Abubakar Abba" />

Nijeriya Ta Samu Naira Tiriliyan 5.54 Daga Mai A Shekarar 2018 —CBN

Tattalin Arziki

A bisa adadin da aka samo daga gun Babban Bankin Nijeriya CBN ya nuna cewar, Nijeriya ta samu jimlar Naira tiriliyan 5.54 a matsayin kudin shiga na man fetur a shekarar 2018.
Adadin na naira tiriliyan 5.54 na kudin shigar, an same sune ta manyan hanyoyi uku na kudin shiga na man na fetur.
Hanyoyin uku sune, danyen mai da iskar gas da aka sayar, ribar haraji ta mai da kuma ssuran su.
Fashin bakin da aka yi na jimlar naira tiriliyan 5.54t ribar da aka samu daga fannin danyen mai ya nuna cewar an samu naira tiriliyan N1.28 a farkon zangon shekarar ta 2018.
Bugu da kari, adadin ya kuma haura zuwa naira tiriliyan 110 a zango na biyu na shekarar ta 2018 zuwa naira tiriliyan 1.38, inda kuma a zangon na hudu na shekarar ta 2018, Nijeriya ta samu ribar naira tiriliyan 1.39.
A dogon fashin bakin da akayi akan adadin ya nuna cewar, a zango na farko an samu naira tiriliyan
1.28 daga fannin sayar da danyen mai da kudin ya kai naira biliyan N98.21, har ila yau, an samu naira biliyan 926.33 da sauran naira biliyan 263.51.
Bugu da kari, a zango na biyu kuna, an samu kudin shiga naira tiriliyan 1.38 daga dsnyen mai da aka sayar har na naira biliyan 109.32 da kuma kayan PPT nanaira biliyan 841.03 da kuma sauran naira biliyan N447.7.
A zango na uku kuma, Nijeriya ta samu naira biliyan 104.49 daga danyen mai da aka sayar da samun naira biliyan 914.56 daga kayan PPT da kuma naira biliyan 375.14 daga sauran.
Bugu da kari, a zango na hudu kuma, an samu kudin shiga naira biliyan 103.6 daga danyen mai da aka sayar, sai kuma naira tiriliyan 1.04 daga kayan PPT, inda kuma aka samu kudin shiga naira biliyan 317.5 daga sauran hanyoyi.
Ministar kudi Uwargida Zainab Ahmed, ta sanar da cewar akwai bukatar a kara samar dakuaden shiga ga Nijeriya bata fannin mai ba don a kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan.
Zainab Ahmed ta sabar da hakan ne a lokacin da take yin jawabin ta taron cibiyoyin kudi da ciyar da tattalin arziki na shekarar 2018, inda ta kuma shwarci jihohin dake kasar nan su kara samar da hanyoyin ssmun kudaden shigar su.
Ta yi nuni da cewar, a saboda ci gaba da samun faduwar da akeyi ta farashin mai na cikin gida a shekaru da dama da suma shige zai yi wuya gwamnati tarayya ta iya cimma burin ka’idar kasafin kudin ta, inda ta yi nuni da cewar, hakan ya faru ne saboda shekarun da kasar Man ta shafe tana dogaro akan mai duk da cewar kasar tanada dimbin albarkantu na arzikin kasa da zasu iya samar mata da dimbin kudaden shiga.
A karshe ta yi nuni da cewar akwai bukatar samar da dabarun samar da kudaden shiga don ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba.

Exit mobile version