Daga Sabo Ahmad
Nijeriya har yanzu ta kasa cin moriyar wasu makudan kudi da suka kai dala bilyan 100 don bayarwa ga kasashen da ke kokarin bunkasa kasuwancin ingantattun magungunan gargajiya.
Shugaban Hukumar kula da ingancin magungunan gargajiya, Sam Etatubie, ne ya bayyana haka lokacin da kwamitin kimiyya da fasaha na majalisar dokokin jihar Legas ya kai ziyar aiki ga Hukumar, inda ya bayyana cewa, Nijeriya ta yi asarar wadannan makudan daloli ne da rasa guraben ayyuka masu dimbin yawa sakamakon rashin samar da kasuwar ingantattun magungunan gargajiya a kasar
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin kimiyya da fasahar na majalisar Honarabul Beni Lar, ya bayyana cewa, rashin samar da kudi ba shi ne babbar matsala ba, ya kamata Hukumar ta nemi hadin gwiwa da sauran takwarorinta na kasashen duniya yadda za su amfana da juna. A kan jikirin da ake samu kuwa, na mallakar lasisi daga Hukumar kula da ingancin abinci ta kasa, Lar sai ya ce, majalisar dokokin na shirin samar da wata doka da za ta saukaka wa masu neman lasisi daga Hukumar, sannan sai ya roki gwamnatin jihar da samarwa da Hukumar filin da za ta gina matsuguninta don ciga da gudanar da aikace-aikacenta cikin walwala.
Haka kuma ya tabbatar wa da Hukumar cikken goyon bayan majalisar wajen tabbatar da samun nasararsu.