Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewar mutane masu kyakkyawan hali da ingantacciyar akida ne ya kamata su zama shugabanni a dukkan matakai dan samun cigaban kasar nan.
Gwamnan hakan ne a lokacin da yake bude shirin horar da matasa na kwanaki uku wanda hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin Neja da kungiyar (LGI) Lead Gobernment Initiatibe a babban dakin taro na Idris Legbo Kutigi da ke minna.
“Shugabanci mai inganci, rikon amana kuma dabi’un wadanda muke zaba shi ke tafiyar da kasar nan,” a cewarshi.
Ya ce, kafin kasar nan a samu canjin da ake tsammani, akwai bukatar mutane su shiga harkokin siyasa, saboda ba wanda zai iya gyaran kasar nan shi kadai.
Gwamnan ya ce, kawo karshen rashawa a dukkanin bangarorin kasar nan, wanda dole mu fuskance shi, idan muka samu mutane masu kyakkyawar halaye za a iya samun tsarin siyasa mai inganci.
“Ya kamata mu yi aiki a matsayin na ‘yan adam da kyakkyawar dabi’a, ya kamata mu zama masu kyautatawa juna.
Gwamnan wanda ya halarci rantsar da shugabannin LGI, ya ce shi ne na farko yayi hadin guiwa da kungiyar saboda kyakkyawar manufar kungiyar na wayar da kan matasa akan tsarin shugabanci.
Ya bayyana farin cikinsa kan sanya matasa a tsarin horarwa ga matasan jihar, ya nemi matasan da su yi anfani da wannan damar wajen shiga harkokin siyasa da gwamnatocin kasar nan.
Gwamnan ya nuna damuwarsa akan karancin mata a siyasa a jihar, ya nemi da mata su rungumi siyasa dan cigaban tsarin mulkin dimukuradiyya.
Shugaban kwamitin amintattun kungiyar ta LGI, Mista Shina Peter ya ce tawagar ta taho jihar ne dan horar tsarin shugabanci, dubarun isar da sakwanni, wayar da kan jama’a a siyasan ce, gudunmawar dan kasa wajen cigabanta.
Mista Peller wanda dan majalisar wakilai ne mai wakiltar Iseyin/Itesiwaju/Kajola da Iwajowa daga jihar Oyo, ya bayyana cewar tawagar tana wayar da kai ne akan cigaban yakunan al’umma, da horar da wadanda ya kamata a horar, dan samar da cigaban al’ummomin karkata.
Ya ce sun zabo mutane biyu daga kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar dan su halarci horarwar wanda zuwa yanzu sun sake karbar mutane hamsin da gwamnatin jiha ta zabo za a horar da su a matsayin masu sanya ido wanda ya bada jimlar adadin mutane dari.
Ya jawo hankalin matasan da za a horar din, da su nuna sha’awarsu akan abubuwan da suka shafi kasa kuma su sanya kudurin shiga jam’iyyun siyasar da suke ra’ayi da zai ba su damar shiga harkokin siyasa gadan gadan.
Shugaban ya yabawa gwamna Abubakar Sani Bello kasancewar shi ne gwamnan farko da yayi hadin guiwa da kungiyar, ya nemi sauran jahohi da su yi koyi da irin wannan dubarun dan kawo karshen talauci da kirkiro cigaban karkaru.
A daga cikin mahalarta taron, sun hada da kwamishinan ma’aikatan matasa da wasanni, Hon. Emmanuel Umar, sai shugaban majalisar dokokin jiha, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Jibrin Ndagi Baba, da shugaban kungiyar matasan Neja, Malam Bello Sheriff.