‘Yan Nijeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu akan rashin nasarar da tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles ta yi, a wasan farko da ta buga na gasar cin kofin duniya tsakaninta da Croatia.
Mafi akasarin magoya bayan ‘yan wasan na Super Eagles sun nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin Nijeriya a wasan da ta yi rashin nasarar da 0-2.
Tsohon gwarzon dan wasan Super Eagles Jay Jay Okocha, na daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan wasan na ranar Asabar,inda ya dora alhakin kayen da Nijeriya ta sha akan rashin dabara a bangaren mai horarwa da kuma ‘yan wasan.
Okocha, wanda ya bayyana haka yayin zantawarsa da gidan talabijin na Super Sports, ya ce ‘yan wasan Nijeriya sun buga wasan ne a guraben da basu saba buga wasa ba, lamarin da ya sa suka gaza nuna bajintarsu.
Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayar da misalin cewa kama ta yayi, kaftin din tawagar Super Eagles Mikel Obi, ya buga bangaren dan tsakiya mai tsaron gida, kamar yadda ya ke yi a lokacin da yake kungiyar Chelsea, amma ba sashin dan tsakiya mai jefa kwallo ba.
Okocha ya kara da cewa Aled Iwobi, wanda a halin yanzu shi ne mafi kwarewar dan wasan tsakiya a tsakanin ‘yan wasan na Super Eagles, kamata ya yi a wasan na ranar Asabar, ya buga bangaren tsakiyar, amma ba gefe ba.
A ranar 22 ga watan Yuni da muke ciki Nijeriya za ta fafata da Iceland, yayinda kuma a ranar 26 ga watan za ta buga da Argentina.
Laifin Mai Koyarwa Ne Ya Sa Mu Ka Yi Rashin Nasara, Cewar Ighalo
Dan wasan gaba na Nijeriya, Odion Ighalo, ya ce bai ji dadin yadda ya buga wasan da suka fafata da kasar Croatia ba, inda ya zama shi kadai ne tilo mai jefa kwallo na tawagar Super Eagles din.
Ighalo ya bayyana haka ne, yayin da yake sukar tsarin rarraba ‘yan wasa da mai horar dasu Gernot Rohr ya zaba, na sanya ‘yan wasa uku a baya, biyu a gabansu, uku a tsakiya sai kuma jefa kwallo daya a gaba, wato 3-2-3-1, sabanin tsarin da aka saba gani na hudu a baya, hudu a tsakiya, da kuma masu jefa kwallo biyu a gaba; 4-4-2.
Korafin na Ighalo na zuwa ne bayanda tsohon gwarzon dan wasan Nijeriya Jay Jay Okocha ya dora alhakin kayen da Nijeriya ta sha akan rashin dabara.
Okocha, ya ce mai horar da ‘yan wasan Nijeriyar ya sauya musu guraben da suka saba buga wasanni a kai, dalilin da ya hanasu tabuka wani abin azo a gani.
Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayar da misalin cewa kama ta yayi, kaftin din tawagar Super Eagles Mikel Obi, ya buga bangaren dan tsakiya mai tsaron gida, kamar yadda ya ke yi a lokacin da yake kungiyar Chelsea, amma ba sashin dan tsakiya mai jefa kwallo ba.
A ranar 22 ga watan Yuni da muke ciki Nijeriya za ta fafata da Iceland, yayinda kuma a ranar 26 ga watan za ta buga da Argentina.