Abubakar Abba" />

Nijeriya Ba Ta Da Cikakkiyar Ma’adana Kan Yadda Ake Amfani Da Mai —NBS

Daga Abubakar Abba

Koda yake Nijeriyake akan itace kan gaba a cikin nahiyar Afrika wajen fitar da manfetur, sai da abin takaici, itace ta daya a nahiyar wajen shigo da man da aka sarrafa cikin kasar.

A cewar hukumar NBS duk da cewar, itace ke akan gaba wajen shigo da dangin mai da aka sarrafa harda fetur,babu daya daga cikin hukumin gwamnatin dake da cikakken ma’adanar bayanai akan yadda ake yin amfani da man a kullum a kasar nan.

Janar na kididdigar na kasa, Yemi Kale ya shaida wa kafar yada labarai ta Premium Times  cewar, dukkan ma’adanan bayanai da kafafen ‘yada labarai suke bugawa   a yanzu da wanda sauran hukumomin gwamnati suke fitar wa sun tsufa ko kuma ana yi masu kwaskwarima ne kawai.

Mista Kale, wanda ya sanar da hakan a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja ta hanyar mataimakin  Esiri Ojo, ta hanyar wayar tafi da gidan ka, ya ce wadannan ma’ajiyar bayanan  baza a iya dogaro akan su ba wajen samar da tsari ko daukar matakai a hukumance ba.

A cewar sa, “a yanzu mu a (NBS) bamu da cikakkiyar ma’adanar bayanai akan man da ake amfani da shi, amma muna gudanar da bincike da zai samar da cikakken bayanai a fannin.

A cewar sa, duk alkaluman da ku ke ji hukumin gwamnatin tarayya harda kafafen yada labarai suke bugawa kawai shaci fadi ne.

Hukumar ‘yan NBS itace keda alhakkin tara dukkan bayanai da kididdiga akan dukkan ayyukan da suka shafi fannonin tattalin arzikin kasar nan.

Bayanai Masu Cin Karo Da Juna Na Kamfanin Nnpc Dana Hukumar  PPPRA:

Mai magana da yawun kamfanin  (NNPC), Ndu Ughamadu, shima ya tabbatar da wannan maganar, inda ya ce har yanzu kasar nan ba ta da kididdigar ma’adanar bayanai takamai miya akan bayanan man da ake amfani da shi a kasar ba.

A cewar sa, kamfanin  NNPC baida tabbacin kididdigar man da ake amfani da shi a kasar nan.

Ya ci gaba da cewa, kamfanin ya dogara ne kawai akan alkaluman sashen kayyade farashin mai (PPPRA) take samar wa.

Mista Ughamadu ya bayyana hakan ne a hirar da kafar Premium Times ta yi da shi ta hanyar wayar tafi da gidan ka.

A cewar sa hukumar  (PPPRA), itace keda alhakkin kayyade farashin mai a kasar nan, amma har ita kanta kuma alkaluman data ke samarwa suna cin karo da juna.

A 2012, lokacin da  tallafin mai yake daya daga cikin tambarin farashin yin amfani da mai alkaluman sun haura daga kasa da lita miliyan talatin a duk kullum zuwa kimanin lita miliyan sittin.

Alkaluman Kamfanin NNPC da hukumar PPPRA ma’adanan bayanan su suna cin karo da juna akan yadda ake yin amfani da mai, inda hakan ya sanya yan ‘yan kasuwa masu sayar da man suke yin amfani da alkaluman wajen  yin ikirari ga gwamnati akan tallafin na mai don samar da shi.

A ranar bakwai ga watan Fabirarun 2017, karamin da albarkatu Ibe Kachikwu ya shedawa kwamitin dake majalisar wakilai cewar, man da ake amfani da shi a kullum a kasar nan, ya kai yawan lita miliyan  ashirin da takwas.

ministan ya ci gaba da cewa, alkaluman sun sauka daga kimanin lita hamsin zuwa hamsin da biyar a ranar da hukumar hukumar (PPPRA) ta fara yin amfani da biyan tallafi akan mai.

MA’ADANAR BAYANAI TA NBS DA TA NNPC SUNA CIN KARO DA JUNA:

Kididdigar hukumar NBS a yanzu akan yadda ake yin amfani da mai a watan Nuwambar 2016.

A cikin rahoton da hukumar ta wallafa  ta ce, kimanin lita biliyan 12.66 na mai ne ake amfani da shi a kasar nan daga cikin watan Janairu da kuma watan Satumba shekarar.

Yawan kwanukan daga tsakanin daya ga watan Janairun da kuma na ranar talatin ga watan Satumbar 2016 ya kai yawan 273 ko kuma watanni takwas da kwana ashirin da tara.

NBS ta ci gaba da cewa, alkaluman sun kai kimanin lita miliyan 51.87 a kullum.

Amma alkaluman sun haura yadda ake yin amfani da man kamar yadda NNPC ta wallafa a cikin sanarwar akan kididdiga ta shekara a kafar ta ta yanar gizo.

Sanarwar data wallafa ta nuna cewar, kimanin lita biliyan 17.41 ko lita miliyan 47.6 ta mai  ake samar a kullum, aka rabar a 2016.

TAYAR DA JIJIYAR WUYA TSAKANIN NNPC DA SHUGABAN RIKONONIN KAMFANIN:

A lokacin da ake cikin rikici ta kwanan baya, shugaban kamfanin rikonin kamfanin NNPC Maikanti Baru, ta kara janyo rudani akan maganar.

