Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Nijeriya Na Bukatar Biliyan N289.86 Wajen Samar Wa Mutane 6,456,275 Mitar Lantarki

Published

on

Bincike ya nuna cewa, Nijeriya tana bukatar naira biliyan 289.86 wajen samar wa mutane guda 6,456,275 mitar wutar lantarki a fadin kasar gaba daya. Wannan bincike ya zo ne sakamakon bayanin da masu ruwa da tsaki a cikin kamfanonin wutar lantarki suka gudanar, inda suka bayyana cewa, akwai bukatar hadin kai a tsakanin kamfanonin wajen amincewa da kayayyakin aikin da ake gudanar wa a bangaren wutar lantarki domin a cimma burika. Saban adadin masu amfani da wutar lantarki wadanda ba su da mita, an same shi ne a binceken da kamfanin da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC), wanda ya nuna cewa, mutane 6,456,275 masu amfani da wutar lantarki ba su da mita.

Tun da farkon wannan wata, majiyarmu ta bayar da rahoton cewa, masu amfani da wutar lantarki za su fuskanci karin kudin mita sakamakon karin da hukumar NERC ta yi na farashin mita. Hukumar ta kara farashin mita mai layuka guda uku ne daga naira 67,055.85 zuwa naira 82,855.19, yayin da ta kara farashin mita mai layi daya daga naira 36,991.50 zuwa N44,896.17. Sakamakon karin farashin mitan, bincike ya nuna cewa, idan aka bukatar samar wa mutane guda 6,456,275 mita mai layi uku a fadin kasar nan, to sai an kashi naira biliyan 534.93.

Haka kuma, idan ana bukatar samar wa wadannan mutane mita mai layi daya, to sai an kashe kudaden da suka kai naira biliyan 289.86, kafin a iya samar wa wadannan mutane mita a fadin kasar nan. Wannan ya nuna cewa, ana bukatar kudi har naira biliyan 289.86, kafin a samar wa wadanda ba su mita.

Hukumar da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya ta samar da wani sabon tsari a bangaren wutar lantarki na amfani da mita, wanda za ta yi aiki kafada da kafada da kamfanoni masu rarraba wutar lantarki domin samar da mita ga mutanen da ba su da shi. Wannan bai zo da mamaki ba, ganin yadda kamfanoni masu rarraba wutar lantarki suka bukaci masu gudanarwa a bangaren wutar lantarki da su hada kansu wajen magance matsalolin kayayyakin aiki wanda ke bayar da tazara a cikin kasuwancin.

Hukumar NERC ta ce, “tazarar da ke tsakanin masu mita da marasa mita babban matsala ce a wannan fannin.

“Rahoton hukumar ya nuna cewa, ta gudanar da rajistar masu amfani da wutar lantarki guda 10,374,597, amma guda 3,918,322 kacal masu mita a karshen watanni hudu na shekarar 2019.”

Ta ce, sama da kashi 62 na wadanda ta yi wa rijista masu amfani da wutar lantarki, har yanzu akwai wadanda ake bin su bashin kudin wutar lantarki. Ta kara da cewa, samar wa dukkan wadanda aka yi wa rijista masu amfani da wutar lantarki mita, yana da matukar mahimmanci wajen samun kudaden shiga a bangaren wutar lantarki.

Shugaban sashen bincike na kungiyar kamfanoni masu rarraba wutar lantarki a Nijeriya, Sunday Oduntan, ya bayyana cewa, idan ana so a cimma tsarin da aka yi a kan inganta kayayyakin aiki a wannan fanni, to dole sai an samu hadin kai masu gudanarwa a cikin wannan fanni. Ya bayyana cewa, rashin hadin kai a tsakanin masu gudanarwa yana matukar kawo tarnaki a cikin wannan harka na rarraba wutar lantarki.

Haka shi ma, shugaban lauyoyi na bangaren wutar lantarki a Nijeriya, Uket Obonga, ya bayyana cewa, dole sai kamfanonin wutar lantarki sun samar wa mutane mita, idan ana bukatar a rage tazara tsakanin masu mita da kuma wadanda ba su da shi a Nijeriya. Obonga ya kara da cewa, wadanda ba su da mita a Nijeriya sun linka wadanda suke amfani da mita a bangaren wutar lantarki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: