Babban Kwamishinan kasar Indiya a Nijeriya Abhay Thakur ya sanar da cewar, Najeriya zata iya karbar bashin dala biliyan biyar mai dauke da kudin ruwa can Kazan. Abhay Thakur ya samar da hakan ne a lokacin da ya kaiwa Ministanb Sadarwa Adebayo Shittu a ofishin fake garin Abuja a ranar Litinin data gabata. Babban kwamishinan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ci gaba da cewa, Firimiyan kasar ta India ya bada da irin wannnan bashin ga wasu kasashe fake a cikin nahiyar Afrika na dala biliyan10. Ya ce, Nijeriya ta na da dama wajen Neman rancen fake da kudin ruwa kashi 1.75 bisa dari. Thakur ya ce, indiya ta na kokari wajen inganta huddar ta da Nijeriya ta fannin samar da ci gaba da kuma fasaha. A basin jawabin Shittu ya ce, Indiya ita ce ta daya wajen huddar jadakadanci da Nijeriya. Acewar Shittu a bangaren yarjejeniyar, zamu iya kulla harkar samar da ci gaba. Ya ce kamfanonin kasar Indiya da damage suna son suzo Nijeriya don su zuba jarin su ta hanyar kakkafa masana’antu. Ministan ya yi kira ga Kwamishinan ya baiwa masu zuba Marin na kasar ta Indiya don suzo Nijeriya su zuba da kuma yin hadaka da masu ruwa da tsaki da kuma kafa sadarwa ta zamani a Abuja da ake da ran za ta samawar wa da Nijeriya kudin shiga.
Nijeriya Ta Ciwo Bashin Dala Biliyan Biyar Daga Kasar Indiya

- Categories: KASUWANCI
Related Content
Kimanin Masarar Naira Biliyan 30 Aka Yi Asara Sakamakon Matsalar Tsaro A 2020 - Manoma
By
Sulaiman Ibrahim
July 29, 2021
Gwamnati Ta Zargi 'Yan Nijeriya Mazauna Waje Da Taimaka Wa Nakasa Attalin Arziki
By
Sulaiman Ibrahim
July 29, 2021
Kasuwanci Na Raguwa Ne A Nijeriya Sakamakon Matsalar Tsaro - CBN
By
Sulaiman Ibrahim
July 29, 2021
Abubuwa 10 Da Babban Rahoton Bankin Duniya Ya Bayyana Game Da Nijeriya
By
Muhammad
July 27, 2021