Yusuf Shuaibu" />

Nijeriya Ta Narkar Da Naira Tiriliyan 1.62 Wajen Shigo Da Mai A Wata Tara

Shigo Da Mai

Nijeriya ta kashe yawan kudade da suka kai na naira tiriliyan 1.62 wajen shigowa da mai tun daga watan Junairu har zuwa watan Satumba, kamar yadda rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta nuna. A cewar NBS, Nijeriya ta kashe naira tiriliyan 1.72 wajen shigo da mai a gaba daya shekarar 2019.

Bincike ya nuna cewa, man fetur ne aka fi shigowa da shi a cikin kasar nan, wanda ya karu da kashi 11.7 tun daga watan Junairi har zuwa watan Satumba. An shigo da man wanda ya kai na kashi 511.64 na naira biliyan 532.62 a farkon wata ukun shekarar 2020, wanda ya zarce na naira biliyan 87.08 na wata biyu da na naira biliyan 371.75 na wata ukun shekarar 2019. A farkon wata ukun wannan shekarar, Nijeriya ta kashe naira tiriliyan daya wajen shigo da man fetur. An lissafa cewa, an kashe kashi 73.04 wanda ya kai na naira biliyan 700.46 a wajen shigo da mai cikin kasar nan a wata ukun wannan shekarar, kamar yadda hukumar NBS ta bayyana. Sai dai an samu raguwar masu amfani da mai a wata biyun shekarar 2020, sakamakon dokar hana zirga- zirga da gwamnatin tarayya ta kakaba domin dakile yaduwar cutar Korona.

Bincike daga kamfanin mai na kasa (NNPC) ya nuna cewa, yawan mai aka shigo da shi domin  a sayar da ragu da lita biliyan 2.25 a watan Maris, an sami lita biliyan 1.81 a watan Afrilu, sannan kuma an sami lita miliyan 495.10 a watan Mayu. A karkashin shirin sayar da man, an zabi matatun mai na kasar waje da kamfanoni kasashen ketare da kamfanonin gida wadanda za su dunga gudanar da harkokin kasuwancin mai a karkashin shugabancin kamfanin NNPC. Nijeriya ta dogare ne da tace danyan mai daga kasahen ketare wadanda ake dawowa da man sai a siyar da shi a cikin kasar nan. Kamfanin NNPC shi ke shigo da man a cikin kasar nan. Duk da gyara bangaren mai, amma har yanzu ba a bari ‘yan kasuwa suna shigo da man ba sakamakon yadda kasuwancin canji kudade ke gudana.

Exit mobile version