A jiya Lahadi Gwamnatin Tarayya ta shaida cewar, ya zama dole kuma wajibi ne daga yanzu jami’an difolamasiyya na kasa da kasa sai sun mallaki lambar shaidar kasancewa dan kasa, wato NIN.
Sannan, mazauna Nijeriya ’yan kasa waje za su rika mallakar lambar muddin za su zauna a cikin kasar na tsawon shekaru biyu ko fiye. Sannan, an kuma ce, za a samar da cibiyar yin rijista ga jami’an diflomasiyyar a ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje da ke Abuja.
Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, shi ne ya shaida hakan, yana mai cewa, cibiyar musamman din da za a samar, ma’aikatarsa ce kai tsaye za ta kula da yin aikin rijistan kai tsaye.
Pantami ta cikin sanarwar da mai taimaka masa, Dakta Femi Adeluyi ya fitar, ya kara da cewa, an samar da cibiyar ne bisa roko da bukatar hakan da ministan kula da harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama ya yi lura da bukatar hakan da kasa ke da shi.
“Za a fara aiki a cibiyar ne a ranar Talata 19 ga watan Janairun 2021.
“Wannan cibiyar rijista ta musamman din, za ta taimaka matuka wa jami’an diflomasiyya wacce kai tsaye ma’aikatar sadarwa za ta lura da aikin rijistan ta hannun hukumar samar da shaidar tantancewa ta kasa ko a ce shaidar dan kasa.
“An samar da cibiyar ne bisa bukatar hakan da Ministan kula da harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya yi wanda kai tsaye zai taimaka wajen saukaka ayyuka da harkokin diflomasiyya.
“Mallakar shaidar dan kasa NIN wajibi ne ga dukkanin jami’in diflomasiyyar da zai zauna a Nijeriya sama da shekara biyu ko fiye.
“Har-ila-yau, ya zama dole ne ga dukkanin mazauna kasar nan ta halastaccen hanya kamar yadda doka sashi na 16 na hukumar samar da shaidar dan kasa NIMC ta 2007 ta samar.
“Dokar na cewa ne dole ne ‘yan Nijeriya da kuma mazauna kasar su mallaki shaidar NIN tun 2007. Koda yake bin matakin ya dan yi sako-sako, amma yanzu an dawo da shi,” in ji sanarwar.