Nijeriya Na Amfani Da Tan Miliyan 2 Na Naman Kaji Duk Shekara – Farfesa Eustace    

Naman Kaji

Daga Abubakar Abba,

Farfesa Eustace Iyayi, Babban Jami’in Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Kasa (NIAS) ya bayyana cewa, Nijeriya na amfani da kimanin tan miliyan 2 na naman kaji a kowace shekara.

A cewar Farfesa Eustace, har ila yau, kashi 70 a cikin dari na wannan adadi an shigo da su cikin kasar ne kafin rufe iyakar.

Babban Jami’in Cibiyar ya ci gaba da cewa, sama da tan miliyan daya na kaji ne aka hana shigowa da su cikin kasar nan, inda aka fassara su zuwa ayyuka kusan 100,000 da kuma talotalo, yayin da aka ajiye kimanin Naira biliyan 50 a bangaren kiwon kaji.

Bugu da kari,a cewar kungiyar ‘yan kaji ta kasa (PAN), rufe iyakar ya rage rage fasa kaurin da ake shigowa da shi cikin kasar nan, tare da adana wa sana’ar kaji kimanin Naira biliyan 50.

Farfesa Eustace ya kara da cewa, kungiyar ta  PAN tana kan gudanar da  ayyukan samar da kayayyaki a cikin masana’antar dillalan nama inda ya karu zuwa kashi 70 a cikin dari daga yin amfani da kimanin kashi 45 a cikin dari sabanin a baya saboda rufe iyakokin kan tudu na kasar nan.

Ya ce bangaren kiwon kaji shi ne bangaren kasuwanci mafi tsoka a bangaren noma wanda ya kai jarin kimanin Naira tiriliyan 1.6.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya da babban banikin Nijeriya  CBN na iya kokarinsu don bunkasa bangaren ta hanyar bayar da tallafi don shigo da kayan masarufi, musamman masara, wacce ta kunshi kusan kashi 70 a cikin dari  na abincin kaji.

Ya yi nuni da cewa, ya  kamata a ba manoman kaji tallafi domin harkokinsu na kiwon kajin, inda ya sanar da cewa, dole ne a samu abin farawa ga duk wata harkar kaji.

Ya kara da cewa, ya kamata a sanya kwai a cikin shirin ciyar da makarantu sannan a biya manoman kaji a lokutan da suka fuskanci wata wahala.

A wani labarin kuwa, Gwamnatin jihar Adamawa ta ce ta sayo takin zamani tan 5,000 domin rabawa ga manoman jihar, ta yadda za a kara samar da amfanin gona.

Dokta Dishi Khobe, shi ne kwamishinan aikin gona na jihar, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya a Yola.

Khobe ya bayyana cewa gwamnati za ta sayar da takin kan farashi Naaira 5,000 a kowane buhu, domin tallafa wa manoma masu karamin karfi dama kara karfafa masu guiwa kan harkar noma domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Exit mobile version