Sulaiman Ibrahim">

Nijeriya Ta Samu Zaman Lafiya Fiye Da Shekaru Biyar Din Baya – Burutai

Nijeriya tana cikin aminci yanzun fiye da shekarar 2014, in ji shugaban rundunar soji (COAS), Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.
Ya bayyana hakan ne a asibitin 44 inda sojin suke jinya a jihar Kaduna, yayin ganawarsa da Sojin da suka ji rauni yayin gabzawarsu da ‘yan ta’adda.
Shugaban Sojin kasa (COAS), wanda ya bayyana farin cikin kasancewarsa tare da majin yatan, ya yaba da kokarin da suke yi na ganin sun kubutar da kasa daga hannun ‘yan ta’adda, ya ce, kokarinsu ba zai tafi a banza ba, ba tare da yabawa ba, yana mai yaba musu kwarai da kishin kasa da kwarewa.
A cewar sa: “Na yi matukar farin cikin ganinku saboda haduwa da wasu daga cikinku a fagen fama, kun yi niyyar biyan kyauta mafi kyawu. Wannan shi ne ruhin gaskiya na soja mai kauna da kishin kasa.
“Ina alfahari da ku, sanadiyyar kishin kasar ku yau abokan aikinku da ‘yan Nijeriya suke zaune lafiya, kuma ina mai farin cikin cewa muna zaune cikin kwanciyar hankali kuma Nijeriya ta aminta yanzu fiye da yadda muka samu kanmu shekaru biyar da suka gabata”.
Ya tabbatar wa sojojin da aka raunata samun ingantacciyar kulawa ta asibiti, gami da bin diddigin karin samun lafiyarsu zuwa kasashen waje in akwai bukatar hakan.
“Na fahimta kuna bukatar wuraren nishadi anan. Wasu kuma suna bukatar samun karin girma, mun lura da hakan kuma za’a magance matsalar gwargwadon yadda ya kamata.
“Za mu ci gaba da turo jami’an mu don ganin yadda kiwon lafiyarku zata inganta ta hanyar tsarin karbar dabaru domin ta haka idan kuka murmure, za ku iya komawa bakin aiki.
“Bari na tabbatar muku da cewa yaki da ta’addanci aiki ne na hadin gwiwa kuma ana iya cimma wannan ne ta hanyar himma da koyarwar da aka koya mana da kuma amfani da su a fagen yaki.
Babban daraktan asibitin (CMD) na asibitin ya bayyana mani matsalar alawus dinku, bada jimawa zamu ga yadda za mu sallami kowa.
“Dole ne mu bunkasa wadannan asibitocin, kayan aikin da ba mu da su za mu samo, saboda haka ba sai mun bukaci zuwa yin tiyata a wani wuri ba.
“Wannan shi ne daya daga cikin asibitocin da muka inganta. Mun yi irin wannan a Yaba da sauran wurare. Muna kuma gina Asibitin Sojan Nijeriya a Maiduguri, kuma muna da guda daya a Abakiliki. ”

Exit mobile version