Connect with us

SIYASA

Nijeriya Na Bukatar Tsayayyen Shugaba

Published

on

Shugaban majalisar Dattijai kuma mai neman takatar shugabancin kasar nan a karkashin jamiyyar PDP Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa, Nijeriya na bukatar shugaba mai karfi da basirar gudanar da aiki a zaben shugaban kasa dake tafe a shekarar 2019.

Saraki ya yi wannan bayanin ne a garin Abakaliki, a jihar Ebonyi a ci gaba zagayen da yake yi don ganawa da wakilan jamiyyar PDP a jihar da zasu hudanar da zabe dan takara da zai daga tutar jamiyyar a zabe ma zuwa. Ya fara wannan zagayen ne daga jihar Ebonyi Dana Inugu.

Saraki ya samu kyakyawar tarba daga masoya da yan jamiyya a wani taron girmamawa da aka gudanar a babban dakin taro na jamiyyar dake garin, ya kuma bayyana wa masu saurararonsu wanda suka hada da Gwamnan jihar Mista Dabe Umahi da mataimakinsa Batista Eric Kelechi da shugaban majalisar dokokin jihar sai bkuma tsohon gwamnan jihar Sanata Sam Egwu shugaban jamiyyar PDP na jihar da sauran masu ruwa da tsaki, ya kuma sanar dasu cewa, in har zama shugaban kasa zai gudanar da mulki ne tare da kowa shugabanci dake cike da adalci kudurin bunkasa kasa baki daya.

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu kasar nan na a wani marhala ne mai sarkakiya a tarihinta na ci gaba, a saboda haka Nijeriya na bukatar shugaba tsayayye wanda zai jagoranci kasa zuwa tudun mun tsira.

Ya kuma taya gwamnan jihar, Mista Umahi a bisa ayyukan alhairi daya gudanar a fadin jihar, ya ce wannan namijin aikin ne ya sa masu ruwa da tsaki na jamiyyar PDP ta jihar suka amince masa tsayawa takara a karo na biyu, daga nan sai ya bukaci yan jamiyyar su bashi kuri’arsu a zaben fid da gwani da za a yi don fitar da dan takara a jamiyyar.

A nasa jawabin, Gwamna Umahi, ya yaba wa shugaban majalisar dattijai a bisa nasarorin daya samu a matsayinsa na gwamna na tsawon shekara 8 a jihar kwara, da kuma nasararsa a matsayin shugaban majalisar dattijai tun shekarar 2015.

Daga nan ya kara da cewa, daga yadda shugaban majalisar dattijan ya gabatar da jawabinsa ya nuna cewa, yana da basirar gudanar da mulkin Nijeriya, a kan haka ya bayar da tabbacin za su yi kyakyawan nazarin a kan bukatar zabensa a matsayin dan takarar shugabancin jamiyyar PDP a zabe mai zuwa.

Cikin tawagar shugaban majalisar dattijan a kwai shugaban kwamitin yakin neman zabensa Hon. Mohammed Wakil da sauran jama’a.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: