Ma’aikatar harkokin noma da raya yankunan karkara ta bayyana cewa, za ta bunkasa noman kashu wanda zai iya samar wa matasan Nijeriya sama da 500,000 ayyukan yi. Sakataren dun-dun-dun a ma’aikatar, Dakta Abdulkadir Mu’azu shi ya bayyana hakan wanda ya ce, hakan zai bunkasa tattalin arziki. Mu’azu ya bayyana hakan ne a taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki bangaren noman kashu wanda ya gudana a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Mataimakin daraktan ma’aikatar, Mista Bernand Chukwuemeka shi ya wakilci sakataren wanda ya bayyana cewa, kara martabar kashu yana daya daga cikin mahimman amfanin gona da ma’aikatan za ta inganta. Ya kara da cewa, inganta noman kashu da ma’aikatar da ke kokarin yi domin a samu nasarar samar da ayyukan yi ne da kuma samun kudaden shiga daga fitar da shi zuwa kasashen ketare. A cewarsa, a yanzu kana Nijeriya ta shuka tan 175,000 a gonaki wadanda suka kai hetta 150,00 wanda za a sami kilogiram guda 350 ga kowacce hetta.
Ya ce, “bunkasa noman kashu a Nijeriya zai samar da tan 175,000 wanda ya kai kashi 20, wanda zai iya samar da sabbin ayyukan yi guda 500,000 da kuma karin kudaden shiga wanda ya kai naira miliyan 10.
“Wannan yana nuna cewa, kamfanonin kashuu za su bunkasa a Nijeriya idan aka hada hannu da karfe, wannan shi ne makasudin haduwan mu a yau,” in ji shi.
Tun da farko dai, shugaban hukumar fannin binciken noman kashu da cibiyar binciken noman koko a Nijeriya, Dakta Ibiremo Samuel ya bayyana cewa, ya zama wajibi cibiyar da ta samar da hanyoyin inganta noman kashu a cikin kasar nan. Samuel ya kara da cewa, cibiyar ta samu nasarar bunkasa mabambamtan irin kashu da kuma hanyoyin da za a bi domin kaucewa kwarin gona domin a samu yabanya mai kyau. Samuel ya ce, cibiyan da samu nasarar bunkasa jus wanda ake sarrafa shi da kashu da kuma horar da mata da matasa hanyoyin da za su bi wajen sarrafa kashu domin ya koma jus.
Hakazalika, shugaban kungiyar manoman kashu ta Nijeriya, Mista Ojo Ajanaku ya bukaci mahalarta wannan taro da su yi amfani da wannan taro wajen aiwatar da bunkasa noman kashu a Nijeriya domin samun gagaruman kudaden shiga da kuma ayyukan yi ga dimbin matasa.