Daga Abubakar Abba, Kaduna
Mataimakin Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Bala Ibn Na’Allah ya koka akan irin yanayin da ake dashi a kasar nan ta harkar zirga-zirgar jiragen sama.
Na’Allah wanda shine Mataimakin Shugaban Kwamiti na Majalisar Dattawa a harkar sufurin jiragen Sama.
Ya ce, “a ilmance, abin da nake nufi shine, mu ke da yanayi mafi rudarwa a duniya wajen gudanar da sufurin jiragen sama kuma harkar ba za ta iya ci gaba karkashin wannan yanayi.”
Na’Allah mai wakiltar al’ummar mazabarsa ta Kebbi ta Kudu daga Jihar Kebbi ya yi koken ne lokacin da ’ya’yan kungiyar dalibai masu koyon tukin jirgin sama da injiniyoyi suka ziyarce shi a ofishinsa dake Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cewar shi, wadanda suka zuba jari a harkar, da kyar suke samun riba, domin wani lokaci, ribar tana tafiya ne akan masu ruwa da tsaki, kamar matuki da kamfanin Inshora da Injiniyoyi da sauran ma’aikata da kuma masu sa ido akan tafiyar da harkar.
Sanata Na’Allah ya ci gaba da cewa, hukumomi masu sa ido akan harkar, sun dage sai lallai wadanda suka zuba jari a harkar sun biya da Dalar Amurka, alhali yawancinsu, basu da kudaden biyan.
Ya yi nuni da cewa, idan aka ci gaba da tafiya a hakan, harkar ta sufurin jiragen sama, ba za ta taba ci gaba ba a yanzu a kasar nan.
Ya bayyana cewa, masu sa ido a harkar sun zama wani karfen kafa,don sun ga sune keda wuka da nama akan lura da harkar.
Ya ce, bai kamata ba a rinka tsawwalawa masu yin harkar ta hanyar cazar su makudan Dalar Amurka.
Na’Allah ya bayyana cewa,Nijeriya tana daya daga cikin ‘ya’ya ta kungiyar Sufurin jiragen sama ta kasa da kasa(ICAO), wadda ta baiwa matuka jirgin sama damar da suyi amfani da damar taron na garin Cape, wajen bayar da hayar jirage da tashin su.
A cewar shi, wannan yarjejenyar, a karkashin dokar Nijeriya, an amince da ita, kuma za ta taimakawa matukan jiragen.
Sai dai, Sanata Na’Allah ya ce, abin takaici, masu sa ido akan harkar, sun ja da hakan a bisa cewar za ta kashe durkusar da masu jirage na cikin gida kasa.
Ya ce, a saboda hakan wadanda suka bada hayar jiragen su a karkashin yarjejeniyar ta garin Cape, tasa su dole suka dawo da jiragen su gida.
A karshe Sanatan ya koka akan yadda ganin mafi yawanci dalibai matuka jiragen sama da aka yaye a kasar nan wadanda basu samu aikn yi ba.