Nijeriya Da Brazil Sun Ƙulla Yarjejeniyar Horar Da Matasa Kiwon Dabbobi
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Da Brazil Sun Ƙulla Yarjejeniyar Horar Da Matasa Kiwon Dabbobi

byAbubakar Abba
4 months ago
Brazil

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, za ta dora matasa kimanin 37,000, a kan sana’ar kiwon dabbobi; a cikin shirinta na taimaka wa matasa da koya musu kiwon dabbobi, na Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, ya sanar da hakan ne a Abuja, yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga kasar Brazil a karkashin rukunonin kamfanonin JBS S.A.

  • Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya
  • Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

Ministan ya bayyana cewa, hadakar da aka yi da kamfanin kan zuba hannun jari, za ta mayar da hankali ne wajen taimaka wa matasan, musamman wadanda ke da sha’awar harkar kiwon dabbobin.

“A kowa ce jiha, ciki har da babban birnin tarayya da ke fadin kasar nan, za a zabo matasa kimanin 1000, wadanda yawansu zai kama 37000, za a ba su horo tare da kuma samar musu da tallafin kudade; domin fara wannan kiwo, za a kuma a gudanar da shirin ne tare da hadakar gwamnatocin jihohi,” in ji Idi.

A cewar tasa, wadanda za su amafana da shirin, har da mata, kazalika, wasu gwamnatocin jihohin, sun amince da samar da wuraren kiwon, inda gwamnatin tarayya kuma za ta samar da Irin da za a yi amfani da shi wajen shuka.

Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan  258.5.

Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa.

A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu.

Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka bangaren kiwon Kajin gidan gona, duk dai a cikin wannan shiri.

Har ila yau, kamfanin ya sake zabo Jihar Ogun, domin tabbatar da ganin ta amfana da shirin, kazalika; kamfanin na yukurin zuba hannun jari na kimanin dala biliyan 2.5, duba da cewa; jihar ita ce ta kasance kan gaba wajen aiwatar da kiwon Kajin gidan gona a dukkanin fadin Nijeriya. 

Wani mai zuba hannun jari a kamfanin Wesley Batista ne ya tabbatar da hakan, lokacin da wasu jami’an kamfaninsa, suka kai ziyara; wanda John Coumantaros ya jagoranta zuwa wurin Gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun, a fadar gwamnatin jihar, da ke garin Abeokuta.

Batista ya sanar da cewa, Allah ya albarkaci kasar nan da albarkatun kasa da dama, wanda ya sanar da cewa; za su yi amfani da ilimin da suke da shi da kuma kwarewarsu a wannan bangare na kiwon dabbobi, musamman domin samun damar kara habaka tattalin arzikin kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega

2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version