Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Nijeriya daga wasannin kwallon kwando na tsawon shekara biyu.
Wata sanarwa daga ma’aikatar wasanni ta kasa ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan matsalolin da suka dabaibaye harkokin kwallon kwando a kasar nan.
Za’a nada kwamiti na riko domin yin garanbawul akan kwallon kwando na kasa Kamar yadda ministan wasanni Sunday Dare ya tabbatar.