Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ta Kora ’Yan Kasar Indiya 36 Da ’Yan Kasar Koriya Biyu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta amince ga gaggauta fitar da wasu ‘yan kasar indiya 36 da kuma wasu ‘yan kaar koroiya 2 daga kasar nan.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ya bayana haka a wata sanarwa da babbar sakataren ma’aikatar, Mohammed Umar, ya sanya wa hannu a Abuja ranar Talata.

Mista Umar ya ce, Ministan ya sanya hannu a kan fitar da mutanen  daga cikin kasar nan a ranar Talata, kamar yadda dokar kasa ta ba shi hurumin yin haka, doka shige da fice ta kasa mai lamba 45 (2, 3 and 4) ta shekarar 2015.

Mista Dambazau ya yi bayanin cewa, ‘yan kasar Indiyan sun shigo kasar nan ta takardun jabu da kuma sa hanun jam’ian shige da fice na jabu, yayin da ‘yan kasar Koriyan suka kasa sabunta takardun zaman su a kasar nan a lokacin da aikisu ya kare tare da gwamnatin jihar Zamfara.

Mista Dambazau ya bayar da sunayen mutanen kamar haka; Mista AN CHUN SIK da Mista JON SU GYONG dukkansu ‘yan kasar Koriya.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen ‘yan kasar Indiyan su 36 kamar haka: -Mista Sajji da Misis Sajji Arbini da Misis Sunil Babujumma da Misis Meemi da Mista Papachi da Mista Deba  Mista Rajani da Misis Kiran Shibachadra da Mista Shibachadra da kuma Mista Shakthi.

Sauran kuma sun hada da: Mista Prabhukumar da Mista Rajan Mista Shree Kumar da Mista Jagandeesh da Misis Mamathaja da Misis Sheela da Mista Prasad da Mista Pappa da kuma Misis Nirbeni

Sauran sunayen sun hada da: Mista Shambhu Kumar Misis Reshma da Mista Rabi Kumar da Mista Iraji da Misis Jinotha da Mista Kishore da Mista Nageena da Misis Sheelabathi da kuma Mista Nentaraju/Santhosh Kumar.

Ministan ya kuma bayyana saura ‘yankaar indiya da aka kora kamar haka, Misis Sumati da Mista Krishna Lokesh da Mista Santhil da Mista Basantha da Mista Seebu da Mista Bishwanath da Mista Bishwanth Ramya da kuma Mista Rajeshwari.

Ya kuma tabatar da kudurin shugaan kasa Muhammadu Buhari na kara tallafawa hukumar ‘Nigeria Immigration Service’ don karfafa dokokin shigeb da fice na kasar nan.

Ya kuma bukaci dukkan ‘yanNijeriya dake zaune a fadin kasar nan su tabatar da suna bin dukan dokokin kasa, don kuwa hukmomin tsaron kasa ba za su yarda da rashin mutunta dokokin kasa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: