Nijeriya Da Tunisia: Sakon Osimhen Ga Tawagar Super Eagles

Daga Sulaiman Ibrahim,

Dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen ya yi wa takwarorinsa fatan alheri yayin da suke fara gasar cin kofin Afrika na 2021, AFCON, zagaye na 16 da Tunisia a daren Lahadi.

Osimhen ba a zo da shi Kamaru ba, amma ya aiko da sakon murna da goyon bayansa daga Naples, Italy gabanin wasan Nijeriya na AFCON zagaye na 16 da Tunisia a filin wasa na Roumde Adija.

Dan wasan Napoli ya kasance a cikin jerin ‘yan wasan lokacin da Augustine Eguavoens ya zo, amma dole tasa ya janye shi daga tawagar bayan ya kasa murmurewa daga raunin da yaji a fuska.

Rashin sa babbar cikas ne ga Nijeriya, amma dan wasan mai shekaru 23 ya na da kwarjini ga takwarorinsa kuma ya yi musu fatan alheri a karawarsu da Tunisia.

Ba Osimhen ba ne kadai babban dan wasan da bai samu halarta tawagar Super Eagles a gasar AFCON ta 2021 ba, akwai ’yan kwallo irin su Emmanuel Dennis da Odion Ighalo da kuma Leon Balogun.

Exit mobile version