Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Nijeriya Ta Yi Asarar Tiriliyan N61.1 Ta Haramtattun Hanyoyin Kudade

Published

on

Nijeriya ta bayyana cewa, ta yi asarar naira tiriliyan 61.1 ta haramtacciyar hanyoyin harkokin kudade a cikin shekara 10 da suka gabata. Masana sun shawarci kasar da sauran kasashen Afirka da su kafa dokar hana kudaden sulalewa.

Shugaban cibiyar tattara haraji na Afirka, Albin Mosioma, shi ya bayar da wannan shawara, inda ya bayyana cewa, wajibi ne kasashen Afirka su kafa dokar hana kudade sulalewa domin inganta tattalin arzikinsu da kuma samun kudade masu yawa wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.

A wajen taron majalisar dinkin Duniya a watan Satumba karo na 74, wanda kungiyar bunkasa nahirar Afirka ta shiryan, shugaban kasa Muhammed Buhari ya bayyana cewa, Nijeriya ta yi asanar dala biliyan 157.5 a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2012 daga wannan mummunan lamari. Bugu da kari, ayyukan mutane na bukatar kirkira domin kara samun kudaden shiga.

Mosioma ya bayyana hakan ne a wajen taron tattara haraji karo na bakwai. Akwai bukatar bin wasu hanyoyi domin inganta kudaden shiga.

A cikin jawabinta na hanyoyin tattali kudaden haraji, sakataren kudi ta cibiyar tattara haraji na Afrika, Rachel Etter-Phoya, ta ce, “mafi yawancin kasashen Afirka sun samu ‘yancin kai ne sama da shekaru 50 da suka gabatar, amma har zuwa yanzu sun kasa bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga.

A cikin bayaninta, babbar lauya kuma malama a jami’ar Nairobi, Layla Lateef ta bayyana cewa, hanyoyin samun haraji na tattalin arziki a kasashen Afirka ya yi karanci musammam ma lokacin cutar Korona wacce ta raunata tattalin arzikin kasashen Duniya.

“Bai kamata mu ci gaba da dogaro da amso bashi ba. Ya kamata mu samo hanyoyin samun kudaden haraji a cikin gida domin mu yi amfani da su wajen cimma muradunmu,” in ji ta.

Ta cigaba da cewa, samun hayoyin haraji a cikin kasa yana da matukar mahimmanci, domin zai sa kasa ta kasance mai kirkira. Lateef ta bayyana irin matsaloli tattara haraji a ake fama da su a nahiyar Afirka kamar haka, tsarin shugabancin kasa da matsalolin harkokin noma a matsayin hanyar samun tattalin arziki da kuma matsalolin mutanen karkara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: