Idris Aliyu Daudawa" />

Nijeriya Na Sa Ran Masu Zuba Jari Daga Kasashe 15

Wata cibiya dake kula da sa hannun jari, tare da hadin kan hukumar dake kula da alhakin samar da abubuwan more rayuwa, wadanda dama sune ke jan hankali masu sa hannun jari, da kuma ofishin dake kulawa yadda ake samun fasahar da kuma amfani da ita, da sauran wasu hukumomin gwamnati, suna sa ran samun masu sa hannun  jari daga kasashe goma sha biyar.

Kasashen da ake sa ran su ne United States United Kingdom,Thailand, Brazil, South Africa, France, Germany, Spain, Indonesia, da kuma China. Da yake yin bayanai a wani taro na kasa da kasa, a Abuja wanda ya mayar da hankali akan sa hannun jari zuwa Nijeriya, da akwai kuma shugabannin hukumomin gwamnati masu yawa, da suka halarci shi taron. Akwai shugaba NIG wanda wani kamfani ne da yake zaune a kasar waje amma mallakar dan Nijeriya ne, wanda shi ya na tallar Nijeriya ne, Chidi Umeano, ya bayyana cewar wasu daga cikin kasashen an ce masu ne su zo su sa hannun jari ko kuma gina masana’antu.

Ya kara bayyana cewar’’Muna sa ran kasashe goma sha biyar ne zasu zo, saboda yin harka da Nijeriya, wannan kuma ya danganta ne da ko shigo da kayayyakin cikin gida, ko kuma fitar dasu duwa waje. Kamar dai United States da UK da Thailand da Brazil da South Afirka da France da Germanay da Spain, Indonesia, da kuma China.

Muna amfani ne da wannan damar a gaiyace su zuwa Nijeriya, domin su kafa masana’antu, muna ce masu su zo, saboda su yi musayar ilmin su da ‘yan Nijeriya, muna son su zo saboda su koya mana abubuwan da suke yi, da kuma yadda suke yinsu. Saboda mu bunkasa tattalin arzikinmu, ta hakan ne za a samar da ayyukan yi masu yawa.’’

Umeano bugu da kari ya kara bayyana cewar shi taron an shirya shi ne, saboda a tallata kayayyakin Nijeriya na gida, domin su wadanda suke samar dasu, su samu hanyar, samun kudaden waje, ya kuma kara da cewar ‘’Saboda muna da kayayyaki wadanda zasu yi gogayya, kafada kafada dana kasashen waje.’’

Ya ce, Nijeriya ta shiga hada hulda kasuwanci da masu fada aji, akasashe daban daban na duniya, saboda a samar da ayyuka wadanda suka bambanta, ta hanyar yin wasu abubuwa, ko kuma gabatar dasu, domin a nuna cewar lalle Nijeriya ja gaba ce, ta bangaren tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Babban jasmi’i na NOTAP Dan’azumi Ibrahim ya bayyana cewar, abin yana da muhimmanci, a samu jawo hankalin masu sa hannun jari daga kasashen waje, zuwa Nijeriya. Ya ce, al’amarin yadda za a samar da kudaden da kuma dawo da wasu kudaden, da wasu kamfanoni, fiye da  kashi 90 ne,  na fasahar wadda ke bunkasa tattalin arzukin Nijeriya  shigowa ake yi da ita.

 

Exit mobile version