Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ta Sa Jarin Dala Biliyan 45.7 Cikin Wata Shida

Published

on

An bunkasa tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar zuba jarin zunzurutun kudi Dala biliyan 45.7 a bangaren hada-hadar kasuwanci daban-daban a farkon watannin shidan wannan shekarar da muke ciki.

An samu kididdigar hakan ne daga Hukumar kula da zuba jari ta Nijeriya, wadda t ace an zuba jarin na Dala biliyan 45.74 a cikin wasu aikace-aikace guda arba’in da biyu a jihohi tara da ke fadin kasar nan tare da Birnin tarayya Abuja.

Bincike ya tabbatar da cewa, kokarin da Hukumar ke yi ya bayar da dama ga masu sha’awar zuba jari da su zuba jarin Dala Biliyan45.7 a bangarori goma sha biyu da za su habaka tattalin arzikin kasar nan.

Haka kuma binciken ya tabbatar da cewa, bangaren hakar ma’adanai da fasa dutse ya aka zuba wa kaso ma fi tsoka na kasha 61 daga cikin kashi 100; sai masana’antu kashi, 28  daga cikin kashi 100; sai sufuri da rumbunan adana kayayyaki da ked a kashi 5 daga cikin kashi 100;  Gidaje kashi 3 daga cikin 100, sannan sauran bangarori kuma suka tafi daga cikin kashi 3 daga cikin kashi 100.

Bayanin ya ci gaba da cewa, masu zuba jarin sun fito ne daga kasashe goma sha daya.

Wasu kamfanoni daga kasar Faransa sun saka kashi 35 daga cikin 100, sai mai bi musu daga Nijeriya da suka sa kashi 31 dag cikin 100.

Rahoton ya ci gaba da cewa wasu kamfanoni daga Tarayyara Turai sun sa kashi 20 daga cikin 100; sai Ludembourg, mai kashi 7, sauran kashi 8 kuma sun zo ne daga sauran kasashen.

Rahoton ya ci gaba da cewa, jihar Ribas ita za ta fi kowace jiha amfana da kashi 35 daga cikin 100. Sai Bayelsa da Legas  da ke da kashi 26 kowannensu, sannan sai jihar Delta mai kashi 7 daga cikin 100.

Babban sakataren Hukumar Yewande Sadiku, ya bayyana cewa, yanzu haka suna aiki kafada da kafada da jihohi yadda za su cusa musu tunanin gayyato masu zuba jari daga kasashe. Sannan kuma ya ce, Hukumar ta su na da kyakkyawan hadin kai da jihohi yadda za su dinga lura da dukkan masana’anta ko aikace-aikacen da masu zuba jari ke gudanarwa.

 

Advertisement

labarai