Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Ta Tara Naira Biliyan 550 Ta Hanyar Sayar Da Kadarorin Gwamnati, Inji BPE

Published

on

Darakta Janar na hukumar sayar da hannun jari na kasa BPE Aled Okoh, ya sanar da cewar, kimanin naira biliyan 550 aka tara daga sayar da hannun jarin wasu kadarorin gwamnatin tarayya guda 142.

Okon ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a taron manema labarai da hukumar ta kirawo akan ayyukan hukumar da sauran wasu shirye-shiryen ta na shekarar2018.

A cewar Okoh Nijeriya ta tara dala biliyan 7.8 a matsayin jarin da aka zauna kai tsaye a da sayar da hannun jarin kamfanni 53 a cikin shekaru 18 da suka wuce.

Ya sanar da cewar ba dukkan tsarin na sayarwa ko kuma na kudi akan kaddarori ne aka sayar dasu ba kuma baza a dauke su a zaman kididdigar da aka jinginar ba.

A cewar sa, kimanin kashi 37 na kasuwanci an sayar da hannun jarin su kuma basa tabuka wata rawar a zo a gani.

Ya danganta hakan akan masu matsaloli da suka shafi tattalin arziki ya kara da cewar, baza mu yi watsi da wannan kasuwancin na amma zamu yi dubi akan yadda zamu magance matsalolin.

A cewar sa muna son mu taimaka wajen kawo karshen kalubalen da ake fuskanta a fanin wutar lantarki.

A cewar Okoh kimanin naira biliyan 330 aka biya a zaman kudin fansa na kimanin ma’aikata su 49,000 a lokacin da aka sayar da hannun jarin fannin.

Akan sayar da hannun jarin matatun mai Okoh ya ce, hukumar ta yi imanin cewar gyaran su yafi sayar dasu a yanzu.

Ya yi nuni da cewar, yarjejeniya ce mai kyau ga gwamnati saboda nan gaba. Ya sanar da cewar, banu wani shiri na sayar da kashi 49 bisa dari na shiyar gwamnati na sarrafa iskar gas.

A cewar sa, muna amfana da tagomashin yadda gwamnati zata ganshi a matsayin zuba jari musamman daga zuba jarin na daloli da kuma zuba kudin shiga ga gwamnati.

Bututan man da ma’adanar man duk suna cikin kadarorin da a yanzu ake shirin sayar da hannun jarin su.

Ya lisasafa wasu cinikayya da tsare-tsare da a yanzu hukumar ke kan yi wadanda suka hada da sayar da hannun jarin cibiyar wuta ta Afam wadda ya kamata a kammala a tsakanin watan Disambar 2018 da kuma farkon shekarar 2019.

Sauran sun hada da, sake fasalin bankin aikin noma da sanya wajajen shakatawa guda uku da aka zaba da kuma bayar da jnginar filin baje koli na kasa da kasa dake jihar Legas.

Hukumar an kirkiro ta ne a karkashin dokar 1999 don haba tattalin arzikin kasa da kuma karfafa masana’antu masu zaman kansu.

Darakta Janar ya sanar da cewar, a karkashin wannan tsarin ma’aikatar mai da albarkantu, mun samu nasarar gyra matatun mai bada kudin gwamnati ba.

Ya sanar da cewar a shekaru da dama da suka wuce, munyi kasafin kudi don gyara matatun man.

Ya sanar da cewar, gana dayan shirin ya kasance ne a tsakanin kamfani mai zaman kansa da da masu zuba jari don farfado da matatun man da sake gyaran su.

Ya yi nuni da cewar sama da lokuta da dama da suka wuce, mai zuba jari ta hanyar inganta kayan da aka sarrafa zai iya biyan kansa

 
Advertisement

labarai