Nijeriya Ba Za Ta Yarda Da Sake Yakin Basasa Ba – Osinbajo

Fasaha

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce Nijeriya ba za ta lamunci sake maimaita wani yakin basasa ba domin ba zai kawo wa kasar alheri ba. Mista Osinbajo ya fadi hakan ne a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, APC, da masu neman takarar gwamnan Anambra, wanda reshen jam’iyyar APC Patriots na jihar ya shirya a Abuja ranar Laraba.

“Abin da ke faruwa a game da irin rikice-rikicen da ya afku a wannan sashen na duniyar kasashe masu tasowa, shi ne cewa galibi yaki ne da ba shi da iyaka.

“Duk wanda yake tunanin zai iya zuwa ya buya a wani wuri, ba zai sami wurin buya ba, a karshen kowa zai wayi gari cikin wahala.

“Ko da ba ku sha wahala ba, iyaye, yara, matasa da tsofaffi da dangi za su sha wahala. Ba za mu iya samun damar yaki a kasar nan ba, ba za mu iya yin hakan ba,” in ji shi.

Mista Osinbajo ya ce dole ne jiga-jigan siyasa su tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen ta hanyar fadar gaskiya da kuma daukar matakan magance halin da dasar ke ciki.

“Ina addu’a cewa kasarmu ba za ta taba sanin rikici ba, amma na san cewa kowane rikici na faruwa ne sakamakon rashin nasarar fadar gaskiya da fada wa al’ummomi gaskiya.

“A karshen ranar, manyan masu fada a ji ne ke yanke hukunci kan abin da ke faruwa a kowace al’umma, kiyaye abin da ka iya haifar da mummunan yanayi,” in ji shi.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce fitattun mutane na iya kawo canji mai yawa ta hanyar kalaman da suke yi. “Idan ba za mu yi magana ba game da rarrabuwar kawuna, kuma muka yi shiru muka kasance karkashin wannan hali na rashin tsaro, to kuwa babu shakka makiya zaman lafiya da wadanda ke son haifar da rashin hadin kai za su samu hanyoyinsu.

“Kuma idan kuwa har hakan ta faru, za mu ga kanmu a guje jama’a- jama’a,” in ji Osinbajo. Don haka, ya bukaci manyan ‘yan siyasa a kasar nan da su yi magana a koyaushe kuma su tsaya domin kare kasar da kuma sauran jama’a.

Mista Osinbajo ya tabbatar wa ‘yan takarar na APC cewa shugabancin jam’iyyar zai tabbatar musu da daidaito a zaben fitar da gwani da za a yi a watan Yuni don tabbatar da cewa dan takarar da ya fi dacewa ya fito a matsayin dan takarar.

Ya kuma umurce su da su yi aiki cikin hadin kai da kuma sadaukar da kai ga jam’iyyar. “Babu wani dan siyasa da zai iya cin zabe shi kadai. Ina kuma son ba ku shawara kan wanda ya ci nasara ya kara himma, ”in ji shi.

Taron shi ne dandalin tattaunawa na farko tsakanin masu neman takarar APC a Anambra, da nufin shirya kasa don nasarar jam’iyyar a Nob. 6 zaben gwamna.

Exit mobile version