Abubakar Abba" />

Nijeriya Ce Ta 13 A kasashen Da Ke Shigo Da Tumatirin Gwangwani

Tumatirin Gwangwani

Duk da cewa a yanzu, yawan Tumatirin da Nijeriya ke noma wa ya kai yawan tan miliyan 2.3 sabanin tan-tan miliyan 1.8 da ake noma a shekaru biyu da suka gabata, har yanzu kasar ita ce ta 13 a fadin duniya da ke shigo da Tumatir din Gwanhwani.

Babban Darakta na Hukumar gudanar da bincike kan ‘ya’yan itatuwa na kasa NIHORT Dakta Abayomi A. Olaniyan ne ya sanar da hakan a taron bayar da horo ga mutane sama da 150 da a ka zabo daga mazabar tarayya ta Ndokwa/Ukwani da ke a jihar Delta.
Taron wanda aka gudanar a yankin Kwale da ke a jihar, an bai wa mutanen ne horon kàn yadda ake shuka Tumarir da kuma shuka ‘ya’yan itaciyar Ugwu, inda ya kara da cewa, bukatar Tumatir da ake da shi a kasar nan a duk shekara, ya kai yawan tan-tan miliyan 3.
Abayomi wanda kuma shi ne Babban Jami’i na kasa na Hukumar NIHORT da ke a garin Ibadan ya ci gaba da cewa, har yanzu Nijeriya ita ce babba ta 14 a wajen noman Tumatir a duniyaz inda kuma ta zamo ta biyu a nahiyar Afrika.
An shirya taron horaswar bisa hadin gwaiwa tsakanin Hukumar da kuma mazabar ta Ndokwa/Ukwani wacce dan majalisar mazabar DakotOssai N. Ossai ke wakiltar alummarsa a majalisar wakilai.
Abayomi wanda wani Darakta a Hukumar Dakta Ephraim Nwanguma ya wakilce shi ya ci gaba da cewa, samar da isassun wuraren adana wa, sarrafa wa, za su tkimaka matuka wajen girbe ingantaccen Tumatir, musamman domin a rage yin asara a yayin gurbinsa.
Don a magance matsalar ya ce, akwai bukatar a sarrafa Tumatir domin rage yin asara yayin da aka girbe shi da kuma dorewa wajen rabar da shi, inda ya bayyana cewa, hakan zai taimaka matuka wajen rage shigo da Tumatir din gwangwani cikin kasar, tare da inganta darajar wanda a ke nomawa a kasar.
Da ya ke yin tsokaci kan ganyen na Ugwu ya ce, ganyensa na da matukar mahimmanci ya na kuma kara habaka tattalin arzikin kasa, inda ya kara da cewa, Irin na Ugwu na kuma dauke da sanadaran amino acid, inda kuma hakan ya sanya wasu nasana’antu su ke yin amfani da shi wajen hada man gyada, inda kuma ya shawarci wadanda su ka samu horon suyi amfanin da horon da su ka samu don ingknta rayuwarsu da kuma samar wa kawunansu kudaden shiga.
Da ya ke yiwa wadanda su ka amfana da horon jawabi, shugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar NIHORT Majo Janar Mohammed Garba mai ritaya ya sanar da cewa, bangarorin biyu za su iya bayar da gudunmawarsu wajen habaka tattakin arzikin kasar nan, inda ya bayyana cewa, horon an yi shi ne da nufin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa da kuma mata domin su ma su zamo masu dogaro da Kansu.
Ya sanar da cewa, tattalin arzikin Nijeriya ya na da karfin da zai iya bunkasa rayuwar yan kasar, samar masu da ayyukan yi, musamman ta hanyar basu horo kan renonon ‘’ya’yan itatuwa, musamman domin kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
dan majalisar mai wakiltar mazabar Ndokwa/Ukwani Dakta Ossai ya jaddada bukatar bai wa matsan horo kan sana’oi da ban da ban, musamman a tannin noma, inda kuma ya yaba wa Hukumar NIHORT kan bayar da horon kan renonon’ya’yan itatuwa.
daya daga cikin wadanda su ka amfana da horon Mista Jude Omenogor ya Nina jin dadinsa kan horon, inda kuma yi alkarin yin amfani da horon don bayar da ta sa gudunmawar a fannin.

Exit mobile version