Bello Hamza" />

Nijeriya Ba Mabaraciya Bace, Inji Jakada Kayode

Daga Bello Hamza

Kasar Nijeriya ba Mabaraciya bane amma kasa ce mai mahimmanci dake bayar da gudummawa a cikin kasahen duniya, jakadan kasar nan a yankin Atlanta ta kasar Amurka Mista Kayode Laro, me ya bayyana haka garin Atlanta.

Laro Ya yi wannan bayanin ne ga kanfanin dillancin labarai na kasa (NAN) sakamakon karrama wasu yan Nijeriya dake zaune a Amurka da suke bayar da gudummawa domin karfafa fannin samar da kiwo lafiya a Nijeriya.

Wadanda aka karrama sun hada da Dakta Ezekiel Macham Mona kungiyar Zumunta, da Emelia Orubele na cibiyar “Nigerian Chamber of Commerce” da kuma Dajta Segun Ajayi na  “Hospitals for Humanity”

Sauran wadanda aka karrama sun hada da Misis Bibian Shaku na “House of Globalisation” da  Dakta Charmaine Emelife of Association  na “Nigerian Physicians in the Americas”.

Wata kungiyar mazauna Amurka mai suna MedShare ce ta karrama mutanen, kungiyar ta bayar da gudummawar Kayan asibiti na fiye da Dala Miliyan 40 a Nijeriya.

Ya ce, Nijeriya kasa ce data yi fice wajen cudanya da sauran kasashen duniya.

Laro Ya ce,  “Yana mahimmanci mutane su sani cewa ba wai mun zo gaban kungiyar MedShare a matsayin mabarata bane, wannan ba maganar bara bane”

“Lamarin ba kamar muna yawo da hula neman a taimaka mana da kayan aikin asibitocin mu bane, Lallai na haka bane”

“Wannans hulda ne na arziki tsakanin kungiyar MedShare da kungiyoyi daban daban a cikin Nijeriya”

Jakadan na Nijeriya ta kara da cewa, kungiyar MedShare ta dauki huldartayda Nijeriya da mahimmancin gaske haka kuma ofishin jakadancin yana daukan huldan da ke wanduwa tsakanin MedShare da matukar mahimmanci”

Ya kuma Yaba wa wadanda aka karrama saboda daukaka sunan Nijeriya da suke yi, ya ce, samun irin wannan yanayin yana da matukar wahala ta yadda zaka samu dukkan wadanda aka karrama wa suna nan a sa kansu domin karban kyautan nasu.

Daya daga cikin wadanda aka karrama, Misis Bibian Shaku, ta ce, a halin yanzu kungiyarta na shirin shigar da sundukai 2 coke da kayan magunguna da kayayyakin asibiti na fiye da Dala 600,000 zuwa garin Fatakwal da Abuja domin amfanin yan Nijeriya.

Exit mobile version