Nijeriya ta kashe kusan naira tiriliyan biyu wajen biyan bashi tun daga watan Junairu har zuwa watan Satumbar shekarar 2020, kamar yadda rahoton hukumar da ke kula da basuka ta kasa (DMO) ta bayyana. A ranar Alhamis ce da ta gabata hukumar DMO ta bayyana cewa, basukan da ake bin kasar nan ya karu da naira tiriliyan 1.21 a shekarar da ta gabatar, wanda ya sa basukan suka kai na naira tiriliyan 32.22. Hukumar DMO ta bayyana cewa, an dai hada basukan ne da na cikin gida da na waje wanda ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi 36 cikin har da Abuja.
“Gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi cikin har da Abuja sun kara yawan basukan da ake bin su, domin su sami damar farfadowa daga matsalolin da suka fuskanta lokacin cutar Korona,” in ji ofishin hukumar DMO.
Rahoton da hukumar DMO ta fitar wanda aka nuna wa manema labarain, ya nuna cewa kasar nan ta narkar da kudade na naira tiriliyan 1.99 wajen biyan bashi tun daga watan Junairu zuwa watan Satumbar shekarar 2020. Yawan kudaden da aka kashe a biyan bashin cikin gida ya kai na naira tiriliyan 1.53, yayain da yawan bashin na kasashen ketare ya kai na dala biliyan 1.27 wato na naira biliyan 467.44. A farkon shekarar 2020, an kashe naira biliyan 609.13 wajen biyan bashin a cikin gida Nijeriya. Haka kuma, an kashe dala miliyan 472.57 kwatankwacin naira biliyan 170.60 wajen biyan bashi a kasashen ketare a farkon wata ukun ta shekarar 2020, an kashi dala miliyan 287.04 wato naira biliyan 103.62 a wata shida, sannan an kashe dala miliyan 507.15 wata naira biliyan 193.22 a wata tara na shekarar 2020.
A cwar hukumar DMO, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar da canjin kowacce dala daya a matsayin naira 361 lokacin da za a biya bashi na wata uku, sannan ya bayar da canjin kan naira 381 ga kowacce dala a wata shida da kuma wata tara.
“Duk da irin matsalolin rashin samun kudaden haraji sakamakon cutar Korona, amma gwamnatin tarayya ta samu nasarar biyan wasu daga cikin basukan da ake bin ta da harajin da ta samu,” in ji rahoton.
Babban Bankin Nijeriya ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kasu nasarar biyan kashi 19.2 daga cikin basukan da ake bin ta.
A watan Disamba, hukumar bayar da lamuni ta duniya ta bayyana cewa, Nijeriya tana bukatar kara samun haraji mai yawa ta hanyar samar da sababbin manufofi da kuma harkokin gudanarwa, domin za ta samu dakatar da yawan basukan da ake bin ta. Ta kara da cewa, idan ta samu nasarar yin wannan, to za a sami damar rahe talauci da samun karin kudaden shiga wanda zai bunkasa tattalin arziki.