Daga Yusuf Shuaibu
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta rattaba hannu a yarjejeniya da masu zuba jari na kasashen ketare, domin zuba jari hakar zinarin Nijeriya. An bayyana cewa, gwamnatin tarayyar ta rattaba hannu ne da kamfanin bunkasa zinari da ke kasar Egypt, an dai cimma wannan yarjejeniyar ne tare da ma’aikatar ma’adanar da bunkasa karafuna domin zuba jari a bangaren zinarin Nijeriya.
Da yake jawabi a wajen cimma yarjejeniyar, karamin ministan ma’aikatan ma’adanar da bunkasa karafuna, Uchechukwu Ogah ya bayyana cewa, yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin La Mancha na kasar Egypt, kokari ne na babban janyo hankalin masu zuba jari wanda sai bayar da sakamako mai matukar mahimmanci.
Kamfanin Egyptian African Arab Company for Debelopment da ke Cairo a kasar Egypt ne ya shirya wannan yarjejeniya.
Ogah ya ce, “burin mu dai shi ne mu janyo hankalin masu zuba jari na kasashen ketare ta yadda za su zuba kudadensu a bangaren hakar ma’adananmu ta hanyar samarwa da sarrafawa a Nijeriya.”
Shugaban gamayyar kamfanonin La Mancha, Naguib Sawiris, ya bayyana cewa, kundin rattaba yarjejeniyar na kamfanin ya fara aiki ne tun da dadewa a Nijeriya. Ya kara da cewa, La Mancha sun dade suna neman irin wannan damar wanda za su zuba jari a bangaren hakar ma’adanai a fadin Afirka. Ya ce, Nijeriya tana da ishasshen zinari wanda za a zuba jari. Ya ce, kamfanin zai fara gudanar da aiki ne a farkon shekarar 2021.