace a ce an gudanar da kididdigar tun shekara ta 2000 da 2010 kamar yadda ya ke a al’adance duk shekara goma a ke yi. A takaice ma dai kasashe da yawa su na gudanarwa ne duk bayan shekaru uku. Ya kamata a san cewa, wannan bunkasar sun zo ne tun kafin Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya hau karagar mulki.

Idan har a ka yi wannan waiwayen, za a fahimci cewa Nijeriya kasa ce da Allah kadai ya san dimbin arziki da ni’imomin da Allah Ya hore mata. Amma tuni kallo ya koma sama a kasar, bangaren ilmi kadai ya ishe ka misali; babu wata jami’ar Nijeriya ko daya a cikin fitattun jami’i’o’in ilmi 1000 na duniya!

Duk da dimbin arziki da kasaitar kasar, duk da baiwa da basirar da Allah Ya ba wa ‘yan kasar nan, duk da irin albarkatun kasa da ma’adinan da muke da su, amma barayin cikinta sun fi ta arziki a yau, kaico!

SendShareTweetShare
Previous Post

Wata Sabuwa: Masu Mata Sama Da Daya Sun Fi Dadewa A Duniya?

Next Post

Ya Kamata Ronaldo Ya Koma United Da Taka Leda —Meireles

RelatedPosts

Dabi'u

Al’adu Da Dabi’u: An Saki Reshe An Kama Ganye

by Muhammad
12 hours ago
0

Kowace al'umma na da al'adu da dabi'unta wadanda ke bambanta...

Kan Iyakokin Najeriya

Baya Ba Zani: Wadanne Dalilai Suka Sa Aka Bude Kan Iyakokin Najeriya?

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Gwamnatin Najeriya mai abin mamaki, wani lokaci idan ta yi...

Barna

Taimako Ko Barna? 24

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Idan ka gabatar da wannan maudu’in a matsayin tattaunawa a...

Next Post

Ya Kamata Ronaldo Ya Koma United Da Taka Leda —Meireles

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version