Abba Ibrahim Wada" />

Nijeriya Ce Ta 33 A Duniya Kuma Ta Uku A Afirka, In Ji Fifa

’Yan Wasan Nijeriya

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya wadda ta kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka a mataki na uku ta zama kasa ta 33 a duniya acikin kasashen da sukafi iya buga kwallo yayinda kuma take ta uku a nahiyar Afirka.

Lashe kyautar zama ta uku da Super Eagles din tayi yasa yanzu ta zama ta uku a nahiyar Afirka kuma ta tsallake kasashe 12 yanzu ta dawo matsayi na 33 a duniya bayan da a watan daya gabata take mataki na 45 a duniya.

Bayan da Nijeriya tayi ta biyu acikin rukunin data samu kanta a kofin na Afirka, rukunin da ya hada da kasar Madagascar da Guinea da kuma kasar Burundi Nijeriya ta kuma doke kasar Kamaru a wasan falan daya sannan kuma ta sake doke kasar Africa ta kudu a wasan kusa dana kusa dana karshe.

Har ila yau, Nijeriya, wadda ta taba lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka sau uku a tarihi ta yi rashin nasara a hannun kasar Algeria a wasan kusa dana karshe sai dai ta doke kasar Tunisia a wasan neman na uku daci 1-0.

Har yanzu dai Nijeriya ce ta uku a Afirka sai kasar Senegal wadda take mataki na biyu sai kuma kasar Tunisa wadda take mataki na farko sai dai kasar Algeriya, wadda ta lashe kofin Africa tana mataki na hudu a Africa sannan kuma ta 40 a duniya sai kuma Morocco wadda take mataki na biyar a Africa sannan kuma ta 41 a duniya.

Kasar Belgium dai har yanzu ita ce ta farko a duniya sai kuma kasar Brazil, wadda ta lashe gasar cin kofin Coppa America a mataki na biyu a duniya sai kuma kasar Faransa wadda ta lashe kofin duniya wadda take mataki na uku a duniya.

Exit mobile version