Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi

byAbubakar Abba
3 weeks ago
Nijeriya

An ƙiyasata cewa, Nijeriya na yin asarar kimanin dala biliyan 10.5, na samun kuɗaɗen shiga daga fitar da kashin dabbobi zuwa kasuwannin duniya, musamman saboda rashin samar da kyakkyawan tsari na ƙasa da kuma kayan aiki.

‘Nagar kimiyya ta Science Direct’ ta bayyana cewa; kashin dabbobi na ɗauke da wasu sinadarai kamar na ‘nitrogen, phosphorus da kuma na potassium’.

Kazalika, ƙungiyar ‘Trendset Ɓisionaries’ ta ayyana matsayin kashin dabbobin, wanda ya kai dala biliyan 10.5; har ila yau kuma ta ƙara da cewa; zai iya zarcewa zuwa dala biliyan 18.3 a shekarar 2030.

Sai dai, an bar Nijeriya a baya wajen kai kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, musamman duba da cewa; ƙasashe a nahiyar Asiya da tarayyar Turai da Ƙasar Amurka, tuni suka yi nisa, wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani da sauransu.

  • Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma 
  • Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

Haka nan, Ƙasar China a faɗin duniya, ita ce kan gaba wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani, inda rahotanni suka bayyana cewa; ƙasar ta China na samar da aƙalla a duk shekara  tan biliyan 3.8 na takin zamani da ta samar daga Kashin dabbobi da kuma na kashin kaji.

Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar.

“Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa.

“Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani, domin ƙara inganta ƙasar yin noma da kuma amfanin gonar da aka shuka,” in ji Chuka.

Mordi ya ci gaba da cewa, rashin cin gajiyar da ba a yi  na kashin dabbobin a ƙasar nan, hakan na ci gaba da haifar da giɓi ga fannin.

“Akwai buƙatar sassan koyar da darussan aikin noma da ke jami’oin ƙasar nan, su sanya darasin koyar da muhimmancin yin amfani da kashin dabbobin a cikin manhajarsu, domin a bunƙasa fannnin”, a cewar Mordi.  Kazalika, ya yi kira ga gwamnati da ta samar da wasu shirye-shirye, musamman domin a ilimantar da manya da ƙananan manoma da kuma ƴ an kasuwa, kan albarkar da ke tattare da kashin na dabbobin.

“Ga ƙasa kamar irin Nijeriya da ke ƙoƙarin ganin ta rage yin dogaro daga fannin man fetur, idan ta mayar da hankali, za ta iya amfana da wannan fannin,” Inji Mordi.

Bugu da ƙari bisa wasu alƙaluma da hukumar kula da ƙididdiga ta ƙasa wato NBS ta fitar sun bayyana cewa, a  Afirka ta Yamma, Nijeriya ce, kan gaba da ke da Shanu masu ɗimbin yawa, inda a ƙasar ake kiwata Shanun da yawansu ya kai miliyan 20.79.

Kazalika, ƙasar na da sauran dabbobi dasuka haɗa da, Tumaki da Akuyoyi da sauarsu.

Sai dai, duk irin waɗannan ɗimbin dabbobin da ƙasar ke da su, da kuma kasancewar ƙasar kan gaba wajen albarkatun dabbobi a Afirka ta Yamma, amma mahukuntan ƙasar, sun gaza samar da wani kyakaywan tsari na cin gajiyar da ke tattare da Kashin na dabbobin.

Albarkatun da ke cikin ƙashin dabbobi da Jininsu da kuma kashin nasu, za a iya juwa su zuwa wasu sinadarai da dama.

A cewar hukumar NBS, a kullum a  Jihar Legas kaɗai, ana yanka Shanu da yawansu ya kai daga 3,000 zuwa  5,000.

Wannan adadin, ba su daga cikin dubban da aka  yankawa, ba tare da yarjewar mahukunatan jihar ba, amma duk da hakan, ba a cin gajiyar alfanun da ke tattare da Kashin na dabbobin.

Sunny Omokaro,  shugaban ƙungiyar ma’aikatan mahauta na ƙasa, ya sanar da cewa, wannnan rashin ci gajiyar ta Kashin dabbobin, ya sanya Nijeriya rashin samun damarmaki masu yawa.

“Sarrafa kashin dabbobin, zai taimaka wajen ƙara samar da ayyukan yi da samar da kuɗaɗen shiga“ Sunny ya shaida wa jaridar BusinessDay hakan.

Ya buga misali da ƙashin dabbobin, wanda ya ce; za a iya sarrafa shi zuwa abincin dabbobin da sauransu.

Ya sanar da cewa, rashin samar da kayan aikin sarrafa kashin dabbobin zuwa wasu nau’ika, na ƙara haifar wa fannin wani sabon ƙalubale.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Sabon Kakin Ƴansanda Ya Ziyarci Cibiyar Ƙungiyar Ƴan Jarida A FCT

Sabon Kakin Ƴansanda Ya Ziyarci Cibiyar Ƙungiyar Ƴan Jarida A FCT

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version