Nijeriya Na Bukatar Sa Jarin Dala Biliyan Takwas Don Samar Da Ingantaccen Ruwa –UNICEF

Daga Idris Aliyu Daudawa

Zaid Jurgi ya bayyana cewa Nijeriya na bukatar akalla Dala Biliyan Takwas domin samar da ingantaccen ruwa.

Zaid Jurgi wanda shi ne shugaban Sashen WASH dake Hukumar UNICEF, a yayin da yake gabatar da kasidarsa a wurin taron tattaunawa dangane da samar da ingantaccen ruwa, wanda ya gudana a garin Jos na Jihar Filato.

Ana bukatar kamar dalar Amurka bilyan 8 ko wacce shekara saboda a samar da tsaftataccen ruwan sha a Nijeriya, idan har ana son ta cimma muradan cigaba na shida daga ciki, nan da shekara ta 2030.

Shi dai wannan muradin ci gaban na shida shi ne yadda za a samar da tsafatatacce kuma isasshen ruwan shag a dukkan al’umma, wani jami’i na majalisar dinkin duniya na sashen asusun gaggawa na kulawa da yara majalisar dinkin duniya, Zaid Jurgi shi ya ya bayyana haka ranar Talata a Jos, a wani taro na aka yi domin tattauna matsalar samar da ruwan sha da kulwa da tsaftace shi a Nijeriya.

Taron dai Hukumar kula da asusun yara na taimakon gaggawa na majalisar dinkin duniya, tare da hadin  cibiyar akan hakkin yara, ta ma’aikatar watsa labarai da al’adu.

Mr Jurgi ya ce su kudaden gwamnatocin tarayya, jihohi da kuma Kananan Hukumomi zasu samar dasu, tare da hadin kan Hukumar kula da asusun yara na taimakon gaggawa na majalisar dinkin duniya, da  kuma sauran wasu masu taimakawa, ta hakan ne Nijeiya zata samu taimako wajen samar da tsaftatacen ruwan shag a al’umma.

Mr. Jurgi, shi babban jami’i ne banagren tsafatace ruwan sha (WASH)a Hukumar kula da asusun  yara na taimakon gaggawa na majalisar dinkin duniya, ya kara jaddada cewar Nijeriya mai yawan jama’a fiy da milyan 60, har yanzu ba tada isasshen tsatataccen ruwan sha, don haka akwi bukata ta akara sa kudi domin a tabbatar da an samu isasshen ruwan.

Idan kuma Nijeriya ta ci gaba a yadda take na maganar ci gaban samar da ruwa, wannan ya nuna ke nan zata ci gaba da tafiya hka, haka kashi 72 ne, zai samu tsatataccen ruwa nan da shekara ta 2030.

Hanyar smun tsatataccen ruwa zai kare yara wadanda basu kai shekaru biyar ba, wadanda ke mutuwa duk shekara, a cututtukan da za aiya maganinsu, saboda yawancin cututtukan  adaliliin rashin tsaftataccen ruwa ne.

Mr Jurgi ya kara bayyana cewar kamar kashi 88 na cututtukan da suka shafi amai da gudawa a Nijeriya, suna fitowa daga jihohin da basu cika haruddan samar da isasshe kuma tsaftataccen ruwan sha.

Kashi 25 na al’ummar Nijeriya suna yi kashi ne a waje ba tare da ruwa mai kyau ba, y ace wannan kashin ya fi yawan jama’ar kasar Canada.

Amma kuma a nata kokarin wajen samar da yanayin da za a daina yin kashi a waje, Mr Jurgi ya ce Hukumar kula da susun  kula da yara na taimakon gaggawa, da hadin guiwa na ma’aikatar samar da ruwa, zasu fara rangadin wayar da kan jama’a akan akan muhimmancin samar da tsatataccen ruwan sha.

Rabin mutane milyan dari da saba’in  basu da wata dama da zasu samu tsaftataccen ruwan sha, yawanci kuma suke samarwa kansu ruwan sha , ta hanyar gigina rijiyoyin burtsatse, ko kuma su debo daga fadamu  da kuma koramu.

Tun farko a taron Bankin duniya yayi kira kira da gwamnatin Nijeriya data a kalla zuba kashi 1.7 na kudaden da ake samu kafin a cire masu haraji, zuwa bangaren samar da tsaftataccen ruwan shan. Sabboda kudaden da take sawa yanzu abin bai kai ko kashi daya ma bisa dari ba.

Exit mobile version