A cikin watan Maris na wannan shekarar a lokacin ganawar da aka yi da Kwamtirola Janar na Kwastam Hameed Ali, Baru ya bayyana cewar, a karkashin maidowa da wasu suke kira tallafi, ya kai yawan tsadar da kamfanin NNPC ya kiyasat da kimanin yadda ake samar da mai naira biliyan N774 na dukkan samar da shi.

Amma Mista  Ughamadu ya warwarewa kafar Premium Times alkaluman da Baru ya bayar cewar basu ne na hakikar abinda aka kashe ba.

Ya ce, anyi kawai kirdado ne akan farashin mai da kuma danyen mai akan wani matsayi na kasuwar mai ta duniya da kuma kudin saukale na mai a kasar nan.

A cewar Ughamadu, sakamakon karin da aka samu na farashin danyen mai a kasuwar mai ta duniya da kuma irin karin da aka samu na shigo da mai, an samu karin farashi mai yawa maban banta tsakanin farashin da aka kayyade na sayar da kuma yadda aka karya farashin a kasashen dake makwabta ka da Nijeriya.

Ya ce, abinda wannan yake bufi shine, farashin da gwamnati ta kayyade na kimanin sayar da mai akan lita naira 145 da kuma bude farshin  da aka yi wanda ya kai naira 171 akan ko wacce lita daya banbancin farashin ya tsaya akan naira ashirin da shida na kowacce litar mai daya.

Ya yi nuni da cewar, a bisa wannan kirdadon da aka yi kimanin lita miliyan talatin da biyar ta mai ake amfani da ita a kullum, inda kuma yawan karbowa ko tallafin mai ya kai kimanin naira biliyan 774 a duk shekara.

A wata ‘yar gajeriyar hira da manema labaran fadar shugaban kasa suka yi da Maikanti Baru    ya ce, a karkashin dawo da naira biliyan 774 a shekara, anyi tane akan kirdadon da aka yi na yawan man da ake amfani da shi a kullum da kuma farashin danyen mai a kasuwar mai ta duniya.

A bisa fasalin da aka yi na alkaluman zasu kai kimanin naira biliyan 64.5 duk wata ko kuma naira biliyan 2.081 a kullum.

Sakamakon ban-bancin farashi tsakanin budaddiyar kasuwa na farashin naira 171 da kuma farashin da aka amincewa ‘yan kasuwa akan naira 145 na kowacce lita daya.

A dogon nazarin da akayi, ya nuna cewar a kalla ana yin amfani da mai lita biliyan talatin a kullum a kasar nan.

Kakakin kamfanin NNPC a kwanan baya ya sanar da cewar, man da ake daukowa daga ma’ajiyar mai  ya ragu da kasa lita miliyan talatin a kullum.

A cikin watan  Agustar 2017 an samar da sama da lita miliyan hamsin na mai.

Ya bayyana cewar, alkaluman daga baya sun karu da kimanin lita miliyan 84.2 a ranar takwas ga watan Dismabar  2017.

Ya ce, yadda farashin danyen ya tashi, haka kudin saukale na mai yake tashi a kasar nan.

A bisa kiyasin da  NNPC ta yi na yin amfani da mai, ya hau da kimanin lita miliyan hamsin da biyar a kullum, inda kuma a karkashin dawo tsadar, shima ya haura da kimanin naira biliyan  993 a shekara.

A kan lita miliyan hamsin a karkashi maidowa ya haura da naira tiriliyab 1.11 na lita miliyan hamsin da biyar a kullum ko zuwa naira tirliyan 1.22 na lita miliyan sittin a kullum ko naira tiliyan 1.33 akan lita miliyan sittin da biyar a kullum ko naira tiriliyan 1.44 akan lita miliyan saba’in a kullum da kuma naira tiriliyan 1.55 a shekara.

BINCIKEN NBS DAKE TAFE:

A kwanan baya Mista  Kachikwu ya sanar da cewar akan tsafar dawo wa ta haura da kimanin naira tiriliyan 1.4 a shekara, inda hakan ya nuna cewar, ma’aikatar mai da albarkantu mai yuwa ta yi kirdado ne akan yawan man da ake amfani da shi, inda NNPC ta kiyasta ya kai yawan lita

miliyan sittin da biyar a kullum.

Sai dai, Ibe daga baya ya janyew wannan furucin da ya yi akan alkaluman, inda ya ce, ma’aikatar tana kan gudanar da aiki da wasu hukumomin gwamnati don samar da cikakken bayanai.

Mista Kachikwu mai yuwa ya yi wannan bayanin ne a bisa binciken da NBS ta fitar na cewar tana kan yin hadaka da ma’aikatar mai da albarkantu da kamfanin NNPC da kuma PPPRA gidauniyar albarkantun mai akan yawan man da ake amfani da shi a kasar nan.

A cewar Mista Ojo, binciken zai hada da yadda ake amfani da man a gida da masana’antu akan tattalin arzikin kasa don samar da bayanai na hakika akan alkaluman man da ake amafani da shi a kasar nan.

Ojo ya ce, a bisa bayana da NBC ta gudanar da bincike akai, zata yi nazari akai don fitar da bayanai na hakika akan man da ake amfani da shi a kasar nan, amma ba wai kawai yin shaci fadi ba.

Ya bayyana cewar, a yanzu haka ana kan gudanar da tarurruka da dama tsakanin NBS da hukumomin aka yi hadaka da su tuni don samar da wani tsari da ake son kammalawa a cikin ‘yan watanni kafin tsakiyar shekara.

 

Exit mobile version