Umar A Hunkuyi" />

Nijeriya Na Bukatar Guraben Aiki Miliyan 20 Duk Shekara – IFC

Hukumar kudi ta, International Finance Corporation, wacce wata reshe ce na bankin Duniya, ta ce, kasashen Afrika suna bukatar samar da sabbin ayyukan yi milyan 20.4 a kowace shekara.
“Afrika tana bukatar samar da sabbin ayyuka a kowane wata. Don haka muna da bukatar samar da shugabannin da suka san abin da ya kamata da sabbin kasuwanni,” kamar yanda aka jiwo a cikin wata sanarwa da ta fito daga Kungiyar shugabannin manyan kamfanoni ta Afrika, a Kigali, ta Rwanda.
Shugaban kungiyar shugabannin kamfanonin na Afrikam Amir Ahmed, ya yi kira ga gwamnatoci da su bar kamfanoni masu zaman kansu da su taka rawar da za su iya takawa wajen samar da ingantattun ayyuka da Afrika ke bukata domin bunkasa da ci gaban ta.
“Ya zama tilas a tafi tare da Kamfanoni masu zaman kansu da kuma masu zuba jari. Domin ba yanda za a sami ci gaba ba tare da su ba,” in ji Yahmed.
A cewar sanarwar, a lokacin da ya kasance huldan cinikayya a tsakankanin kasashen na Afrika tana da rauni sosai, manyan jagororin ‘yan kasuwa na nahiyar ta Afrika sun yi taro domin tattaunawa a kan mahimman abubuwa da suke addaban harkar ta kasuwanci domin nemo hanyar magance su, don ganin bunkasan tattalin arzikin nahiyar.
A na shi jawabin na bude taron, shugaban kasan na Rwanda, Paul Kagame, an jiwo shi yana cewa, “Ba wanda ke tambayar ko tsarin tafiyar da kasuwanci na nahiyar ta Afrika, shi ne daidai, ko kuma yana da alfanu ga nahiyar tamu. Amma dai ya zama tilas mu tabbatar da cewa shirin yana aiki sosai, mun kuma san yanda za a yi hakan.
Manyan shugabannin siyasa da na ‘yan kasuwa an ce duk sun tattauna a kan kalubalen da suke da dangantaka da kasuwanci a tsakankanin kasashen na Afrika a lokacin taron.
Shugaban kasar Habasha, Sahle-Work Zewde, cewa ya yi, “Matukar mun fi mayar da hankalinmu ne a kan abubuwan da suka shafi siyasa, a nahiyarmu, duk muna da manufa guda ne, na ganin mun ciyar da kasashen mu gaba yanda ya kamata, amma hakan ba zai taba samuwa ba, ba tare da tsaro da zaman lafiya.

Exit mobile version