Ministan ma’aikatar gona da raya karkara Alhaji Sabo Nanono ya yi nuni da cewa a yanzu, Nijeriya na tabka asarar samun kudaden musaya na kasar waje wajen sayar da Kanya, saboda rashin habaka fannin.
An ruwaito cewa, Nijeriya ce ke a kan gaba wajen noman Kadanya a daukacin nahiyar Afrika da kuma duniya baki daya, inda kasashen Ibory Coast, Ghana da Togo suka biyo bayanta kuma kasar na da kimanin kadada miliyan 5 na Kadanya.
Alhaji Sabo Nanono ya sanar da hakan ne a wani taron bita kan Kadanya na kwana biyu da kuma yadda mahalarta taron za su za su kaucewa yin asara yayin da suka girbeta.
Ministan wanda mataimakin Darakta a ma’aikatar gona da raya karkara Mista Bernard Ukattah ya wakilce shi a gurin taron ya ci gaba da cewa, noman Kadanya na daya daga cikin amfanin gona da ma’aikatar ta ke son ta daga darajarta.
Alhaji Sabo Nanono ya sanar da cewa, yawan Kadanyar da ake noma wa nahiyar Afirka an kiyasta ya kai tan 600,000, inda ya yi nuni da cewa, saboda asarar da ake yi, hakan ya janyi Nijeriya na yin asarar kudaden musaya na kasar waje da dama.
Ministan ma’aikatar gona da raya karkara Alhaji Sabo Nanono ya yi nuni da cewa, idan aka yi la’akari da yadda masana’antun da ke sarrafa man shafawa su ke da matukatar bukatarta.
Sai dai kuma, an bayyana cewa, akasari masana’antun da ke sarrafa abinci sune suka fi bukatarta idan aka yi la’akri da kasha 90 a cikin dari na yawan da ake numa ta a kasar nan.
Akasarin Kadanyar da ake noma wa a kasar nan, ana fitar da ita zuwa waje ne, inda a cikin kasar nan ake yin amfani da kimanin kashi 20 a cikin dari.
Yawanta ya danganta ne kan yadda ake da bukatarta a kasuwanni, inda kuma ake sayen kimanin kashi 50 a cikin dari na yawan jimlarta.
Ministan ma’aikatar gona da raya karkara Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewa, taron bitar na daya daga cikin dabarun da aka dauka domin kara bunkasa fannin da kuma kara nomanta da ya wa a kasar nan.
Ministan ma’aikatar gona da raya karkara Alhaji Sabo Nanono ya kuma yi kira ga mahalarta taron su yi amfani da ilimin da suka samu a yayin bitar domin kara habaka noman Kadanya a kasar, inda ya yi nuni da fanni ne da zai taka muhummiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan da kuma samar wada kasar da kudaden shiga masu ya wa.
Ministan ya lura cewa shirin zai kkarfafa tallafin fasaha tare da sanya kyawawan aikin Noma na (GAP) don inganta bukatun abinci da kuma a tsakanin masana’antu.
Da yake magana yayin bikin nadin a Abuja, Nanono ya umarci kwamitin da ya tsara tsarin horar da ma’aikatan fadada ayyukan gona a cikin shekaru 2 masu zuwa da kuma ba da shawarar matakan inganta da kuma sake inganta cibiyoyin horar da ci gaba a fadin kasar.
Ministan ya kara da cewa, kwamitin zai taimaka wa ma’aikatar wajen samar da tsarin aiki mai kyau da kuma shirin aiwatar da aiki domin horar da ma’aikatan 75,000 tare da hadin gwiwar Ayyukan Ci gaban Aikin gona na jihohi (ADPs).
Nanono ya jaddada bukatar sake duba hanyoyin koyar da ayyukan fadada ayyuka da ayyukan da ake aiwatarwa a Nijeriya tare da kokarin samar da su sosai.
Da yake mayar da martani a madadin kwamitin, shugaban, wanda shi ne Darakta, Ayyukan Ci gaba a ma’aikatar, Frank Kudla, ya yi alkawarin cewa, kwamitin zai yi aiki kafada-da kafada don bayar da shi kan wa’adin aikinsa.