Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Nijeriya Ta Tafka Asarar Naira Biliyan 138.98 A Kasuwancin Ketare Farkon Shekara

Published

on

Hukumar Kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa, Nijeriya ta tafka asara a kasuwanci na naira biliyan 138.98, a farkon wannan shekarra. Hukumar NBS ta bayyana wannan rahoton na kasuwancin kayayyaki da ke fitarwa zuwa kasashen na farkon wannan shekarar 2020, a ranar Talata. Rahoton ya nuna cewa, yawan kadaden kasuwanci Nijeriya ya kai naira tiliyon 8.3 a farkon wannan shekara ta 2020. Wannan kashi 17.94 ya yi karanci idan aka kwatanta da na farkon wata hudun shekarar 2019, wanda shi kashi 0.80 na yawan kudaden a farkon shekarar 2019.

“Yawan kayayyaki da ake shigowa dai ya kai na naira tiriliyon 4.22 wato kashi 50.8, yayin da kayayyakin da ake fitarwa ya kai na naira 4.08 wato kashi 49.2 na harkokin kasuwanci.

“A farkon wannan shekarar dai an tafka asara wadda ta kai na naira 138.98, wannan ya nuna irin asarar da aka tafka a harkokin kasuwanci a tsakani  kayayyakin da ake fitarwa da kuma wanda ake shigowa da su.”

Rahoton dai ya nuna irin yawan asarar da aka tafka a tsakanin kayayyakin da aka shigowa da su da kuma wanda ake fita da su, wannan ya faru ne sakamakon durkushiwar tattalin arzikin da aka samu a Duniya, saboda barkewar cutar Korona. rahoton ya ci gaba da nuna cewa, matsalolin lafiya da aka samu a Duniya sakamakon wannan annoba ya shafi harkokin kasuwanci da tafiye-tafiya da yawon shakatawa. Idan aka kwatanta da farkon shekarun baya, an samu asarar a wannan farkon shekarar na 2020 wanda ya kai na kashi 76. A shaka bayan shekara ana samun asarar wanda ta kai kashi 116.71.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: