Daga karshe, shugaban kasa Muhammadu Buhari na cika burin ‘yan gani kasheninsa masu goyon bayansa bil hakki da gaskiya, wadannan da ke goyon bayan tsayayyen shugaba mai yaki da cin hanci da rashawa ba tare da nuna bambanci ba, wanda a shekrara 1984 ya garkame kusan dukkan Shugabanin Nijeriya na wannna lokacin a gidan yari a bisa zargin cin hanci da rashawa, ya kuma yi hakan ne ba tare da nuna bambancin siyasar da suka fito ba ko kuma matsayinsu a gwamnatin tarayya dana jihohi, bai kuma nuna bambanci na addininsu ko kabilan da suka fito ba, haka ya kama su tare da jefa su a gidajen yarin dake a fadin tarayyar kasar nan. Yawancin su sun samu ‘yanci ne bayan da aka yi masa juyin mukin da ya haifar da Janar Babangida a matsayin shugaban kasa a shekarar 1985
Yawancin masu goyon bayan Shugaban Kasa Buhari, musamman wadanda suka zama ‘yan gani kasheninsa tun daga shekarar 2003, suna hankoron samun Shugaban Kasa ne wanda bashi da sani ba sabo wanda zai samar wa al’umma maganin matsalolin da take fuskanta, abin da ya fi ci wa jama’ar tuwo a kwarya shi ne kamarin cin hanci da rashawa da kuma rashin da’a a harkokin yau da kullum na ‘yan Nijeriya. Wadannan wasu matasa ne da suka fusata da halin da ake ciki a Nijeriya, kuma suna da labari irin yadda Janar Buhari ya gudanar da mulkinsa a wancan lokacin na mulkin soja. Suna fusata ne a kan dalilai dake a bayyane, musamman ganin cewa, a na basu labarin yadda harkokin rayuwa suka gudana a cikin tsari a makarantun gwamnati da asibitoci da kuma yadda tattalin arzikin kasar nan ke tafiya kamar dai yadda tattalin arzikin kasar Brazil da India ke tafiya da sauran kasashe masu tasowa makamantasu, irin tattalin arzikin arzikin dake samar da cikakken aikin yi ga ‘yan kasar ta, a wani bangaren kuma sai gashi a Nijeriya a wannnan lokacin da makarantun gwamnati suka zama makarantar da talakawa ne kawai suke tura yaransu haka kuma asibitocin gwamnatin sun zama tamkar wajen ajiye gawarwaki haka kuma tattalin arzikin kasa ya kasa samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya, tattalin arzikin ya ci gaba da haifar da wadanda suka kammala jami’a ba tare da samun aikin yi ba.
Wadannan matasa ‘yan Nijeriya ‘yan gani kashenin Shugaba Buhari, suna nan a miliyoyinsu musamman daga Arewacin kasar nan, suna kuma danganta matsalolin da suka shiga da yadda shugabanin kasar nan na baya suka gudanar da harkokin kasar nan, shugabannin da suka mayar da dukiyar kasa zuwa kayansu na gado, abin lura kuma shi ne yawancin wadannan shugabanin sun fito ne daga yankin Arewacin Nijeriya. Wadanan shugabani ne kuma da suka fito daga tasarin makaratun gwamnati amma kuma a yau yaransu ba sa halartar makarantu a cikin kasar nan. In ma suna karatu a kasa nan to suna zuwa makaratu ne masu zaman kansu wanda ake biyan kudade masu yawa da talaka ba zai iya kai dansa ba. Idan kuma wadannan shugabanin da iyalansu na rashin lafiya, suna tsallakawa ne zuwa kasashen waje don samun magani. Suna kuma amfani ne da kudaden gwamnati wajen zirga zirgan neman maganin a kasashen waje.
Irin wannan lamarin ne ya haifar da al’umma musamman a cikin matasa dake da fatan samun ci gaba da sauyi daga Shugaba Buhari. Dukk da cewa, an yi tir da yanayin da aka yi masa juyin mulki sannan yanayin farin jininsa ya yi matuka raguwa ciki har da yankin arewacin Nijeriya, amma duk da haka Shugaba Buhari ya ci gaba da zama wani madogara na samun ‘yanci da fata musamman daga matasanmu, hakan kuma ya faruwa ne a yankin Arewacin Nijeriya, wannan wani abu ne da za a iya kira tamkar wani abin al’ajabi da alhairin da ba a saba ganinsa ba. Ko shi da kansa Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ba zai iya bayar da cikakken bayani na yadda haka ta samu ba. Lallai kuma wannan wani abu ne da zai ci gaba da zama wani abin al’ajabi na tswon lokaci.
Matsalar dake tattare da irin wannan ga shugaban dake ci a halin yanzu shi ne yuwiwar mayar da lamarin kamar addini ta yadda ko yana samun nasara ko baya samu ido kan rufe, shi kuma shugaban na iya daukar kamar babu wata matsala a tattare da yadda yake gudanar da mulkinsa. In kuma haka ya ci gaba da faruwa, a kwai yiwuwar komawa irin halin da shugabanin da aka yi wa juyin mulki a shekara aka kuma jefa su gidan yari a shekarar 1984. Abin lura kuma anan shi ne, tun daga lokacin da shugaba Buhari ya dare karaga shugancin kasar nan a watan Mayu na shekarar 2015 ake ta samu karin tsoron yiwuwar fadawa irin wannan halin da ake magana a baya. Misali, yadda tafiyar da mulkin ya yi tafiyar hawainiya da kuma takaddamar da aka yi ta samu a kan yadda ya yi wasu nade nade jami’an gwamnatinsa, da kuma yadda ya kasa rufarwa masu cin hancu da rashawa kamar dai yadda ya yi a shekarar 1984 da dai sauransu, hakan ya ci gaba da sanya kokwanto a kan shi ko dai har yanzu shi ne mutumin nan mai tsaurin rai wanda ba shi da sani da sabo a harkar yaki da in hanci rashawa. Ko zai iya biyan bukatun matasanmu na yaki da shugabanin masu cin hanci da rashawa ba tare da sani ko sabo ba kuma ya fuskance su ba tare da tsoro ba, lallai wannna babban lamari ne, kuma hakan ne ya ci gaba da kasance hankoron ‘yan gani kashenin Shugaba Buhari.
Duk da cewa, ana samu wasu ci gaba na a zo a gani a fannin gudanar da gwamnati, kuma hakan bai samu yaduwa a kafafen watsa labarai ba saboda wasu matsaloli da a ake fuskanta a kasar, matsalolin da suka hada dana Boko Haram da ta’addanci da kuma haren-haren Fulani makiyaya a kan ‘yan Nijeriyan da basu ji ba basu gani ba, da yadda yake gudanar da siyasarsa a cikin mafi yawanci shekarun da ya yi yana mulki ya samu yaduwar bayanai ne a kafafen wasta labarai na kashe kashen da suke aukuwa a fadin kasar nan. Abin takaicin kuma shi ne, ya fito ne daga kabilar Fulani, abin da kuma masu sharhi ke amfani wajen zarginsa da hannu a kan harkokin wadannan ‘yan ta’addan gaba daya.
Gashi kuma tsufa ya rutsa da shi tare da rashin cikakken lafiya, abin da ya kai shi zuwa neman magani a kasar Birtaniya a lokutta daban daban, hakan kuma yana nuna mana halin da asibitocin kasar ke ciki, a wasu lokutta kusan dukkan abubuwa sun dagule a gare shi, abin lura kuma shi ne rashin lafiyarsa ya fito da yadda shugabanin ke nuna kwadayinsu da kuma yadda suke rike karagar mulki na ko a mutu ko a yi rai. Bukata da son maye gurbinsa a kan karagar mulki ya kara taso wa, musamman a lokacin da aka yi ta yada jita jitan cewa, rashin lafiyar ta yi tsanani kuma yana iya mutuwa a kowanne lokaci, hakan ya yi matukar tayar da takaddama a cikin jam’iyya mai mulki musamman daga wadanda suke da burin zama shugaban kasa, hakan ya kuma taimaka wajen sauya shekar da aka samu na wasu shugabannin jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP duk da cewa, yawancin wadanan shugabanin dama can daga cikin jam’iyyar PDP suka fito. Hakan kuma ya haifar da ganin akalla hudu daga cikinsu suna takarar neman tikitin takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar PDP.
Lallai babu wani tagomashi ga duk wani mai son takarar neman shugabancin kasar nan daga jam’iyyar APC, musamman ganin irin yadda magoya bayansa suka tsayu ba gudu ba ja da baya, goyon baya irin na gani kashe ni da suke yi wa shugaba Buhari, haka kuma dole a godewa mataimakinsa da ya rike matsayinsa, kuma bai nuna yana hankoron neman shugabanci ba, haka ya kuma taimaka wajen samar da yanayin gudanar da shugabanci a cikin tsanaki. Lallai samuwar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin abin alhairin da ya auku ga Shugaba Buhari. Shugaba Buhari na sa’ar samun mataimakin shugaba tsayayye, marigayyi Janar Tunde Idiagbon ne mataimnakinsa a garonsa na farko na shugabancin kasar nan a shekarar 1984 zuwa 1985 ne, ya kuma tsaya masa yadda ya kamata. Wani kuma abin al’ajabi da alhairin shi ne tashinsa daga doguwar rashin lafiyar da ya yi, a yau Shugaba Buhari yana da cikakken lafiya da karsashi fiye da yadda yake a shekarar 2015, hakan ne ya kuma sa jam’iyyar PDP ke sauwala cewa, wani Jubril ne daga kasar Sudan ya maye gurbin Shugaba Buhari.
Idan aka hada da yadda shugabancinsa ya fara da tafiyar hawainiya da matsalolin da aka samu wajen nade naden jami’an gwamnati da kuma harkokin ‘yan ta’adda da matsalolin da aka samu wajen cikakken sadarwa a tsakanin gwamnati da jama’ar kasa da kuma rashin kafa karfarfar gwamnati da kuma rashin maimata dirar mikiya a kan shuganni masu cin hanci da rashawa kamar yadda ya yi a shekarar 1984 tare da matsalar da ya fuskanta dangane da rashin lafiyarsa, duk da sun kawo karshen shugabancinsa. Da kuma tuni an manta da batun sake neman takararsa a karo na biyu, haka kuma ita kanta jam’iyyar APC, da tuni ya yi kusufi kamar yadda jam’iyyar PDP ta yi. Amma kuma daga dukkan alamu cikin abin alhairin da ya auku ga Shugaba Buhari shi ne, ita kanta jam’iyyar APC, wasu matsaloli da wasu shugabaninmu ke jefa kansu da kuma ana iya kauce musu yana da wahalar a iya yin cikakken bayaninsu, hakan kuma ya sabawa duk wani nazari na masana ilimin kimiyyar siyasa, misali dole a samu a kundin tarihi na cewa, jam’iyyar APC ce kada a fadin duniyar nan da ta kasa kiran babban taron jam’iyyar a dukkan matakan shugabanci tun bayan da ta lashe zabe a shekarar 2015.
Ga mu a Nijeriya a karkashi jagorancin Shugaba Buhari wanda aka cire rai a kansa a fannoni da dama, jam’iyyun adawa karkashin jagorancin jam’iyyar PDP ta ci gaba da bata masa suna ta kowanne fanni, amma duk da haka sai kara karfi yake yi. Muna iya shiga gardama a kan cewa, ba a iya maimata abin da ya fara shekarar 1984 ba a kan jami’an gwamnati masu cin hanci da rashawa, amma lallai ya samu nasarar karkatar da kudaden gwamnati zuwa gudanar da ayyukan ci gaba a fadin tarayya kasar nan. Cikin shaidun ayyukan da ya gudanar sun hada da, manyan ayyukan hanyoyi da layin jirgi da ya keta sassan fadin tarayyar kasar nan, haka kuma ba a taba samu
ba a tarihin kasar nan na baya bayan na bunkasar da aka samu a fannin samar da wutan lantarki, a karon farko a tarihin kasar nan umna maganar samar da Migawat 7,000, a shekarun baya bamu taba wuce Migawat 3,000 ba, ga kuma kyakyawan ci gaba da ake samu a gina gadan da ta ratsa kogin Neja, duk suna cikin alkawurran zabe da aka yi a baya, ga kuma taimako na kai tsaye don bunkasa tattalin arzikin gwamnatocin jihohin Nijeriya.
