Yusuf Shuaibu" />

Nijeriya Na Iya Samun Dala Biliyan 10 A Bangaren Kimiyya Kafin 2030­

Kimiyya

Shugaban hukumar bunkasa bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi ya bayyana cewa, Nijeriya tana tsammanin samun dala biliyan 10 a bargaren kimiyya. Abdullahi ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki a kan tsare-tsaren kimiyya na kasa. Ya bayyana cewa, gwamnatin tatayya ta fuskanci kaluba ne a cikin kimiyya da fasana wanda a kawi mukatar ta dauki darasi ga abubuwan da suka faru a baya.

Ya ce, “idan muka duba yawan matasan da muke da su, za a ga akwai karancin sanin ilimin kimiyya, muna neman hanyoyin da za mu sami akalla dala biliyan 10 kafin shekarar 2023 ta kama, hakan ba zai iyuwa har sai an samar da kudade masu yawa wajwn gudanar da ayyuka a wannan bangare.

“Nijeriya tana daya daga cikin kasashen Afirka wajen bunkasa kimiyya da fasaha. Mun kawo wadansu tsare-tsare da zai taimaka wa Nijeriya wajen samun kudaden shiga masu yawan gaske ta yadda gwamnati za ta samu samar bunkasa ilimi da kiwon lafiya. Domin kimiyya na taka mahimmiyar rawa wajen saurin farfado da tattalin arziki ta kowata fuska musamman ma a bangaren samar da kayayyaki da ayyuka,” in ji shi.

Ya kara da cewa, akwanan nan ne aka fitar da wata kididdiga wanda ya nuna cewa, nan da shekaru 10 kimiyya za ta samar wa duniya zunzurutun kudade wanda ya kai na dala tiriliyan 1.7.

“Domin haka, muna bukatar hanyoyin da za a bunkasa kimiyya a Nijeriya ta yadda zai bayar da damar farfado da tattalin arziki a cikin ‘yan shekaru kadan. Tabbas Nijeriya ta yi matukar amfana da harkokin kimiyya.

“Yanzu abin da muke bukata kadai dai shi ne, samar da hanyoyin da za a magance matsalolin kimiyya. Inda daga karshe za a gabatar da wasu tsare-tsare da zai dakile rashin faruwar duk wata matsala a bangaren tattalin arziki,” in ji shi.

A wajen wannan taro, wakilin babban bankin Nijeriya (CBN), Fadele Adeolu, ya bayyana cewa, babban bankin tana kokarin shiga cikin wannan shirin.

“CBN a shirye yake a shiga cikin wannan tsari da zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan. Ina addu’a wannan shiri haifar da sakamakon da ake bukaya,” in ji shi.

Shi ma wani masanin kimiyya mai suna, Abdulsalam Umar, a nawa jawabin ya bayyana cewa, idan aka sami nasarar gudanar da wannan aiki, zai magance matsalolin tsaro a cikin kasar nan domin zai bayar da damar da za a samu muhilli mai kyau tare da samar da kayayyakin da zai dakile lamarin cikin sauki,” in ji shi.

Exit mobile version