A kwai manya manyan nasarorin da aka samu a kasar nan, amma nazarinmu a nan shi ne cewa, duk an samu wadanna nasarorin ne sakamakon alhairin dake tattare da Buhari da kansa, in muka daukin yanayin abin da ya faru a shekarar 1984 da kuma tsananin rashin kudin shiga da aka fuskanta. Ta yaya aka samu irin wannan gaggarumin nasarorin? musamman ganin dan kadan din kudaden shiga da aka samu, tare da kuma yin nazari akan yadda ake gudanar da yaki da cin hanci rashawa, watakila babban abin da ya haifar da wannna nasarar shi ne tsayuwa da kuma jajircewar Shugaba Buhari da kansa. Yawancin abubuwan da ‘yan siyasar Nijeriya za su bayyana rashin yiwuwarsa musamman idan abin ya hada da sarrafa kudaden jama’a, sai gashi wannan mutumin ya gudanarwa ba tare da wani wahala ba. Hakan kuma yana kara tuna mana da dalilin da Janar Babangida ya bayar a matsayin abin da suka sa aka yi masa juyin mulki a shekarar 185, wanda wai shi (Buhari) mutum ne mai tsayuwa ba tare da gudu ba a kan abin da ya yi imani da shi na ci gaba al’umma.
Tsayuwa tare da dakewa sune sirrin samun nasara a dukkan harkokin shugabanci. Duk wani shugaban da ake juyawa ba ya samun nasarar jagorancin al’ummarsa. Ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda daga dukkan abin da ya bayyana, tun lokacin da ya karbi mulki a watan Mayu na Shekarar 2015 yana kara tabbatar da zargin da Janar Babangida ya yi masa ne na kasancewa mutum mai tsatsauran ra’ayi, sai kuma gashi yana ta samun gaggarumin nasarori a harkar shugabancinsa. Hakan zai iya sa mutum ya dauka cewa, in aka hada nasarorin da Janar Babangida ya samu a zamanin mulkinsa da kuma irin dakewa da tsayuwar Shugaba Buhari a mulkinsa da kuma yadda ya yi yaki da jami’an gwamnati masu cin hanci da rashawa, hakan na nuna mana ma’anar tsatsaurar matakin da Janar Babangida ke nufi ke nan. In za a kwatanta shi da shugabanin da suka wuce a baya abin da za a iya zarginsa da shi kawai shi ne, fitarsa kasar Birtaniya neman magani da kuma rahoton cewa, yaransa na karatu ne a kasashen waje, bayan wannan kuma sai zargin cewa, wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa na fuskantar zargin cin hanci da rashawa tatare da su.
In har dai zamu yi adalci, dole mu yarda da cewa, Sakataren Gwamnati da shugaban hukumar leken asirin kasa (DSS) da wasu shugabannin bangaren rundunar tsaro duk sun rasa ayyukansu a bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi musu, shi kuwa Alkalin Alkalan Nijeriya da kansa ya amince da aikata wasu nau’in hadin baki da rashin gaskiya amma sai gashi wasu ‘yan siyasa daga bangaren adawa suna goya masa baya. Ana ta kokarin kawo hujjojin tsarin mulki da na shari’a don a kare gurfanar da shi a a gaba shari’a. Wasu kuma na gabatar da hujjar cewa, wai tun da ana dab da gudanar da zabe bai kamata a gurfanar da shi ba, wasu kuma na gabatar da hujjar gaggawar da aka yi na bincikarsa duk dai don a kange shi daga fuskantar shari’a.
Har ana neman cire rai a kan yadda za a fuskanci takaddamar sai kawai Shugaban Kasa Buhari ya dauki matakin bazata a kai, Shugaba Buhari ya yi amfani da umurni ne daga kotun da’ar ma’aikata inda ya dakatar da Alkalin Alkalan tare da nada mukaddashin Alkalin Alkalai na kasa nan take. Hakan ya tayar da jijiyar wuya daga lauyouyi da kungiyoyin rajin kare hakkin bil adam, haka kuma rahotanni na cewa, shugabanin majalisar dokoki wadanda suka mayar da kansu kamar wani reshe na kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar PDP sun shirya dawo wa daga hutu don tattauna lamarin dakatarwa da aka yi wa Alkalin alkalan.
Abin lura a ana shi ne, Shugaba Buhari ne kadai a tarihin kasar nan zai iya dakatar da Alkalin Alkalan Nijeriya a na gab da yin zaben da shi da kansa yake takara. Lallai Shugaba Buhari ne kadai shugaba a tarihin kasashe irin Nijeriya da ba ya jin wani barazana ko tunanin yiwuwar ba za a sake zabansa ba. Wannan abu ne mai yiwuwa in dai ba a taba abin da ya yi imani da shi ba, kuma lallai wannan ne irin shugaban da matasanmu na Nijeriya ke hankoro da bukata.
Duk mai adawa na gasikya dole ya yarda da cewa, Shugaba Buhari mutum ne ba ba a abin da ya damesa, amma a bin takaici a nan shi ne, sai gashi mutanen da ake tunanin masana ne, masu ilimi sun yi gagngami a kan gwamnatin da take gudanar da harkokin ta a bayyanane ba tare da boye boye ba, duk da sunan wai cika doka da oda da kuma bukatar ba dukkan bangarorin mulki hakkokinsu, wasu manyan lauyoyin kasar nan ‘SAN’ dake da zarge zarge da dama a kan Alkalin Alkalan, a yau sun zama masu kare shi, haka kuma shugaban kungiyar lauyoyi na Nijerya wanda a halin yanzu yana fuskantar shari’a a gaban kotun da’ar ma’aikata a kan cin hanci da rashawa, a yau kuma yana tattara lauyoyi don kare Alkali Alkalan Nijeriya, haka kuma wasu sashen kungiyoyin fararen hula da harkokinsu ya yi kamari a kan yadda suke shiga harkokin siyasa, wai sai gasu yau sun fito suna goyon bayan Alkalin alkalan da ya amince da aikata cin hanci da rashawa da kansa.
Abin na da ban takaici yadda muke kwakulo ayoyin doka da nufin halasta aikata miyagun aiki. A hakan wai muke son bunkasar kasar mu a haka muke son shiga rukunin kasashen da suka ci gaba tare da karfafa tsarin dimokradiyyar mu, ta yaya za mu cimma wannan matsayi tare da yin zagon kasa ga shugabanmu, lallai babu kokwanto cewa, dukan al’umma na samun shugaban da ya cancancesu ne, kuma lallai shugabancin Buhari wani baiwa ne garemu don mu kasance a matsayin hadaiyyar kasa a inuwa daya. Lallai muna bukatar tafiyar da mulkin da za a hada da tsatsaurar matakai da kuma halin ba ruwanmu wanda zai dauki mataki ba tare da maduwa da duk abin da zai biyo baya ba.
Duk da cewa, ba duba nake yi ba, amma na san cewa, kurar da lamarin dakatar da Alkali Alkalan Nijeriya ya haifar zai lafa da zaran an shiga harkokin zabe, wanda muke gab da shiga nan na mako uku masu zuwa. Nasarar Shugaba Muhammadu Buhari zai kawo karshen lamarin, za a sha mamaki musamman yadda mutane ke tunani da kokwanton nasarar Shugaba Buhari. Ina kuma tunanin yawancin shugabanin da suka samu nasara ba a daukar su da mahimmanci a kan dauka kamar ba za su iya kai labari ba. Amma wani abin dake a bayyane a kan lamarin Shugaba Buhari shi ne, babu wanda ya iya yin hasashen yadda yake gudanar da mulkinsa ciki kuwa har da matarsa.
Rashin iya hasashen yanayin mulkinsa da kuma irin gagarumin nasarorin da ya samu da kuma takaicin da wasu suka shiga sakamakon haka, duk sun hadu sun yamutsa mutane ,hakan ya sa muna da tabbacin sake haifar da karin ire iren Buba Galadima masu yawa.
A kwai yiwuwa kara sabbin jinni a cikin gwamnati za kuma a samu karin kaimi a yaki da cinhanci da rashawa a lokutta masu zuwa. Shari’a Alkalin alkalan Nijeriya na zama kamar wani makulin rufe shekaru hudu na farkon mulkin Shugaba Buhari, mayar da hankali a kan masu shari’a zai zama wani fage na sauya fasalin bangaren shari’a da ‘yan sanda da kuma dawo da mutumcin al’umma gaba daya.
Idan kuma aka hada da ci gaba da aka samu a bangaren samar da hanyoyi da bangaren jirgin kasa da dawo da darajar makarantun gwamnati da filayen jiragen sama da farfado da asibitocin mu da sauran ayyuka, haka kuma da kokarin hada tafiyar ci gaban tsarin dimokradiyyarmu da samar da cikakken ci gaba a dukkan bangarorin rayuwar jama’ar Nijeriya, duk za su kara bayyana a karshen shekara hudu na mulkin Shugaba Buhari masu zuwa a karo na biyu, wadannan ci gaban za su kara bayyana mana cewa, lallai Buhari alhairi ne ga Nijeriya.
Da zaran an samu haka, Shugaba Buhari zai zama uba ga tsarin dimokradiyyarmu. Za a iya ba tsohon Shugaban kasa Obasanjo wanna matsayin amma ya riga ya watsar da daman da ya samu na zama haka, musamman kokarin da ya yi na neman shugabancin kasar nan a karo na uku. Ba za a kuma iya sanin halin da zai shiga ba in har Shugaba Buhari ya kara fadada yakinsa na cin hanci da rashawa. lallai wanan na daga cikin dalilan sake hadewar da tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda ya yi fiye da shekara 16 yana sukansa.
Hadin kan da aka samu a tsakanin tsohon Shugaban Kasa Obasanjo da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku na daya daga cikin abin takaicin da suke faruwa a kasar nan, mutum zai yi mamakin yadda za a hada bin doka da oda da aikata manyan laifuffaka da kuma ayyukan kungiyoyin kare hakkin bil adama na Nijeriya, wadanda suka yi gangami a kan ci gaban kasarmu Nijeriya. Dole sai an samu irin tsayuwar daka na Shugaba Buhari da halin ba ruwanmu kafin a samu irin ci gaban da muka samu, lallai Buhari alhairi ne ga Nijeriya, a karkashin mulkinsa ne kawai muke iya samun wannan nasarar da muke tsananin bukata a hankoronmu na neman kai kasar nan tudun muntsira.
Tabbas tafiyar ba zai taba zama da sauki ba, za a samu gangami daban daban na masu aikata laifufuffuka, za su hada kai ta fannoini da dama don kawo wa shekaru hudu na mulkin Shugaba Buhari masu zuwa cikas, sai dai ina da yakinin cewa, daga karshe ‘yan Nijeriya za su yi farin cikin samuwar gwamnatin Shugaba Buhari a dukkan fannonin rayuwa. ‘Yan Nijeriya da dama za su ci gaba da yin korafi da kuma yin tir da gwamnatisa, kungiyoyi kuma za su ci gaba da yaki da zaben sa a karo na biyu, amma kamar yadda ya faru a shekarar 1984, wanda haka ya haifar da ‘yan gani kashenin Buhari a shekarar 2003, hakan kuma shekaru hudu na mulkinsa masu zuwa zai haifar da rukumin ‘yan Nijeriya ne da za su dauke shi a matsayin uban kasa. Tabbas irin wannna shugabanci ne muke fuskanta a halin yanzu. Shekarar 2023 zai bayar da bayanin alhairin da muka samu na shugaba Buhari, tsayayyayen shugaba da zai shiga kundin tarihin kasar nan.
– Lukman, ya rubuto ne daga Dandamalin ‘Progressibe Gobernors Forum’ Abuja. Za kuma a iya tuntubarsa a smlukman@gmail.com